Chapter 50
Chapter 50
cika mutum mai kyawun hali da tausayi tabbas duk macan da ta aure shi tayi dace da miji na saki jikina sosai dashi, domin shine yake kaini makaranta cikin motar shi kullum, siyayya kuwa babu irin wacce baya min, har yaron shi sai da ya kawo min ya yini a gurini Grnay tayi ta tsokanar sa, sai dai yayi dariya kawai. Ina dawo wa daga makaranta granny take fada min yau Mai gidan zai dawo domin yayi waya bayan futa ta yace." Yana jirgi, shikkenan na nemi nutsuwata na rasa domin Sam bana kaunar abunda zai sake hada ni dashi, tunanin hada kaya na nafara yi domun ina gudun cin mutumcin da zai yi min a gidan shi.... *20/11/2019* [11/21, 10:38 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *58* Mimi na sanya tayi wanka ta gyara jikinta tsaf! Nima nayi wanka ban yi wata kwalliya ba, na sanya atamfar mu ta anko Candy mu, ina kokarin zama kusa da ita tace." Asma'u ya kamata a shirya masa abunci ko."? Kallonta nayi na minti biyu kana nace"Kina da tabbacin zai ci abincin idan ka shirya masa nifa bana son wulakanci domin yanzu ma na had'a kayana tsaf! Zan tafi inda nafi wayo." Marairaice fuska tayi tace"Don Allah kar ki tafi yau kinji ki bari na warware tukkuna." Tsaki naja tare da fad'in "Kinsan inuwarmu bata had'uwa guri guda dashi, bana son abun bata rai." Tace" Ki rabu dashi don Allah duk abunda zai miki." Shiru nayi kawai, Granny ta futo daga d'akinta da carbi a hannunta ta idar da sallahr la'asar, ta kalli Mimi sai ta saki dariya tana zama kan kujera tace." Wato da kika ji Mijin ki na kan hanya kinyi wanka tsaf har da kwalliyar fuska." Dariya nayi kadan nace"Dole tayi kar taje ki kwace mata gakinan kin rambad'a kwalli har da sabuwar atamfa." Granny tace"Sai kiyi kuma komai abunki bazan baki kwallina ba." Dariya nayi nace"Ni ba kwalli nake so ba ki bani lallai me ja irin na k'afafunki." Kallon k'afar tata tayi tace." Yana gidana nima Iyami ce ta kawo min daga garinsu, duk sanda zata zo gidanan zan ce ta Zo miki dashi." Nace"Yawwa granny ko yanzu ma a kira ta a waya ai tana da waya ko?"? Granny tace"Tana da waya to wai ke meye kika damu da kunshi sai kace wata me miji, ki bari mu masu miji muyi." Dariya ta bani sosai nake yi nace"Ni ko nake da miji a hannu kin San shi don kullum yana zuwa gaishe k.............Kafin in karasa ya shigo parlor tuni k'amshin turaran sa, ya mamaye parlor. Yana sanya da Riga shart fara tas tana da gaje ran hannu, wando jikinsa jins ne blue ya sanya fencing cap (hana sallah) idanunsa sake da bakin glass wuyan shi wata siririyar sark'e ce silver sai shek'i take, hakama a gogon hannun Shi, shi kanshi blet din da yayi amfani dashi abun kallo ne kafin kazo kan takalmin k'afar shi, booth mai igiyoyi blue colour in da kasan bature haka ya koma. Duk zancan da Asma'u suke da granny a kunne shi. Fuskarsa murtuk! Ya tsaya bakin kofa, yana karb'ar wayoyin shi daga hannun Rambo Granny ta washe baki tana fad'in"Oyoyo angon karni ya dawo sannu da zuwa angon Aishatu sannu da zuwa."! Mik'ewa tayi karasa bakin kofar sai washe baki take, fuskarsa ya saki kad'an ganin kakar tashi ya rungomta jikinsa hade da sumbatar goshin ta yana fadin"Granny na same Ku lafiya."? A sake tace." Lafiya ba lafiya gaskiya amma shige ka huta tukkuna." Hannunta ya rik'o suka k'araso parlor, ina kallon Mimi ta yunk'ura ta mike tsaye ta nufi inda suke, sakin Granny yayi ya kamo ta ya rungume ta hadda lumshe ido! Kauda kaina nayi da sauri ina da na sanin zama na a gurin. Fuskar ta ya d'ago da hannunshi yace." Momyna haka kika koma."!? Mimi ta fara k'walla, saurin rungume ta yayi yana Dan dukan bayan ta kad'an cikin sigar rarrashi yace." Sorry baby na ya taso ki a gaba kiyi hakuri insa Allahu zaki warware." Kungunta ya riko har suka k'araso tsakiyar parlor. Ya kalleni a d'age. Nima na kalle shi babu yabo babu fallasa. Wuce wa yake kokarin yi, granny tace "Zaka wuce baku gaisa da Asma'u ba, yarinya hazika kuma jajurtacciya ta tsaya kan matarka sosai, gaskiya samun me zumuncin ta sai an tona." Babu yabo babu fallasa tace." Granny na ganta ai ni da ita waye zai fara gaida wani ko banza na girme ta nesa ba kusa ba, bayan haka kuma a gidana take dole ta girmama ni." Tsaki granny Taja tana fadin"kai dad'i na da kai kenan,son girma kowa ai da irin tashi fahimtar ko kaga ka wuce bata gaishe ka ba." Fuskata na saki don kar in kunya ta granny nace"Sannu da zuwa ka dawo Lafiya. "? A fakaice ya kalle ta, yayi saurin dauke kansa, jin muryar ta ya tayar masa da abubuwa da dama, yana tafiya yace." Lafiya k'alau na dawo." Bedroom d'insa ya shige da Mimi rungume a jikin sa. Wanka ya shiga ya futo Mimi na kwance kan bed ya kalleta cike da tausayi ya dawo da matsananciyar sha'awa babu hali domin akwai rashin imani ya kusanci Mimi duba da halin da take ciki. Sabbin kaya ya sanya ya shirya tsaf dashi kana ya zauna kusa da ita. Mik'ewa tayi zaune cikin kasala, shi kuma ya tsira mata idonsa. A hankali yace." Momy kin rame sosai laulayi ya sanya ki a gaba ko." ? Mimi tace." In laulayi ne kadai da sauk'i kullum da daddare fa bana iya bacci ciwon ciki, Dr Mujahid ne a tsaye a kaina sai Asma'u, domun ta dalilinsa take zaune a gidanan tunda shi ya tursasa ta, yana da kirki wallahi, kusan kullum sai ya shigo ya duba ni." Fuskarsa ya kirne! Kamar bai tab'a Dariya ba yace." Kina so kice min kun karya mun doka ke da Asma'u, bana nan kuna shigo mun da k'ato cikin gida. "!? Mimi ta tsorata ganin yanda yake zare mata idonsa. Tsawa ya buga mata tare da fadin" Kinyi shuru ki bani amsa ta." Gyada kanta tayi tace." Tun ranar ya ganmu zamu hospital shine ya dauke mu a mota can asibitin su ya akaimu shine ya sanya akai min duk wasu gwaje-gwaje." Mik'ewa yayi tsaye da sauri ya nuna ta da hannu Cikin daga murya yace." Da kika kirani a waya me na fada miki."? Mimi tayi shiru gabanta sai fad'uwa yake yi. Ni da granny duk muna jiyo hayaniyar shi, yace." Ko ba cewa nayi dake kar Ki sake ki bi ra'ayin wancan yarinyar ba, wato ni ban Isa dake ba kenan , in banda lalacewa da kudina da komai Ku shigo mun da wani banza cikin gidana bayan bananan, me hakan yake nufi."!!? Mimi har ta fara kuka tana bashi hakuri Cikin banbami masifa ya cigaba da cewa" Nace dake akwai kudi a dakina ku yi amfani da ko nawa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78