Chapter 28
Chapter 28
mutu da wannan rayuwar." Hankalina ya kai k'oluluwar tashi jin abunda Mimi take fad'a ban tsaya naji Abunda Ummansu Munnu take cewa ba na futa daga d'akin. ba tare da sun ganni ba. Diri-diri nake harabar a sibitin kamar wata sabuwar mahaukaciya nayi waje da sauri na, bakin titi na tsya na tari a dai-dai ta sahu, na fad'a mishi idan zai kaini. Har kofar gidan Kawu Yunusa ya aje ni, nace"Bari in shiga ciki in karb'o maka kudinka." Kallo kawai d'an a dai-dai ta ya bita dashi. Ina shiga soron gidan naci karo da Musa zai futa yaci kwalliya cikin shaddar sa, gaishe shi nayi ya amsa yana was he min baki, tare da fadin "Husna kece a gidan nan da Safiya." ? Nace"E h Musa ga mai s dai-dai ta can bashi kudinsa don Allah." Da sauri ya futa ni kuma na shige gidan. Muka gaisa da Baba Mariya a muntunce sai tsokana ta take da amarya amarya ni dai nayi mata shiru, tace"Na ganki duk a furgice ." nace"Kawu yanan ko."? D'aga kanta tayi tare da fadin yana sama tare da d'aya Kawun naki Idiris nasan maganar auran ki suke yi." Mik'ewa nayi ina fadin"Yawwa dama gurinsu Nazo." Babu yabo babu fallasa nayi sallama dakin Kawun namu Wanda ya zame mana waliyi, daga ciki naji muryar shi yana fad'in "Shigo ko waye." Na shiga cikin mamaki suka Bini da kallo shi da Kawu Idiris na zauna muna gaisawa . Kawu Idiris yace." Daga ina kike da sassafe nan." ? Nace"Daga asibiti. " Kawu Yunusa yace."Waye babu lafiya."? Kuka na fashe musu dashi nace"Mimi ce ." Kawu Idiris yace."Mai ya same ta kiyi shiru kiyi mana bayani yanda zamu gamsu." Cikin kuka nace"Aman jini take sosai da kyar likitoci suka shawo kan Matsalar kuma sun ce lallai a bata abunda take so idan ba haka ba zuciyar ta zata buga da ko wane lokaci." Kawu Yunusa yace." To mu wannan ai bs hurumin mu bane zaki zo ki tayar mana da hankali da sanyi safiyar nan." Kawu Yunusa yace." Nima abunda na gani kenan kije ki Sanar da kanin mahaifin ta shine magana." Kallonsu nake cike da mamaki dama halinsu ne rashin zumunci da rashin taimako Sam 'yan uwan Babanmu basu da kara basu da kawaici kowa kansa ya sani da iyalinsa, mun sha wahala sosai bayan mutuwar mahaifinmu shiyasa nake jinjinawa aunt Hauwa ta ko wane fanni domin ta taka muhimmiyar rawa a gare mu, kafin Umma ta tsaya da k'afafunta. Nace." Kawu Wallahi nayi rantsuwa da Allah mutukar baku sanya Ya Aminu ya janye maganar auransa da Mimi ba to nima dole Ku warware nawa Ku mai da wa da Amjadu kudinsa, na aure da kuka karb'a, Mimi ba son Aminu Amjadu take so saboda haka yace. Zai auremu ni da ita Ya Aminu dole ya hak'ura tunda shi namiji ne idan yak'i hak'ura kuma to nima bazan aure shi ba." Jikinsu ne yayi sanyi jin abunda yarinyar take cewa, Suna murna arziki ya shigo musu gida ai ba za su Bari wannan dama ta kubce musu ba shiyasa suka yi ruwa suka yi tsaki kan al'amari idan banda rashin hankalin Asmau da kanta ta zo nema wa kanta kishiya. Babu ruwan su su dai burinsu suga tabbatuwar auran ta da Amjadu ko banza zai kira su Waliyyanta Kuma zai dunga tunawa dasu, duk abunda zai biyo baya babu ruwan su." Kawu Yunusa yace." Wannan ce matsalar taki."? Gyada kaina nayi ina share hawaye na, Yace." Kar ki damu zan samu Aminu in rarrashi shi tunda kinji kin gani shikkenan Allah ya sanya alkairi." Ameen nace na mike hade da yi musu sallama. Tana futa suka cigaba da maganar cike da mamaki sukan ba damuwar su bace hakan burinsu tabbatuwar auran kawai. Ko da na koma asubitin tashin hankali na tarar domin Ya Aminu ya dawo ya tadda Surutun da Mimi take yi tamkar me motsuwar kwakwalwa take sambatu tare da fad'in sunan Amjadu , fad'uwa yayi a gurin hankalinsa a tashe, yana dafe k'irjinsa haki! Yake sosai, likitoci suka shigo dakin suka dinga fada sosai suka yi kora waje, nan suka dauki Aminu da bai San a wace duniyar yake ba, cikin tashin hankali suka yi wani daki dashi ganin yanda yake jawo numfahi da kyar oxygen suka sanya masa. Mimi jikin ya kara rike wa likitan ta kamar ya mammari su Umma haka yake ji ya dinga fada sosai da sosai itama Oxygen din aka sanya mata Dr din yana addu'ar Allah yasa kar jinin ya dawo mutukar jinin ya dawo da zubah to babu shakka sakamakon su ya nuna masa cewar zuciyarta zata iya daina aiki. *11/November/2019* [11/12, 11:13 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *Mallakar_BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA* *49* Hankalin Umma ya kai k'oluluwar tashi inda ta dinga wata irin zufa!! Gabanta yana wata irin fad'uwa su biyu kawai iyayen su suka Haifa ita da k'anwar ta, Aisha maihaifyar Mimi kenan tabbas idan ta rasa Mimi bata da wani Abu da ya dangaci k'anwar ta, Mimi take kallo a matsayin Aisha k'anwar ta, Aminu danta ne dole zata iya sarrafa shi ya hak'ura da Mimi a bata zabin ranta, ko da kuwa Shi Aminu zai rasa tasa rayuwar wannan hukuncin ta yanke, ba tare da bata lokaci ba ta sanya aunt Hauwa ta kira mata Kawu a waya yace gasu nan zuwa asibitin. Sunzo sun tadda badakalar da take faruwa Umma tace Ita ta Riga ta gama yanke hukunci Aminu ya janye auran sa a kan Mimi dole a aura mata Wanda take so. Kawu Yunusa yace." Muma maganar da take tafe damu kenan domin Asma'u taje har gida ta Sanar mana saboda haka tunda taga zata iya shikkenan dama kuma shi yaron Neman auran mutum biyu yazo ita da Mimi saboda haka kan Aminu baza mu bari a rusa wannan auran ba domin mu abun alfarin mu ne, hada jini da Amjadu saboda haka zamu tattashi Aminu." Wannan shawarar ita ce matsaya Babansu Munnu na tsaye bai ce komai ba sai da suka gama magana yace."Idan babu damuwa Aminu yazo ga Munnubiya na bashi sai a d'aura auran rana daya. Kawu Idiris yace." Mungode da wannan karamci zamu jira ya dawo hayyacinsa muji ta bakinsa. 4:35 Aminu ya farka masha Allah nuffashin sa ya dawo dai-dai budar bakinsa "Ina Mimi take kar kice min ta mutu Innalillahi wa'ina ilahi raji'un." Ya fada yana yunk'urin tashi zaune Dr Yayi saurin mai dashi ya kwantar yana rarrashin sa fafur Aminu yak'i zama dole sai an kaishi gurin Mimi, Dr da kansa ya Dora shi keke saboda jikinsa babu k'wari kai tsaye dakin da Mimi take ya nufa da shi. Mimi na kwance sambal hancin ta sakale da oxygen idanunta a rufe Aminu ya tsura mata ido zuciyarsa nayi masa zafi wai yanzu shi Mimi take gudu tafi son bare dashi, hak'ika Allah ya jarrabe shi da kaunar ta tun tana 'yar jaririyar ta, Ashe zan Ga wannan ranar ta bakin ciki, wasu zafafan hawaye ya share cikin zuciyar sa yace ."Ya zama Dole in hak'ura dake Mimi domin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78