Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 56

Chapter 56

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Masa kofar,Kan gado ta koma ta zauna shi Kuma ya Shiga ban d'aki,alwala yayi Bayan ya gama ne ya fito ya wuce Masallaci ba tare da yace Mata uffan ba. Itama mikewa tayi ta Shiga ban d'aki tayi alwala ta shimfid'a sallah ya Shiga yin sallah,Bayan ta idar ta zauna Akan sallayar tana azkar. Ma'aruf Kuma bai dawo cikin gidan ba har sai da gari ya fara haske,ya Shigo har cikin d'akin bakin sa d'auke yake da sallama,tana zaune akan sallaya, d'ago kanta tayi ta kalle shi suna had'a ido ta kawar da kanta a hankali, amsa sallamar sa tayi had'e da fad'in "Ina kwana" Ya amsa da "Lafiya how was your night?" Tace "Alhamdulillah" had'e mikewa,sallayan ta nad'e kana ta Shiga ban d'aki, Jin saukar ruwa a shower ne yasa ya fice daga d'akin,Bayan ta gama ne ta leko taga baya d'akin fita tayi cikin sauri ta nufi kofar ta sa key. Gaban Mirror ta nufa ta zauna,kallon kanta tayi a mirror ko me ta tuna Naga ta girgiza kai had'e da Yar karamar dariya mai d'an sauti,Mai ta Shiga shafawa a jikin ta Bayan ta gama ne ta ciro kayan da zata sa, Riga da skirt d'in atamfa ta sanya a jikin ta, ba tayi wani kwalliya ba powder ta shafa sai kwallin da ta saka a idon ta sai lip glow. Fita tayi daga d'akin, parlor ta nufa kallon d'akin ta tsaya yi tana ganin kokarin iyayen nata had'e da sa musu Albarka, komai na d'akin Royal Blue ne da Sky blue ya haska d'akin sosai ga wani uban kamshi da d'akin keyi. Motsin da taji ne yasa tayi saurin maida kallon gun, a hankali take ta fiya har ta Isa kofar da take jin karar,a hankali ta Turo kofar had'e da kusa kanta ciki, kallon kitchen d'in ta tsaya yi tana Murmushi,ta shagala da kallon kitchen d'in har ta manta dalilin da yasa ta Shigo. Ido hud'u sukayi,kallon kallon suka Shiga yi wa juna,wani irin kallon yake binta dashi ganin yanda tayi matukar kyau Duk da ba wani cika take dashi sosai ba kayan yabi jikin ta,kamar a jikinta aka d'inka shi. Ganin kallon da yake mata yayi yawane yasa tayi sauri juyawa da niyar fita cikin Murya mai sanyi yace "Isha!!! A hankali ta juya tana kallon sa murmushi yayi kana yace "Kinyi kyau" Murmushi itama tayi had'e da fad'in "Thanks" ta juya zata fita yace "Hold on mana" ajiye spoon d'in dake hannun sa yayi ya nufe inda take hannun ta ya riko ya jaa ta izuwa gun gas cooker da yake girki da ita. Marfin tukunyar ya bud'e yace "Look Waifa gwanin ta zan miki Kuma sai naga baiyi yanda nake gani idan Mama tayi ba" Isha kusa dariya ta Shiga yi Tace " Me ne wannan d'in?" "Bakya gani Irish potatoes ne" "Eh na gani ina nufin me kake son girkawa?" "Chips Mana ai tunda kwanaki ka ka fad'a min kina son chips sosai sai na kudiri aniyar yi miki shi da kaina" Dariya take yi sosai shi Kuma ya rungume hannun sa yana kallon ta cikin Muryar dariya Tace "chips fa kace" ya ama da "Eh Mana" Dariya ta kumayi Tace "ba dai chips ba sai dai pourage" yace "Pourage Kuma gwate kenan fa?" "eh Mana ina ka tab'a ganin chips haka,ai da ka dage ka koya Kan irin ranar Nan tazo" " Uhmn Gaskiyar ki,ai ni yanzu ma gani nake kamar mafarki nake" Jin abinda yace ne yasa ta daina dariya kamar anyi ruwa an d'auke Tace "Ban gane kamar mafarki ba?" "Umm na d'auka bazan tab'a samun ki ba Isha" Murmushi tayi Tace "Kasan mene ne?" Yace "A a sai kin fad'a" Sauke tukunyan tayi kana Tace "bari na nuna naka yanda akeyin chips sabida gaba" Kai ya d'aga had'e da fad'in "to" Nan ta Shiga fere Irish d'in shima wani wukan ta d'auko Yana Taya ta ,sai ta fere biyar bai fere d'aya ba tayi ta dariyar su sunayi suna Hira sama sama,Bayan sun gama ta soye shi had'e da soya kwai ta d'aura a gefe, a tare suka kai abincin dinning,zama yayi tayi serving d'insu suka fara ci. Bayan sun gama cin abincin a tare suka kai kitchen, a parlor ta zauna da niyar Kallo taji yace "d'auko mayafin ki mu shiga mu gaida su Mom" Mikewa tayi had'e da fad'in to, d'aki ta shiga ta d'auko hijab dinta har kasa, tana fitowa suka wuce part d'in su Mom, da sallama suka shiga mom ce na gani a tsaye ita da Mardiya. Baki a bud'e take kallon su Tace "Har kun tashi? Yanzu fa na ke cewa yarinyar Nan ta kai muku breakfast" Neman wuri yayi ya zauna had'e da fad'in "ai mun karya" "Shine kasa 'yata girki daga zuwan ta?" "A a ni nayi girkin fa" Mom kallon Ma'isha tayi Tace "Wai hakane?" Murmushi tayi kana Tace "Na daiyi Mom" "Yauwa nasan za'a Rina" Kama baki yayi yace "Lallai bakya tsoron Allah ina laifin ma kice mata tare mukayi?" Dariya kawai tayi Bata ce masa komai ba, mom Tace "Sai ka nemi wuri ka zauna ka bar ta a tsaye" Gyara Zama yayi kana yace "Yan zun Nan fa Kika ce Yar kice meaning ba sai ance Mata ta zauna ba tunda a gidan su take ko?" Tab'e baki Mom tayi, zuwa tayi ta riko hannun Isha ta zaunar da ita, Ma'aruf kallon Mardiya yayi cikin Murya kamar fad'a yace "Ke baki iya gaisuwa bane? Ko baki ga Mutane bane?" "Uhmn Yaya Kenan ai gani nake kamar Duk Kun manta dani shiysa, ina kwana?" Ya amsa da "lafiya" Maida kallon ta ga Isha tayi taace "Ina kwana Aunty Isha" Murmushi tayi had'e da fad'in " lafiya Lau kin tashi lafiya?" " Lafiya ya Amarci?" Murmushi kawai tayi bata ce Mata komai ba, kallon da Ma'aruf ya mata ne yasa ta ajiye food flask d'in dake hannun ta , had'e da kokarin barin gun. Mom ce Tace Mata "Ya haka Kuma anan Zaki bar min abincin? 'dauka ki Kai musu part d'in su" Cikin sauri ta d'auka ra fita. Ma'isha har kasa ta durkusa Tace "Mom ina kwana?" Cike da fara'a ta amsa da "Lafiya Lau ya kwanan bakonta?" Murmushi tayi had'e da fad'in "Alhamdulillah" Ma'aruf ma gaishe ta yayi Bayan sun gama gaisawa yace " Dad ya fita ne?" Ta amsa "Yana d'akin sa , ku shiga ku gaishe shi" mikewa yayi had'e da kallon Ma'isha yace "Zo muje" mikewa tayi Sim sim tana binsa a baya, d'akin Dad suka nufa Bayan sun gaishe shi ya musu nasiha da fatan Allah ya basu zaman Lafiya Mai d'aurewa, Nan suka tashi suka koma part d'insu kasantuwar Mom bata parlor d'in. "Mamy yanzu haka zamu zuba Ido muna kallon Daddy yana abinda ya ga dama a gidan Nan ki duba kiga yau ma ya shigo da mace" Faisal ke wannan maganar. Sunusi yace "Mata dai ai su biyune yau Kam" Faisal yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, that's it Wallahi yau d'in Nan zan yi maganin Yan iska" ya mike Yana huci yayi d'akin sa. Mamy kallon sa kawai tayi ta kawar da kanta, Sunusi yace "Mamy Wai baza kice wani abu bane ba?" "To me zance muku tunda

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});