Chapter 48
Chapter 48
zai dawo." Tsaki naja a karo na biyu nace"To sai me."? Kiyi zaman ki mana." Tace"Yace ma kakar shi zata zo ts taya ni za ma." Nace"To kin huta ai amma don Allah ki daina Wannan kukan da kike yi bashi da amfani." Mimi tace"Habibty Wallahi kwana biyu bana jin dadin jikina kullum bana iya cin abunci ga jiri da tashin zuciya ina ji." Nace" kinji asibiti ko kin San dai kina da maleria." Tace." Banje wallahi, amma don Allah gobe kizo muje ki rakani." Nace" Allah ya kaimu, yanzu kakar tashi tazo ko kuwa."? "Tana kan hanya." Nace "Shikkenan Allah ya sawake don Allah ki kwantar da hankalin ki." To tace mun na kashe wayar. Munnu ta kalle ni tare da fadin "Bata da Lafiya ne." Nace"Wai zazzab'i take ji da jiri. " Munnu tasa dariya tare da fadin"Shikkenan Mimi ta hau network sai fatan sauka Lafiya. " Take naji wani muguwar fad'uwar gaba, na kalli Munnu cikin mamaki nace"Ciki."? Munnu na dariya tace"Eh mana wallahi ko kaffara bazan yi ba Mimi ciki gare ta, kinsan ranar d'aurin auran ta tayi wank ma tsarki kin manta har su Maryam suka dinga tsokanar ta, tana shiga zatayi gamo aikuwa gashinan. " Rasa miyau nayi a bakina ya bushe Kama's gashi babu wani tes ko na kwabo jikina yayi sanyi sosai Wahidun k'ahar Allah mai barwa da hanawa.......... *19/11/2019* [11/20, 10:07 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *57* Munnu ce kawai take surutun ta i ta kad'ai ni kam ina can duniyar tunani lamarin ubangiji wai Mimi har tayi ciki zata haihu, Allah babu yanda baya tsara almarin shi. Yanzu Sai dai kawai mu taya ta addu'ar sauka Lafiya, yau sama-sama nake a makarantar, domin na kasa sakewa da abun ya fado min zan ji fad'uwar gaba, ya zama Dole na cire son shi a cikin zuciya tunda yanzu nasan yayi min nisa na har a bada. ****** Ina koma wa gida Umma take min zancan Miki ta kirata a waya wai bata da lafiya bayan haka kuma Mijinta yayi tafiya tace kije ki taya zama." A tausashe nace"Umma nima munyi waya da ita d'azu ta fad'a min, amma ni dai bata ce min naje in taya ta zama ba, tace kakarshi zata zo ta taya ta zama. Amma dai munyi maganar zan rakata hospital taga dactor. " Umma tace"To tunda kakar shi zata zo sai kiyi zaman ki, ai na dauka ita kadai zata zauna a gidan." Girgiza kaina nayi. Mik'ewa nayi na shiga kicin domin wata irin yunwa nake ji. Washe gari da wuri na shirya Dan ma Allah yasa bamu da lecture a ranan da ko sai dai Mimi ta hak'ura Umma nayi wa sallama na tafi tana fadin 'ki gaishe min ita da jiki. Umma ba yarinya bace ta fahimci Mimi ta samu ciki. Sosai take murna da farin ciki. A dai-dai ta sahu na samu har gidan Mimi na biya shi kudinsa sannan na tsallaka Titi na Isa jikin gate din inda nake hango masu gadi a zaune, fuskata ba b'oyayya bace a gurin su, nan d'aya daga ciki ya tawo da sauri ya bude min na shiga ciki ba tare da na kalle shi ba na wuce part din Mimi cikin nutsuwa. Suna zaune ita da granny a parlor suna hira nayi sallama na shiga, Mimi ta amsa tare,da mik'ewa da sauri ta tare ni, kallon fuskar ta nayi sosai naga ta rame amma tayi haske sosai. Zama nayi kan kujera ina gaida Granny ta amsa fuskarta a sake, take fadin"ai gwara kuje likita ya dubata tun d'azu take amai gashi bata ci komai ba Mimi na kalla dake ya mutse fuska nace"Ina gani ba sai munje asibiti ko in kira Mujahid ya duba ki, ko ya kika gani." Shuru tayi daga bisani tace"Bari in yi masa waya jiya na fad'a masa zamu je asibiti dake yace." Babu matsala amma yanzu nasan babu abunda zai ce tunda yasan Mujahid din. " Shiru nayi ina kallonta na dauki wayarta tana kiran sa, ina ji sai da tayi ringing sai biyu ana ukun ya d'aga muryar da da alamun bacci da gajiya naji yana fad'in"My wife kin tashi Lafiya ."? Mimi tace." Lafiya Lou Alhmdullahi nayi ta kiran wayar ka, tun d'azu baka dauka ba." A hankali yace." Bacci nake Momy nayi aiki na gaji." Mimi tace." Dama Asma'u ce tace ko Dector Mujahid za muyi wa magana tunda likita ne ba sai munje asibiti ba." Tunda Mimi ta fara magana naji kamar in tashi in fuzge wayar daga hannunta in kwad'a mata mari, Mimi wata irin sukuwa ce da bata da wayo. Nashi b'angaran kuwa Mik'ewa yayi zumbur ya wani hade fuskar sa tam! Yace." Bani Asma'u muyi magana da ita." Wayar ta mik'o mun da sauri na bi hannunta da kallo, Idanun kakar shi ya sanya na karb'i wayar raina a b'ace.! A hasale yace." Ke kar ki kuskura ki gayyato min wani gardi cikin gidana, wai da sunan yazo duba wife dina, saboda rashin hankali irin naki. Wallahi sai na b'ata miki rai, mutukar kika shigo min da saurayin ki gida, ki kaita Asibiti a duba ta ko nawa ne a kashe amma ban yarda da wannan iskan cin ba."!! Shuru nayi INA saura shi yanda yake wani magana a zafafe nace k'ila da yana kusa duka na zai yi. "Kinji ko baki ji ba."! Yafad'a cikin tsawa! Raina ya b'aci sosai amma ganin granny dake zaune idanunta a kaina yasa nace " Naji." Tsaki yaja ya kashe wayar sa. Mimi ta karb'i wayar jikinta a salube domin da ita da granny din duk sunji irin tsawar da yake buga min. Granny tace"Rabu dashi don Allah kinji Ina ce shi Mujahid din abokinsa ne kuma makocin sa, ne don zai taimaki iyalinsa sai ya hana kan wane dalili."? Tace 'kira shi a wayar yazo ya duba ta Allah yasa bai futa aiki ba." Nace"A'a tunda yace kar ayi to a barshi granny kibar maganar Mimi ta tashi kawai muje a sibiti kamar yanda ya fad'a." K'wafa tayi tace"Sai kuje Allah ya tsare nasan dai ta tsuniyar gizo bata wuce koki Allah ya raba Lafiya sai kun dawo." Ta fadi maganar tana gyara zaman ta cikin kujera. Abun mamaki muna futa sai ga motar Mujahid ya futo, tsaf cikin shirin futa aiki. Da sauri ya tsayar da motar kusa damu, fuskarsa a sake ya leko da kansa yana yi min wani irin kallo na so yace." Me yasa baki fada min zaki zo ba."? Murmushi nayi kurrum, dauke kansa yayi ya kalli Mimi tare da fad'in"Madam yane da'alama babu Lafiya domin ga alamu nan na gani." Nace"Aikuwa asibiti zamu je." Murmushi yayi yace." Shine baki Sanar da ni, ba, Ku shigo muje." Nace"A'a kaje kurrum." Fuskarsa ya b'ata yana kallona yace." Bana son gaddama Asma'u don Allah Ku shigo mu tafi." Mimi da tsayuwa gurin ta gagare ta saboda jiri ta bude motar da sauri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78