Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kai a gogonsa ya d'aura ya dauki key ya futa da sauri. Rbow suka ji ana kokarin tada mota hankali a tashe suka futo daga gurinsu, suna tambayar sa yace." Su koma kawai shima yanzu zai dawo jikinsu duk babu k'wari suka tsaya a gurin har sai da suka ga futar shi Daga gidan. Kai tsaye......Asibitin Zana ya nufa zuciyarsa kwata-kwata babu dad'i abun yana mutukar bashi mamaki shi dai yasan babu wata Kalmar so da ya tab'a fadawa Mimi wacce har suke zargin sa da ya yaudara ta, maganar auran ta kuwa ya fada ne saboda son da take masa gami da ganin yanda suka shak'u da Asma'u yana ganin ko ya aure su su biyu ba za a samu matsala ba, yanayin dabi'un Mimi da nutsuwar ta gami da kunyar ta suna bashi sha'awa amma zallah so gangariya babu Wanda yake wa sai Asma'u duk cikin 'yan matansa babu wacce ta samu wannan matsayin kamar ta hak'ika Asma tana da babban matsayi a zuciyarsa. Da wannan tunane-tunanen ya Isa asubitin, Madi suka bude masa kofar ya shigo cikin sauri suka biyo motar da gudu yana parking suka bude masa kofa suna yi masa barka da zuwa. Amsa musu yayi babu yabo babu fallasa, ya wuce ciki. Suka tsaya suna binshi da kallo tare da tunani wane dalili ne ya kawo shi asibitin ? Suna zargin yau ya zagayo su ne duba marasa lafiya da. da bada tallafi kamar yanda ya saba, murna suke sosai yau zasu cika aljihunansu. Wayarsa ya futo da ita yana laluben numbar da ta kira shi da ita yanzu.... *10/November/2019* [11/11, 9:19 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *Mallakar_BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.* *48* Ringing d'in wayar ne ya dawo dani cikin hankalina wayar na duba sai naga numbar sa, da kamar kar in dauka wata zuciyar tace"Dauki kiji me zai ce miki. Jin alamun ta daga wayar ne yasa yace." Gani cikin hospital din ki futo kiyi min jagora har inda kuke." Bai saurari Abunda zata ce ba ya kashe wayar sa. Futowa nayi daga gurin da nake. Har yanzu suna tsaye kan Umma sun yi mata rumfa Aminu sai fiffita yake mata. Aunt Hauwa ta kalle ni tare da fadin"Da ina kika shiga tun d'azu. " Cikin wayan cewa nace"Futsari naje nayi." Raba ido nake yi a gurin ko Allah zai sanya I n hango shi Da yanayin tafiyar shi na gane shi. Shiru nayi har ya k'araso gurin. Cike da mamaki suke kallonsa. Ya mik'awa Aminu Hannu su gaisa. Da kyar ya mik'a masa nasa hannun kamar yanda yayi masa jiya. Umma ya kalla yace." Umma Ashe bayan tafiya ta jiki ya rike CE." Umma ta gyara zamanta hade da gyara mayafin ta tace"Wallahi kuwa aman jini take sosai." Gaban shi ya fadin jin abunda Umma tace, Yace." Bari in ga dector babu matsala insha Allahu komai zai zo da sauki." Binsa mukayi da kallo har ya shige ciki abun mamaki babu Wanda ya hana shi shiga cikin ma'aikatan sai ma da d'a gyara masa hanyar wuce da suka yi. Kamar yanda dector ya yiwa Kawu Baya ni haka yayi Amjadu baya ni Wanda ya gamsar dashi kuma shima ya gane kan ciwon Mimi kamar yanda Asma'u take fada cewar ciwon sonsa ne yake damunta. Yace." Doctor yanzu kun gama komai ko."? Gyada kai Dr yayi tare da fadin"Mun gama komai dasu domin har sunje sun karb'o magani a pharmacy kuma yanzu na sanya nurse ta bata maganin babu matsala insha Allahu mutukar an bi doka." "Yanzu sauransu biyan kudi domin yanzu nake cewa Narse ta zo mik'a musu rasit." Yace." Kar ka damu insha Allah ka bani numbar accont din Ku na hospital din sai a turo maku hakkin Ku. Da sauri Dr ya dauki 'yar k'aramar ta karfa da biro ya rubuta masa hade da mik'a masa, ya San ba iya kacin kud'in su zai tura musu ba Dole sai yayi musu kari, tunda dama ya saba kawo musu ziyara a sibitin. Har ya mike zai futa sai kuma ya tsaya tare da fadin"Yanzu babu halin a ga yarinyar. " ? Dr ya mike da sauri yana fad'in"A'a Yallab'ai kai zaka iya shiga ka ganta." Tare suka shiga room d'in da Mimi take kwance bacci take sosai sai dai har yanzu nuffashin ta bai gama dawo wa normal ba. Dr ya futa hade da jawo masa kofar , ido ya tsura mata sosai yake kallonta mace har mace tana Neman ta jefa rayuwar ta a wahala. Domin shi a ganinshi wahala ce,kaso Wanda bai San kana yi ba, bai tab'a tunanin son da Mimi take masa ya kai haka a zuciyar ta, sai yaji zuciyar sa tana ce masa da ma wannan Soyayyar daga gurin Asma'u ka same ta daka ji dad'i. Amjad mutum ne mai mutukar son a dunga tattashin sa da rarrashin sa kulawa da soyayya, shiyasa yake addu'ar Allah ya bashi mace wacce take da wannan azanci domin matan ma suna suka tara. Yafi minti goma a tsaye a kanta yana kallonta, kokari yake yaji wani abu wanda ya shafi so ya darsu a zuciyarsa a game da ita, bai ji komai ba sai dai tausayin da taye mata da kuma kaunar da yake mata saboda sunan Maman shi, Wanda ba ita kadai yake wa wannan kulawar ba, mutukar A kace kina da suna Aisha to zaki samu kulawa sosai a gurin shi. A gogon dake daure a hannunsa ya kalla hud'u shaura na Asubah. Gyad'a kansa yayi ya bude kofar dakin a hankali ya futa, har yanzu suna zaune a inda suke sai dai sun matso cikin wata rumfar kwano dake gurin saboda sanyin asubah. Sosai suka bashi tausayi mussaman Asma'u da ya ganta tayi wujuga-wujuga da ita ga idanunta sun kode. daga nesa ya tsaya tare da fadin "Umma ni zan wuce Allah ya bata lafiya." Umma tace"Ameeen suma ameen mun Gode k'warai da kulawa." Kallona naga yayi a fakaice sai kuma ya kalli Aminu dake dauke dauken kai ya mik'a masa hannu domin suyi sallama. Da kyar Aminu ya bashi hannunsa, Amjadu ya wuce yana mamakin abunda Aminu yake yi sai kace jahili in banda dalili ya kai dalili Aminu ya Isa yaga inuwar shi ma ballanta ya hada hannu dashi, duk sanadin Asma'u ne. Sai da ya shiga motar sannan ya kira ta a waya, ina jin wayar na ringing naki dauka Munnu ta karba daga hannuna tana dubawa. Mik'a min tayi tare da fadin"Shine." Aunt Hauwa tace" Sai ki tashi kije mybe akwai abunda zai ce miki." Kallon da Umma tayi min ne yasa na mike da sauri na bi hanyar da naga ya bi.Na gane motar shi tunda duk inda suke basa b'uya bayan haka kuma gurin da haske. Kallonta yake yana daga cikin motar har ta k'araso. Ajiyar zuciya ya sauke babu wasa a tartare dashi ya bude motar tare da fadin"Shigo muyi magana dake ta fahimta." K'in shiga nayi na tsaya ina kallonshi. Shima ya kalle ni babu fara'a yace." Time d'in sallah ya kusa ki shigo muyi abunda zamuyi in tafi gida Ok."

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});