Chapter 30
Chapter 30
tab'a fad'ar alkairina ba sai yau. Murmushi naga tana yi kunne na kasa sosai ko zan ji abunda yake fada mata Wanda yake sata sakin wannan kayataccan murmushi, babu abunda nake ji daga b'angaran sa saboda ya k'ara yin kasa da muryar sa sosai, ita kanta Mimi sai ta kasa kunne sosai sannan zata ji abunda yake fad'a. Ji nayi zuciyata nayi min wani irin zafi nayi saurin kauda kaina tare da ambatar innalillahi cikin zuciyata domin ji nayi take wani kunci ya ziyarce ta, zuciyar tawa sai take raya min kamar da akwai wani munafurci a ciki don me yasa zai dinga magana a waya kamar munafuki wannan bayi bane ni a ganina. Maganar da Mimi tayi ce ta dawo dani hayyacina , wayar take mik'o min tare da fadin"Yace." A baki wayar ku yi sallama." D'aga murya nayi domin yaji nace"Mimi kashe wayar nan don Allah bacci nake ji, tunda dai kun gaisa dashi shikkenan dama haka nake so in sanya zuciyar ki farin ciki, kashe wayar mu kwanta Wallahi nayi bala'in gajiya." Ga mamaki na sai naga Mimi ta kashe wayar kamar yanda na umarce ta ta aje wayar gefan kamar ba ita ta saki fuska sosai tana yi min hira. Mamakin ta kawai nake, nace ta kashe waya ta kashe babu kara bare tayi min magiya kan in karb'i wayar kamar yanda ya bukata, lokotan baya idan taga ina mishi wulakanci haushi take ji amma banda yanzu. Kwanciya nayi gefan ta ina lumshe idona sama-sama naji muryar narse na shigo tana tashina, na bude idona Wanda suke cike da bacci ina kokarin mik'ewa zaune. Mimi tace" Ki k'yaleta mu kwana tare domin ko a gidama a tare muke kwana." Nurse ta futa bata kara magana, sama-sama muke yin hira da Mimi bacci yaci karfina ban San sanda ya kwashe ni ba. Shida shaura na Safiya na tashi lokacin har masu bada magani sun shigo dakin sun bawa Mimi wacce take zaune dungurgur taki yin bacci saboda tsabar farin ciki, mik'ewa nayi ina hamma idona cike da bacci nace." Mimi shine baki tashe ni ba ko? Kinga na rasa sallah asubah." Murmushi tayi tare da fadin "Asma'u naga a gajiye kike gashi kince bacci kike ji shiyasa na kyaleki kiyi hakuri." K'wafa nayi kawai na sauka daga gado toilet din dake cikin dakin na shiga. K'arfe takwas dai-dai likita ya shigo ya gama aune-aunen sa kan Mimi kuma yaji dad'i da ya duba yaga yanda ta kwantar da hankalin ta, nan ya rubuta sallama hade da kara tausar Mimi sosai kan ta kiyaye ta daina saka damuwa a ranta. Nima kuma yace." Mu dinga sanya ido ankata sosai muna guje b'acin ranta. 9:00 am mun futo daga asibiti da bamu shigo da kaya komai ba amma zamu futa dasu niki-niki a hannu muna futa harabar asibitin wata shirgegiyar motar *Siyana* mai dauke da tambarin *A&A mai nasara* sabuwa dal! Ta shigo gurin, Dravar shi ne ya futo da sauri muka hada ido dashi. Saurin kauda kaina nayi daga kansa Ya k'araso gurimu hade da zubewa gaban Umma yana gaishe ta ta amsa a sake, Ummansu Munnu ma ta amsa ita da aunty Hauwa, sai ya mike hankalinsa na kaina yace." Ranki ya Dade oga ne yace in zo in kaiku gida." Cikin zuciyata nace shi kuma ko wa ya fada masa anyi sallama oho! Shiru nayi masa, aunt hauwa naji tana fadin"Aikuwa mungode dama yanzu muke tunanin a dai-dai ta nawa zamuyi damu da kayan mu." Na muka nufi motar kowa na fadin albarka cin bakinsa. Duk yawan mu damu da kayanmu motar sai da ta dauke mu, hat guri Yayi saura doh-doh yaja motar muka tafi gida, Mimi ta sake sosai ina jinsu suna hira da Munnu ban tanka musu ba. Goma shaura muka Isa gida Har ya danyi kura saboda rashin mutane a gidan kwana biyu kawai, ni da Aunt Hauwa muka fara aiki Ummi da Mimi kuwa na rumfa daga inda muke muna jin yanda Umma take rarrashin Mimi da kalamai Masu dad'i da kwantar da hankali. ****** Yau Kwana ki biyar kenan da bud'e sabon company me zaman kansa a jahar kano company *A&A mainasara* ya amsa sunansa sosai ya samu daukaka domin an fara gudanar da harkoki yanda ya kamata kullum a cike yake da baki daga garuruwa daban-daban sun shigo d'aukar kaya. Hakanan Sauran company sa na waje suma komai ya kammala harkoki ake sosai da sosai Allah ya shiga al'amarin. Sanye yake da wani yadi mai masifaffan kyau da tsada ni kam sai ince ma a jikinsa na tab'a ganinsa milk coulor ne mai sharashara anyi masa dinki boda yayi amfani da singlet black kana ganin shatin ta, bai sanya hula ba taje lafiyayyar sumar sa yayi wace take bakkirin sai shek'i take, ya gyara sajan sa kamar ko da yaushe ya feshe jikinsa da turaran shi na ko da yaushe, takalmi mai gidan ya tsa ya sanya a fararen k'afafun shi, blck ne sunyi masa kyau ba kad'an ba, hannunsa daure da agogon shi, na zallar fata fad'ar kudin shi ma b'ata wa ne, komai na Amjadu colour ne domin bai fiye amfani da Abu gama gari ba. A nutse ya futo hannunshi rike da wayoyin shi, kana kallonsa zaka fuskanci akwai damuwa a tattare dashi Dan dai jarumin namiji ne me b'oye damuwar sa. Harabar gidan ya futa, Doh-doh da Rambow suna tsaye kamar dogarai suna ganinshi ya futo Rambo ya nufi inda yake shi kuma doh-doh ya fara kokarin futo da mota. Wayoyinsa ya karb'a yana yi masa barka fa futowa a dakile ya amsa masa ya wuce shi kuma ya bi bayan sa, motar ya bude masa ya shiga ya zauna shi kuma ya zaga ya gurin zaman shi, motar ta futa daga gidan. Sai da sukayi nisa sosai Doh-doh yace." Oga ina muka nufa."? Zaman shi ya gyara tare da Dan ya mutse fuskarsa yace." Muje gidan granny ko." Doh-doh yace." Angama sir." Wayarsa guda ya karb'a gurin Rambo ya fara laluben numbar jiya yaji mugun haushi abunda tayi masa ta sanya Mimi ta kashe masa wayar wato bata buk'atar tayi magana dashi abunda yarinyar take ya soma b'ata masa rai, Sam bai saba ganin wannan shariyar ba a gurin 'yan matan da suke son shi, amma yana ganin dole zai rage zak'ewa a kanta ko zata gane muhumamcin sa. Cikin ikon Allah da ya kira wayar itace ta dauka muryarsa shi a cunkushe ya amsa mata sallama minti biyu tsakani yace." Kina jina ko."? "Umm." Abunda tace kenan. Yace." Munyi waya da dector d'azu an baku sallama shine na turo Doh-doh ya dauke ku a mota babu wata matsala ko."? "Ummm."! Nace. Haushin yanda take masa yaji Umm da Umm sai kace wata kurma, k'aramin tsaki yaja yace." Yanzu zanje in dauko granny zata zo ta duba Momyna." Sama-sama nace"Sai tazo." Kafin na an kara ya kashe wayar a fusace.! Tab'e bakina nayi nace "Kai ka sani kuma. Umma na fad'awa zuwan kakar shi ta tashi ya fara shiri aunt Hauwa na shirin tafiya gida Umma ta hana ta wai ta tsaya su tab'i bak'uwa sosai a ka gyara gidan duk a ka kauda kayayyakin sana'ar Umma dasu ke rumfar tamu kamar su kalazinr
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78