Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

Dangin Ubana Book 1 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

'boye musu asalin Haisam ba gudun Kar wani abu ya gifta suce an musu karya, Bayan sunji bayanin su Daddy suka amince da had'in tunda yara suna son junan su babu 'bata Lokaci suka amince da bukatar su, hakan yasa aka sa ranar aure Nan da wata biyu, drinks ne Niki Niki a gaban su daddy da namomin kaji Amma basu tab'a komai ba suka fice. Haisam na ganin su Daddy yace "habibty ganan su Daddy sun fito zamuuyi waya anjima" Cikin muryar Shagwab'a Tace "Bazan ganka ba Kenan?" "Zan dawo anjima insha Allah, bari Muji yanda sukayi tukunna" "Insha Allah,Mai dad'i ne sabida dad yasan ina son ka,Kuma yana son abin da nake so" "To Masha Allah,I'll call you later." ya katse wayar. Su dad kuwa har jikin mota suka raka su daddy hakanne ya tabbatar Masa da cewar bashi da sauran matsala,ai kuwa suna fita a gidan daddy ya Sanar Masa da and ranar bikin Nan da wata biyu, Haisam farin cikin da yake ciki ya kasa 'boyewa, gidan Abba Suka nufa Umma taji dad'i ta wani 'bangaren wani 'bangaren Kuma bata ji dad'i ba Sam,sabida kullum burinta shine Haisam ya auri Ma'isha tayi wa Abba korafi yayi saurin dakatar da ita akan ba a yi wa d'an yau auren Dole. Shiri suka Shiga yi duka family Ma'isha ma ba'a barta a baya ba,idan tana cikin Mutane ta nuna tafi kowa farin ciki yayin da idan tana d'akin ta Kuma taci kukan ta,son ranta idan ta gama ta wanke fuskar ta. Yau saura sati d'aya bikin Aysha da Haisam, Ma'isha da Meerah na gani zaune a cikin Masallacin asibiti da alama sun idar da sallar ne "Isha kiyi hakuri Dan Allah, Rana ita yau fa auren su,kema sai da nace miki ki tura Ma'aruf Amma kinki har karya fa kikayi wa Daddy cewar Ma'aruf baya Nan Bayan kuma yana Nan,ban San dalilin ki nayin hakan ba" " Dalili d'aya ne kema kin sani,Haisam nake so ba Ma'aruf ba" "Na sani amma ai Haisam d'in aure zaiyi ko?" "Eh Ana gama auren sa zan fad'awa Ma'aruf ya fito" "Ikon Allah,to Allah ya nuna Mana" "yanzu Meerah ya Haisam aure zaiyi fa ko? Kuma wata zai aura bani ba?" Ta fashe da kuka Mai cin raai har Saida sauran staffs d'in suka Fara kallon su rarrashin ta Meera keyi sai da tayi mai isarta ta Mike Kenan ta yanke jiki ta fad'i sumammayi. ____________________________ Please Comment and share Mihaat Ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 39&40 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........._ Cike da fargaba da tsoro suka chiccibeta suka kaita A&E (Accident & Emergency) Nan da Nan likitoci sukayi kanta, kwata kwata bata numfashi da taimakon Oxygen ta fara numfashi, Haisam kuwa yazo wucewa ne don duba patient d'insa ya hango meerah na ta aikin kuka, da sauri ya karasa inda suke ganin Isha ce a kwance bata motsi ya birkice Yana tambayar su "Me ya same ta ne?" Wurin Meerah ya nufa Yana tambayar ta "Meerah what Happened to her? Me ya same ta? Please ki Sanar dani" Cikin kuka Tace "Yanke jiki tayi ta Fad'i" Likitane ne ya juyo yace "Dr Haisam, itace sister d'inka ko?" Cikin rawar murya yace "Eh itace" "To ya akayi kuka bari har ciwon zuciya ya kamata?" Zaro Ido yayi yace "What ciwon zuciya dai? But how comes?" Kafad'ar sa ya d'aga had'e da fad'in "I don't know, thank goodness ma ta samu kulawa cikin gaggawa da an rasata Kai ma kasan irin wannan lokaci d'aya mutum yake mutuwa ko Kuma ya kamu da mutuwar 'barin jiki" Haisam dafe kan sa yayi ya jaa da baya ya jingina da bango yana kallon Ma'isha da haryanzu oxygen na hancin ta, d'an bubbuga shi likitan yayi kana ya fice dashi da sauran nurses d'in. Kallon Meerah yayi yace "Dan Allah ki Sanar dani me ke damun Princess nasan kisan komai a kanta sabida kinfi kusanci da ita fiye da kowa" Kai a kasa tace "Ni ban san komai ba, babu abinda na sani" Girgiza Kai kawai yayi ya Koma kusa da ita ya zauna ya sanya hannunta a cikin nasa Yana ta kallon ta, sai yamma ya tuna bai Kira su Mummy ba, Nan ya kirasu ya Sanar dasu, ba dad'ewa Mummy da Daddy suka zo, mummy na ganin halin da yarta ke ciki ta Shiga rera kuka dakyar daddy ya samu ya rarrashe, a takaice dai Ma'isha a haka ta kwana bata farka ba ta kwana ta wuni tana bacci, sai yamma lis ta bud'e idon ta haisam da kanshi ya duba ta, ya mata alluran da ya kamata, aiko ta sake komawa bacci. A takaice dai Ma'isha Kwanan ta uku a gadon asibiti, sai da ta d'an Samu sauki aka sallame ta, a cikin Yan kwanakin Nan ta rame ta lalace Kamar ba ita ba, kuka kuma sai abinda ya karu,mummy da daddy sunyi rarrashin sunyi fad'an Amma taki fad'a musu, mummy Tace "Ma'isha idan baki fad'an min damuwar ki ba wa Zaki fad'awa umm? Ki duba kiga yanda kika lalace fisabilillahi baki kyauta wa Kanki ba wallahi" "Mummy nifa ba abinda yake damina" "Idan babu abinda ke damin ki me ya kawo miki ciwon zuciyar?" "Uhmnn mummy ciwo ne kawai daga Allah ba wani abinda yake damina" "Toh naji kukan da kike Kuma fa? Ki duba abincin Nan da sadiya ta kawo miko tun na safe baki ma tab'a shi ba" "Zanci Mummy" "A gaskiya Ma'isha bana Jin dad'in ganin ki a haka Dan Allah........ " Sallamar da akayi ne ya katse ta amsawa tayi had'e da kallon kofar don ganin wane ne, Murmushi Umma tayi Tace "Ameerah kece?" "Eh Mummy ina wuni?" "Lafiya lau ya gida ya su maman naku?" " Suna lafiya sunce a gaishe ku da maie jiki" "Allah sarki muna amsawa , sannu Ameerah Allah ya biyaki sai faman wahala

Table of Contents

Chapters

76 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});