Chapter 5
Chapter 5
bai gama zubar da sperm din nasa gaba ga daya ba, tun da suka had'u da yarinyar sha'awa take taso masa akai-akai yanzu haka mamar shi daure wa kawai take, Hibbah tayi masa wasa sosai yanda zai gamsu amma ji yake idan ba sex yayi ba zai samu nutsuwa ba, baya bukatar kowa a lokacin sai Yarinyar ko meye dalili oho. Shine abunda yasa ya tsallake Hibbah ba tare da ya biya mata bukatar ta ba saboda baya cikin nutsuwar sa. Stytem d'insa ce a kan cinyar sa, suna magana da Anthony, sai wajan k'arfe daya da rabi ya kwanta. ******** Da shiri zuwa karb'o din kunan mu muka tashi, amma sai mun fara zuwa gurin saloon tukkuna, ni da Mimi sama-sama muke yi domin har yanzu tak'i sakin jikinta nice ma mai k'okarin yi mata magana, tana amsawa babu yabo babu fallasa. Ina zaune gefan katifar mu ina shafa mai Mimi na band'aki tana Wanka naji kakar wayar ta. Kallon wayar nayi ba tare da na dauka ba, abunda na gani an rubuta ya bani mamaki *My heart beat* da sauri na dauki wayar ina dubawa, gabana na fad'uwa numbar nake bi kamar ina karantawa kamar wata shashasha, tabbas shine, maganar ta sub'e min daga bakina, katsewa wayar tayi ko minti guda bai ba ya k'ara kira. Naji kamar in dauka wata zuciyar tace min kar ki dauka babu ruwan ki. Ji nayi bazan iya hak'ura ba dannawa nayi tare da aje wayar kan katifa bayan na bude muryar. Muryar shi naji mai cike da amo gami da sauti yayi sallama. Gabana ya tsananta fad'uwa *"Hello momyna kina juna"* naji ya fada murya a lankwashe.. Kamar in kashe wayar sai dai na fasa, Wannan murmushin nasa naji Yayi yace." Ku kuna tare da 'yar Uwar ki tayi miki kwarjini kin sa yin magana, domin na lura tsoron ta kike ji." Shiru babu amsa, yace." Ok Momy hope kin tashi lafiya domin itace babbar abun tambaya a gare ni. Yawwa bayan haka kuma INA son in fad'a miki zan je Chana yau insha Allah kiyi wa d'anki addu'a." Cikin taushin harshe yake maganar. " k'it!! Naji wayar ta tsinke, kura mata ido kawai nayi ina kallo Tare da tunanin maganganun da ya fada, Mimi lafiyar ta abun tambaya ce a gare shi, wato ya manta dani tunda ya gama latse ni ya San wacece ni, yanzu kuma Mimi yake so ya yaudara, Sam! Yanzu na dawo daga rakiyar guy nan. Man shafawar na jefar kasa kwanciya nayi kan katifar wani irin Abu yazo ya tsaya min a mak'ogwaro na, lokaci guda Naji ruwan hawaye ya cika idona, k'okarin mai dasu nake inaaa!! Sai da suka zubo, hannu NASA na goge su da sauri domin kar ta shigo ta gani tunani nake yays za'ayi na hana Mimi kula shi, domin na lura tayi mugun nisa a gurin son shi. Mimi ta shigo da sauri tana fad'in"Asma'u goma da rabi tayi kin ga har rana ta sauko k'asa.'' Nace" ni ai na gama ke nake jira." Kayan ta ta dauko tana sanyawa cikin sauri. Ni kuma na mik'e na futa daga d'akin. Sai da mukaje saloon sannan muka karb'o d'in kunanmu sunyi bala'in kyau sosai sun matse ni dama haka nake so ko ina ya futo zam!zam! Dake Allah yayi min yalwar gashin kai bakikirin dashi, sai ya kara mik'ewa sosai da a ka gyara shi, abunda be dame ni ba kenan kwalliya da gashi amma gobe dole in tsula tsiyata son raina Gidan aunt Hauwa muka wuce, muka tarar tayi bakuwa kawarta ce aunt Zainab tun ta k'uruciya nan muka zauna muna kallo muna hira aunt na soyo mana wainar fulawa wacce taji kwai da yaji me dad'i aikuwa na samu abunda nake so tuni na zage ina ci. NTA HAUSA muna tsaka da kallon wani najeria film kawai suka katse tare da nuno *Amjadu* a filin jirgi lokacin yana k'okarin hawa matattakalar jirgi ya tsaya yana magana da wani d'an jarida, tsakanin ni da Mimi ban San Wanda yafi shiga d'imuwa ba, lokaci guda naji wainar da nake fi ta fuce min daga rai duk dadin ta kuwa. Yana sanye da wasu uban suit blue and white hade da necktie d'insa hannunsa daure da wani irin agogo na zallahr fata sai blue sai shek'i yake, k'afar sa sanye da takalmi rufaffafe black sai shaining yake, hannunsa rike da irin jakar nan ta matafiya. Dan jarida bayan sun gama magana dashi sai ya juyo yana fuskantar TV din yace." *To masu kallon ga dai Amjadu AbulAbbas Wanda kuka fi sani daYoung millionaire, zai tafi k'asashe biyu domin gudanar da harkokinsa na yau da kullum domin kawo wa k'asar shi cigaba muna yi masa fatan dawo wa k'asar shi lafiya tare da nasarori, duk wani me kaunar sa, sai ya raka shi da addu'a Allah ya bashi sa'a a dukanin abunda ya sanya a gaba.* Yana gama maganar tashi A ka d'auke shi, film din ya cigaba, aunt da kawarta suka dinga yi masa addu'a gami da fatan alkairi, Ni da Mimi kuwa babu Wanda yace." Uffan! Har yanzu ko wacce ita tasan halin da take ciki. Aunt naji tana fadawa kawar ta abunda ya faru kwanakin baya, Zainab tace"Ko sonta yake ne."? Aunt tace " Nima nayi tunanin haka wallahi amma sai naga kwata-kwata bai nuna alama ba, Zainab tace"ke akwai dai abunda yake faruwa wallahi tunda nake ban tab'a jin ance ya dauki budurwa ya kai ta tayi shopping ba sai akan Asma'u ina ganin son ta yake." Da sauri na kalli aunt Zainab nace"Bani yake so Aunt." Duk suka kalleni nace"Wallahi kuwa Mimi yake so." Mimi tayi saurin sunkuyar da kanta cike da kunya, Aunt hauwa ta jawo ta jikinta tana dariya tare da fad'in"Kai Alhmdullahi kice wahalar mu ta kusa karewa dama nasan Mimi na ta shiga tsara ce babu namijin da bazai so ta ba farar mace alkyabar mata.. Wai!!!! Kice wata shekarar damu za'ayi aikin hajji.'"" Aunt Zainab dariya kawai take wa kawar tata ni kaina duk da halin da nake ciki sai da na dara ganin yanda aunt Hauwa duk ta gigice! Aunt Hauwa ba dai son kudi ba. Nace"Aunt kinga ma wayar da ya bata." K'okarin dauko ta nake Mimi tana kwace jakar sai da na Ciro na mik'awa aunt ta karb'a tana dubawa hade da rik'e baki take fad'in"Mimi wannan wayar si tafi dubu Dari."" Lallai Juma'ar da zata yi kyau tunda ga laraba ake gane ta." Aunt Zainab ta karb'i wayar tana dubawa itama jinjina kai tayi tare da fadin" har wani kamshi wayar take lallai abun na manya ne, Mimi Allah ya dubi maraicin ki, idan kika shiga gidan nan kar ki manta damu don Allah." Cike da mamaki nake kallon su, ina mamakin son kud'in su lallai a duniya idan kayi kudi ka wuce komai Mimi tun kafin ta shiga gidan sun fara magiya.. Kallonsu kawai nake suna zolayar Mimi ita kuma tana wani sinne kai, cikin zuciyata nace "Kin had'u da aiki babba Mimi. ********* K'arfe goma da kwata mun fito cikin shiri kamar wasu taurari Munnu nan tazo mu tafi tare, munyi bala'in kyau mussaman ma ni suffa da b'oyayyan kyau na yau sun futo a zahiri saboda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78