Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,229 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ne kuwa? Anya ba son Asma'u yake ba? Take tambayar kanta, in kuwa hakane babu shakka rayuwar ta tana cikin garari domin baza ta iya had'a miji da Asama ba, gashi duk duniyar nan babu namijin da take so kamar sa, tana ganin sai da ta mutu babu aure. Wayar ra dauka tana neman numbar sa, bugu guda ya dauki wayar, cikin siriryar muryar ta tace"My kayi hak'uri don girman Allah nasan ranka yanzu a b'ace yake, babu shakka Asma'u bata kyauta ba." Ajiyar zuciya ya sauke a kashi d'ari na damuwar sa kashi casa'in ya ragu , yaji dadin maganar Mimi yace." Momyna 'yar uwarki bata da kirki wallahi kanta rawa yake yi, ki rink'a yi mata fad'a kinji ko." Mimi tace"Kullum kuwa cikin fad'a muke yi da ita Sam! Asma'u bata son San gaskiya, wallahi." Ina ji ina sallahr lallai Mimi har sunyi sabon da zata dinga kai suka ta a gurin shi.sauri nake in idar muyi wacce zamu yi da ita. Ina jinsa yace." Kar ki biye mata da duk abunda zata yi miki na rashin mutum ci domin na lura tashan balaga take, idan tayi ba dai-dai ba ki yi mata fad'a koda zakuyi doke-doke da ita kuwa." Mimi tace." Insha Allahu kar ka damu." Yace." Zan dawo gobe ko jibi kiyi min kwalliya me kyau sannan ki turo min pictures dinki ta whatsp zan gani." Cike da kunya tace" shikkenan ka bude data zan turo maka." Sallama sukayi Mimi tana saki murmushi daga ni tana cike da farin ciki. Ina idar da sallah ko addu'a banyi ba nayi kan Mimi da masifa nace "Mimi kin Dade baki kai suka ta gurin sa, ba ki fad'i abunda ya fi haka a gurin shi ba damuwa ta bace, kece yake gaban ki da har idonki ya rufe a kansa kika kasa fari da bak'i aikin banza aikin hofi ina kara dai tunasar dake cewar kiyi hattara ki kula idan ba haka ba ke zai kai ya Baro....Wannan karon Mimi bata k'yale ni ba, itama a fusace ! Tayo kaina tare da fad'in" duk abunda zaki fada ki fada ke ya shafa kowa rai yayi wa dad'i ba kamar me shi ba ne Asma'u kije kiyi abunda kike so kuma wallahi kar ki sake ki kara zagina domin uba bai fi uba ba. " Kanta nayi zuciya ta namin zafi nace" Sai nayi RAYUWAR ki ce ko tawa dake dashi da Yaya Aminu kusa tsinken tsire ku tsikare n......Ban k'arasa ba naji saukar Mari! Da sauri na dafe fuskata ina kallon Wanda yayi min haka, Umma ce tsaye tsakiyar dakin ranta a mugun bace tace" Tsokane mata ido zakiyi ne Mara kunya."? Shuru nayi hade da sunkuyar da kaina kasa ta cigaba da cewa." Duk rashin mutumcin da kikayi ina jinki, ina ce Mimi ta girme ki da har kike tsaye kanta kina nuna ta da d'an yatsa kan ta fada miki gaskiya." Mimi tace"Umma kiyi hakuri don Allah." Tace" ke zan bawa hakuri Mimi da kike k'okarin nusar min da ita, duk da rashin mutumcin da take miki." Mimi tace"Umma wannan duk abunda ya shafe mu ne, dama mun saba fad'a haka." Cike da tausayi take kallon Mimin ta rasa wace irin zuciyace da ita, tace." Ba irin wannan fad'an kuka saba ba. Ke kam zuciyar ki tana da sanyi ina addu'ar kar Allah ya kai gidan me mata ki sha wuya domin kishiyoyin ki zasu raina ki wallahi." Shiru Mimi tayi. Ita kuma Umma ta kama hanyar futa, D'an juyo wa tayi tana kallon katifar mu, waya ta gani tamfatsetsiya cike da mamaki tace"Wannan wayar waye a cikin Ku."? Shiru mukayi dukanin mu.Cike da zargi da tuhuma tace." Ba tambayar Ku nake ba."? Baki na rawa Mimi tace"Tawa ce Ummah." Cikin mamaki tace "Mimi yaushe kikayi magana babu labari." Yanda Umma ta fad'i maganar kai tsaye ya tabbatar mana da cewar Hankalin ta ya tashi. Da sauri tace"Mik'omin wayar nan." Hannu na rawa Mimi ta mik'a mata, ta karb'a had'e da fucewa daga d'akin. Shuru muka yi dukanin mu, yanzu na daina jin taikacin komai nayi kwanciya kawai a zuciya ta nace"Ke ma abunda ake min a gidanan yazo kanki sai kiji in da dad'i baya na juya mata ina lumshe idona babu abunda ya dame ni, injita ta kwanta itama jikinta duk yayi sanyi. K'arfe takwas dai-dai naji hayaniyar Ya Aminu a kaina rumtse idona nayi da k'arfi ina fadin"Ya Aminu Dan bala'i ne wallahi. "Ke Mimi tashe ta kuzo rumfar Umma ina Neman Ku." Yafad'a cikin daga murya. Futa yayi ita kuma tafara tashi na, tsaki ns buga ina kara gyara kwanciya ta, tace"Nasan dai kina ji tom Ya Aminu ne kin san dai halinsa. Nace"Kije ke ni kam babu inda zani." Mik'ewa tayi tana fadin "Taurin kanki ne yake jawo miki komai. Ina jinta ta futa, minti biyu na mike nima domin tsoro ne ya shige nasan halin Ya Aminu bai k'i ya shigo ya dake ni da sanyi safiyar nan ba. Ina shiga dakin Umma na yadda Aunt Hauwa har tazo suna ta mai da magana, zama nayi gefan ta muka gaisa hannun Islam na jawo INA fadin " Baki je makaranta ba yau."? Aunt ta kalle ni tana nazari tace"Ke kuma waye ya fasa miki gefan fuska." Kwallah ce ta taru a idona nayi shiru hade da sunkuyar da kaina. Yaya Aminu yace." Nine nan! Na fasa mata idan kuma tayi min gaddams kan abunda zan tambaye ta yanzu to bakinta zan fasa mata har sai hakori ya futa." Kallonsa nayi cike da rashin tsoro, cikin tsawa yace." Ki fada min a ina kika samo wannan tafkekiyar wayar me uban tsada kin San kuwa kud'inta,? Nasan wayar taki ce, Mimi ta rufa miki asiri ne kawai kamar yanda ta saba." Mimi na kalla dake wasa da hannunwan ta nace"Abunda kike zo kika CE musu kenan."? Da Jan ido ta kalle ni, nace"Kiji tsoron Allah Mimi." Murya na rawa tace"Umma me nace tunda Nazo gurin nan." Umma tace"Baki ce komai ba zargi take." Ya Aminu na kalla fuska a hade nace" Waya ta Mimi ce don haka ita zaka tuhuma bani ba, yanda ka ganta nima haka na ganta. " *4/November/2019* [11/4, 5:49 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *Mallakar_BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.* *40* Yaya Aminu ya kalli Mimi cike da mamaki domin bai tab'a tsammanin faruwan hakan daga gurin ta ba, a nutse yace." Hakane Mimi."? Gyda kanta tayi tana k'ara sunkuyar da kai kasa, aunt Hauwa tayi karaf tana fad'in"dama baku San da wayar a hannunta ba."? Umma tace"Bamu sani ba Wallahi sai yau" aunt tace"To ai ko lokacin da suka je gidana da wayar a hannunta yau kwanansu Uku kenan." Umma ts tsare Mimi da kallon tuhuma tana fad'in" Ki fada min gaskiya Mimi wannan wayar ta wacece tsakanin ke da Asma'u. "Mimi tace" Wallahi Umma tawa Ce." Tace" waye ya baki ita." Shiru tayi, da k'arfi Ya Aminu yace." Ba tambayar ki ake ba." Cikin inda-inda tace"Amjadu ne." Dukaninsu jikinsu yayi sanyi Mussaman Aminu Umma tace"Kina nufin yaron nan mai company ko me."?

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});