Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Nan da Nan jama'ar unguwa suka Fara shigowa cikin gidan kowanne da abinda yake tufawa. Fire service aka Kira ,basu d'au wani lokaci Mai tsawo ba suka iso , suka Shiga kashe wutan, Isha da Mardiya kuwa a motar Meerah aka sasu sai asibiti. Bayan wutan ya d'a tsagaita suka Shiga ciki don duba 'barnan da wutan yayi, Mutum uku suka gani a parlor, Mutum biyu suna zaune a kujera Wanda Mom da Dad ne, yayin da d'ayan Yana kwance a kasa shine Ma'aruf. Nan aka Shiga fitar da gawakin su a waje kowa ya jinjina al'amarin cike da tausayi suke ta kallon su,yayin da masu saurin kuka Kuma sai kuka suke suna yabon hayyyan su musamman ma Dad da Ma'aruf. Bayan sun Isa asibiti, taimakon gaggawa aka Basu, yayin da Meerah ta Kira Dad ta Sanar dashi abinda ya faru, anyi sa'a Yana gari, a lokacin suna gidan Umma shi da Mummy, a razane ya mike zufa na keto Masa, mummy da Umma a tsorace suke tambayar sa abinda ke faruwa, Daddy kallon Abba yayi kana yace "Zo muje" ya fice Abba kuwa yabi Bayan sa ba tare da yaji inda zasuje ba, bin Bayan su sukayi suna tambayar ko Lafiya. Daddy waigo yayi cikin Murya kamar Fad'a yace "Ku koma ciki" Jin yanda yayi maganar Umma ta riko hannun Mummy suka koma ciki, motar daddy suka Shiga. Daddy ne yake jaan motar, a hanyar ne yake Sanar dashi abinda ya faru, Banda ambaton sunan Allah babu Abinda yake har suka isa asibitin dasu Isha suke, suna dosan d'akin da Isha take suka jiyo ihun ta cikin Muryar kuka take fad'in "Dan Allah ku sake Ni, Meerah Ma'aruf fa wayyo na Shiga uku" Meerah itama kukan take Amma bata sake ta ba, da taimakon wata nurse suka rirrike ta, Isha na ganin su Abba da Daddy da dukkanin karfinta ture su ta nufi inda suke cikin kuka Mai sautin gaske, tana fad'in "Daddy Mijina na Shiga uku" ta maida kallon ta ga Abba tana fad'in "Abba ya mutu ko? Shikenan Shikenan na shiga uku, yanzun Nan fa mukayi magana dashi, Innalillahi wa ilaihirraji'un" Daddy ne ya rungume ta Yana fad'in "Ya isa Isha ki daina kukan hakan" Amma kamar cewa yayi ta Kara kukan ne, Abba waje ya fita yace su Umma suzo asibitin, Amma bai Fad'a musu dalilin kiran suba. Isha tafi Mintuna talatin tana kuka, Abba da Daddy suna rarrashin ta, Meerah kuwa ta rakub'e a gefe itama kukan take sosai, Su Mummy suna shigowa suka halin da take ciki, cike da rashin fahimta suke kallon su. Abba ne ya Sanar dasu abinda ya faru, mummy fashewa tayi da kuka da zaran ta kalli Isha sai ta fashe da kuka, Umma ma kukan take, Isha mikewa tayi ta rungumi Umma tana kuka. Meerah fita tayi bata dad'e ba ta dawo hannun ta rike yake da goran ruwa Tace "Umma ki bata tasha, ko zata d'an ji sanyi" tayi maganar cikin sanyin Murya da jin tausayin kawar ta. Dakyar da makyar kyasa Isha ta Karb'a tasha, bata d'auki mintuna biyar ba ta fara Jin jiri, Umma na ganin hakan tayi saurin kaita Kan gado. Nan hankalin su ya Kuma tashi Meerah Tace "Ni Nasa mata maganin bacci zata kwana tana bacci, ina tsoron Kar ciwon ta ya tashi" Abba yace kin kyauta, Duk suka tsaya zugum suna kallon ta, Nan Abba yace " Meerah ya akayi hakan ta faru?" "Abba muna tsaye ne a compound d'in gidan, ya Dawo cikin gidan da fara'a yace ya Dawo ne ya sabida mahaifin sa ya Dawo, yana Shiga cikin gidan bai dad'e ba kawai muka ji wani irin Kara, sai wuta ya kama" Daddy yace "Ha'aaah karar me?" "Ina tunaniin gas ne ya fashe sabida gidan Duk ya d'auki Warin gas" ta karasa maganar cikin Muryar kuka. Abba yace "Allah sarki yaron kirki ya mutu da kuruciyarsa da rabon bazai bar baya ba" Yana girgiza Kai, Meerah bayan hannun ta ta saka ta share hawayen dake fuskan ta tace "Ya bari, sabida yanzu haka Isha na d'auke da cikin wata har na tsawon wata biyu" Duk da hankalin su ba a kwance yake ba bai hanasu murmusawa ba, suna Mai hamdallah, ganin Isha na bacci hakan Yasa suka fita, d'akin da Mardiya take suka Shiga, tana zaune akan gadon marasa Lafiya tayi shiru bata vko motsi har suka shigo bata sani ba, Umma ce ta zauna a gefen ta Tace "Kiyi hakuri 'yata iyayen ki da Yayan ki sunyi mutuwar shahada, sai dai muyi hakuri" 'dago kai tayi ta kalle ta kana ta maida kanta kasa tana wasa da yatsun hannun ta. Nurse ce ta Shigo da sallama Bayan sun gaisa Tace sun sallame ta, Mardiya najin hakan zumbur ta Mike zata fita mummy ce tayi saurin rikota tana tambayar ta "Ina Zaki?" "Gida" tana kokarin ficewa, daddy yace "Umman yara driver na waje ne?" " Eh" "Okay ku tafi gida tare, please ki kula da ita" ta amsa da to had'e bda mikewa, hannunta ta rike suka fice, mardiya bin Umma kawai take kamar wata sakarya har suka shige cikin motan, suka fice daga asibitin. Ayrah na gun aiki ta ji labarin abinda ta faru a gun wasu staffs da ke Hira da saurin ta, ta fice daga asibitin motar ta ta Fad'a ta fice. Driving take kwasam motarta ta 'dauke, buga steering motar tayi ta fad'in "Damn it!!! Fita tayi tana dubwa ko zata ga mechanic Amma Babu, kwasam wata mota tayi parking a gaban ta, ga mamakiin ta Adnan ta hango ya fito daga motar, baki a bud'e take kallon sa. Cike da tsoro ta ke kallon sa a hankali yake takawa Yana tafiya cike da izza, Jikin sa sanye yake da T-SHIRT da Jeans,fuskan sa d'auke yake da eye glass hannayen sa a cikin aljihun sa, sai da ya isa daf da ita kana ya zaro Hannayen sa ya rungumi kirjinsa sa yace "I told you idan Kere na yawo zabo na yawo wataran Dole a had'u ko?" Ya karasa maganar yana matsowa kusa da ita a hankali take ja da baya jikinta na rawa, don a matukar tsoro take, sabida irin kallon da yake mata Kallo ne na tsantsar tsana. Murya na rawa Tace "Adnan please, ka kyaleni na tafi Dan Allah, me na maka, nifa Babu abinda na maka" "Shutttt up jaka wawuya" a tsawace yake maganar, Yar karamar wuka ya zaro a aljihun sa yana nuna Mata had'e da fad'in "wuce muje" "Inaaa..... Inna.. Ina zamuje.....?" "Zaki wuce ne ko Kuma zaki tsaya tambaya ta na Burma miki wukan Nan a ciki?" Yana Mai nuna Mata motar sa. Ayrah ganin gun shiru ba kowa, Kuma zai iya cutar da ita hakan yasa ta nufi motar nasan da d'an sauri Tana yi tana waigawa ko zata ga wani Amma har ta shige motar babu Wanda ya gifta ta wajen. Shima motar ya Shiga ya jaa motar suka bar wajen, tafiya suke har Saida suka fita a cikin gari, parking yayi kana ya kalleta ya murmusa, handkerchief ya zaro a aljihun sa ya Mika Mata had'e da fad'in "Kar b'i ki share hawayen ki" Kin Karb'a ta yi a tsawace yace "ki

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});