Chapter 76
Chapter 76
shi,Bayan na Shiga motar sa sai ya kaini gidan gonan sa tun daga wannan ranar take bani duk wata kulawa sai nake mamakin meyasa ya d'auko ni in dai bai cutar dani yake Shirin yi ba? Dana tambaye shi dalili yace Yana so ya hora nine Amma Kuma bai tab'a cutar dani ko na second d'aya bane....." Ajiyar zuciya na ta sauke ta cigaba da fad'in "Tun a wannan lokacin yace zai dawo dani gida Amma da sharad'in zan aure sa,Ni Kuma a wannan lokacin wutar tsanar sace a zuciya ta naki amincewa da bukatar sa,aiki kawai yake fita idan ya dawo yana Nan a cikin gidan sai abinda nake so yake yi ,Mami kin San zuciya Kuma ya Hadu da dama Nima inason shi tunda akan sa ne na San mene ne soyayya, soyyaya ce Mai karfi ta Shiga tsakanina dashi daga bisani muka yanke shawarar a d'aura Mana aure,Bayan Yan watanni ya nemi mu dawo gida sai naki sabida ina tsoron zaku rabani dashi" ta fashe da wani irin kuka Mai cin raai. Kallon ta Mami tayi ji take kamar karya take mata,Amma duba da yanayin jikinta da bata rame ba ,jikinta yayi kyau tayi fresh hakan ne ya tabbatar mata da cewar gaskiya take fad'a mata. Rungumar ta Mami tayi tana patting Bayan ta kamar wata Yar baby,babu Wanda ya Kuma cewa komai sai sautin kukan Ayrah da AC dake aiki a d'akin,Mami Tace "Ayrah lamarin kin Nan ya d'aure min Kai,wannan wani irin rashin hankali ne Ayrah kin sani cikin damuwa,bana iya bacci bana Kuma iya cin abinci duk a kanki Ayrah, ga Jikin baban Kuma abin Sai Kara gaba gaba yake yi" ta fashe da kuka, cikin tashin hankali Ayrah Tace "Mami Dan Allah ki daina kuka,kinsan kukan uwa Akan 'ya'yan ta ba abu bane Mai kyau" Murmushi mami tayi Wanda yafi kuka ciwo Tace "Kin San da hakan Kika yanke wannan d'anyen hukuncin? Kin tab'a tunanin a wani Hali nake ciki ko da na second d'ayane?" Ayrah kasa magana tayi idan mami tasan wahalar da tasha baza Tace haka ba idan Kuma ta kuskura ta fad'a mata tasan cewar ita da Adnan har abada. *Bayan kwana biyu* Adnan da Abdallah horo ake musu mai tsanani, duk sun lalace sunyi baki, musamman ma Adnan da shine babban Mai laifi, dakyar Ayrah ta shawo Kan Mami suka dunguma zuwa asibiti, tu daga waje take jiyo ihun say da gudu ta Shiga cikin Suma Mami suka rufa mata baya, Ayrah na kokarin shigewa inda take Jin kukan sa, wani police dake tsaye yaga shigowar ta ya daka mata tsawa ba ita kadai ba hatta su Mami Saida suka tsorata. "Ina Zaki?" Cikin kuka Tace "Dan Allah kace su daina dukan shi ni ba sace ni yayi ba" Isha da jaririn ta na samu kulawa sosai a gun Umma da Mummy , harda Haisam da yake ji kamar d'ansane, ranar suna yaro yaci sunan mahaifin sa wato Mansur (Mansur Mansur) su Mardiya sai rawar kai ake, su Meerah uwaye ita ma da d'an katon cikin ta anci ansha daga bisani kowa ya watse anan Mummy ta bukaci Isha ta koma gida Sam Umma bata ji dadi ba dakyar ta amince ta koma gida. Rikici akayi sosai tsakanin family d'insu Adnan dana Ayrah sabida Mahaifiyar shi sama taki amincewa da wannan auren, Adnan kuwa ya kafa ya tsare bazai tab'a rabuwa da matar Sa ba musamman a a yanzu da yasan tana son shi duba da irin karyar da tayi don ta kare shi ya tabbata da ayanzu yana gidan yari. Dakyar mahaifin Adnan ya shawon Kan hajiya larai(Mahaifiyar Adnan) Akan idan ta haihu za'a kawo Masa matar sa, Adnan ya nuna shi Sam bai San da wannan zancen ba a haka yasa dole aka kawo Masa matar sa. 'bangaren Malam Hassan kuwa hankalin shine ya kwanta ganin yarsa ta dawo , Kuma ya amince da auren nasu, Haisam ne ya d'auki nauyin jinyar sa zuwa India inda mami da Faisal ne suka tafi, ya daina fushin da yake da mahaifin nasa. Mardiya kuwa Abdallah ya daina kulata tayi kuka har ta kamar idanun ta zasu Fad'o da taimakon Adnan ya hakura har ya tura iyayen sa a nema Masa auren ta. Zuwa yanzu Little Mansur Yana wata shida a yayinda kamanin sa da ubansa yake sake fitowa , a sanadin sane mardiya ta canza ta daina duk wani mugun hali nata, idan bata gun aiki kullum suna tare dashi bata ma barin Isha ta d'auke shi idan kaga ta kaishi gunta to don yasha nonone hatta wanka ita take mishi. *Bayan shekara d'aya* Abubuwa da dama sun faru, Meerah ta haihuwa yarta mace,taci sunan aminiyarta Ayrah, Ayrah don farin ciki har kuka Saida tayi, Malam Hassan Lafiya ta samu sannan Abdallah da Mardiya sunyi auren su babu wani shamaki, a yayin da Haisam Kuma zallan so yake nunawa Isha, don ita kanta ta Fara tsorata da irin soyayyar da yake Mata, Daddy da Abba suka yanke shawarar d'aura musu aure da zaran ta yaye little mansur. Bayan an yaye little mansur, aka sa ranar Auren Isha da Haisam anyi hidama sosai Saida garin gombe ya amsa, Bayan aure kuwa Isha ta koma aiki a karkashin asibitin Haisam, daga bisani Haisam ya hana ya bud'e Mata babban chemist yasa mata masu aiki tana gida kud'i suna Shiga account d'inta, sai da ta suka mori amarcin sa kana ya koma bakin aiki a hakan ma idan ba wani serious abu bane ba Zama yake a gida. *After 5 years* Dukkanin family suna cikin kwanciyar hankali , a yanzu Isha yaranta 6,3 mata 3 maza da Mansur ya Zama Yara 7, Ayrah kuwa yaranta 4,3 mata d'aya na miji Wanda shine d'an farin ta, sai Meerah yaranta biyu da Mai sunan Isha sai kanin ta daga Nan Kuma haihuwan ya tsaya, Nabila ma tayi aure, haka ma Faisal, a haka family din suke cikin kwanciyar hankali sannan kullum suna cikin mutunci da mutun ta juna. Alhamdulillah Alhamdulillah, a yaune na kawo karshen littafina Mai suna DANGIN UBANA, Nagode sosai da goyon Bayan da kuka bani har na samu na kammala. Kuskuren da nayi aciki Allah ya yafemin abinda na fad'a dai dai Kuma Allah ubangiji ya bamu ladan sa dani daku baki d'aya, har kullum Ni din ce Milhaat taku Yar tarewa ku kasance dani a littafina na gaba Mai suna *HAKKIN SO* da fatan zaku bani had'in Kai Nagode.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76