Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,226 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gurin da yake kafin ya mike ya shiga gida jikinsa a mutukar sanyaye, ya samu Umma na d'aurin sikari a rumfa zama yayi kusa da ita tare da fadin "Umma kinji gagarimun abunda mutumin nan ya dauko mana kuwa." Umma tace"Wane mutumin ? "Amjadu" Aminu ya fada jikinsa babu k'wari, tace "A ina kangan shi kai." "Yanzu muka gama waya dashi, Wai yana son ya auri Asma'u da Mimi lokaci guda." Umma ta saki ledar da take hannunta tana kallon Aminu cike da mamaki tace"Wannan wace irin magana CE."? Yace." Wallahi haka yace" Shiru tayi tana nazarin maganar daga bisani tace"Mimi da Asma'u Anya hadin yayi kuwa gaskiya Indai Yana so sai da ya zab'i d'aya a cikinsu." Aminu yace"Umma mutum me girma kamar wannan ko mata hudu yace." Zai aura a lokaci guda za'iya ya tsallake gidaje sama da miliyan yazo nan bamu aje ba bamu bawa wani ajiya ba, gaskiya ni bazan iya fada masa haka ba." Umma tace "Zaman kishi tsakanin Asma'u da Mimi akwai kwara Mimi sanyi hali Asma'u wayo da rashin kunya gata itace k'arama bana son abunda zai tab'a zumumcin su." Aminu yace." Sai dai idan sune suka so haka amma in sun hade Kansu babu wata matsala. Umma tace" Shikkenan zanyi magana dasu." Ya Aminu ya mike ya futa jikinsa babu kuzari. Mimi na daki a kwance ni kuma ina bakin rijiya ina wanki Umma ta kwala mana kira, aje sabulan hannuna nayi na amsa hade da cewa "Gani nan zuwa Umma. Ina zama Mimi ta shigo salo-salo Umma tace." Kun San abunda yake faruwa kuwa."? Girgiza kaina nayi, tace" A cikin Ku Wa ya tab'a furtawa Kalmar so." Nace"Umma waye." ? Hararata tayi tace"Wanda kuka sani mana." Kaina sai ya daure kawai domin ban fuskanci abunda take nufi ba." Tace"Ke ya baki KUDI hade da yi miki shopping ke kuma ya baki waya, shine nake tambayar wacece a cikin Ku ya taba cewa wance ina son ki,saboda yau ya bujoro mana da bukatar son ya aure Ku duk Ku biyun." Das!das! Haka gababa ya dinga fad'uwa, baki na rawa nace"Umma ban...ban fahimce ki ba." Mimi ta kalla tare da fadin"Ke dai nasan kin fahimce ni ko."? Mimi ta gyad'a kanta tare da fadin"Na fahimce ki Umma a gaskiya ni dai Kalmar so bata tab'a hadani dashi ba sai da ko ita Asma'u. " harara na banka mata nace"Ki fad'i gaskiya dai ko kinyi maganar aure dashi amma ni meye shafe ni da har zai ce zai aure mu ni dake, babu wata kyakyawar alaka mybe ma duk abunda yayi min saboda kene, Umma ni kam babu abunda ya shiga tsakanina dashi Mimi yake so." Na fada raina a bace. " Umma tace"Yanzu dai ya turo Aminu da sako saboda haka sai kuje Ku sasanta kanku." [11/5, 7:40 AM] .: Tab'e bakina nayi na mike hade da barin gurin. Wankina na cigaba da yi ina tunanin al'amarin lallai ma, wai yana so ya aure mu ni da Mimi kiji sai kace Wanda aka ce masa mun rasa majin aure aiko sama da kasa zata hade bazan aure shi ba, Mimi taje ta aure shi, ni gani nake ma kamar da wata manufa ya shirya hakan Ina kallon Mimi ta futo salo-salo ta shiga dakinmu kallo na bita dashi ina tab'e bakina nace"Kin had'u da aiki babba a rayuwar ki, Ya Aminu ne naga ya shigo cikin gidan da sauri hannunshi rike da wayar Mimi ya nufi dakinmu, babu wayar ya futo, da alama shi yake kiranta. Zuciyata naji babu dad'i naji ina son inji wace hira suke dashi, daurewa kawai nayi na cigaba da wankina, ina jiyo muryar Mimi k'asa-kasa tana magana...... Kwafa! Kawai nayi cikin zuciyata nace"wannan guy shigowar shi cikin al'amari mu ba k'aramin hatsari bane domin zai iya wargatsa mana zumuncin mu." Sai da na gama tsaf! Sannan na shiga dakinmu ina k'okarin cire kayan jikina Mimi ta kalleni baki na rawa tace." Asma'u kin San meye."? Kai tsaye nace"sai kin fada." A hankali tace"Wai Amjadu ne zai zo bayan sallahr Isha'i zai kawo mana tsarabar mu." Ba tare da na kalleta ba nace"zai kawo miki tsaraba dai." Har da ke ai." Girgiza kai nayi nace" ni kam bana son komai nashi, ban sani ba ko sai kunyi aure sannan zan daina jin haushin sa." Tace"Waye ya fada miki zan aure shi." Cike da mamaki nake kallonta na kasa cewa komai ma, na cigaba da saka kayansma tace" bazan Iya hada miji dake ba Asma'u, gwara in hak'ura in bar miki shi." Muryar ta na rawa ta k'arashe maganar. Sai ta bani tausayi mutuka nace"Mimi zaki iya hakuri da ruhin ki Ashe? Zuciyar ki tana mutukar kaunar mutumin nan, idan kikayi haka to zaki jefa kanki a halaka, wallahi in har don ni zakiyi haka, to bari kiji wallahi zan iya sadauakar miki da komai na rayuwata domin ki samu farin ciki, ballanta d'a namiji ki kwantar da hankalin ki, ni ba bakuwar zafi bace, Sam Amjadu baya gabana, a yanzu na bar miki shi zan cigaba da yi miki fatan alkairi har karshen rayuwar ki." Kuka tq fashe dashi hade da rungume ni sosai take kuka nima sai na tsinci kaina da share hawaye tace"Asma'u kin San Allah sai dai in mutu da sonshi mutukar kika ce baza ki aure shi nima na hak'ura gwara soyayyar shi ta zama ajalina." Yanda take fad'ar maganar tana shashshekar kuka hade da wani irin Abu yasa hankalina yayi mugun tashi Mimi kuka take wiwi tana dukan k'irjinta hade da fadin"Me yasa zuciyata zakiyi min haka.? Meyasa kullum kike azabtar dani akan son mutumin nan, Asmau da nasan inda zanje in jefar da zuciya ta da najefar na huta da masifa" tana wani irin kuka ta k'arashe maganar. Hankali a tashe nace"Mimi meye haka? Mai yayi zafi? Kina so ki kashe kanki ne? Kike dukan kirjinki." Cikin kuka tace" Asma'u gwara in mutu akan i n rayu a duniyar nan, kwata-kwata zuciyata ba tayi min adalci ba, Asma'u na san ke Amjadu yake so amma saboda sharrin zuciya kullum sai take fada min karya ne, ni yake so, kinga kuwa wannan zuciyar bata da amfani a gare ni, Tunda tana kokarin sanya min abunda bazan samu ba." Cike da tausayin ta nace" Mimi yaya zaki ce baza ki samu ba, kinga na farko dai mutumin nan ya fad'i kirkin ki da kyawun halin ki kyawun zuciyar ki, ko wannan ma amsa ce ta ki gane cewar yana sonki, ki saka a ranki baki da Miji sai Amjadu insha Allahu zan iya bakin kokarina gurin ganin tabbatuwar auran Ku." Hawaye ne kawai yake zubo mata na sanya gefan zanina INA share mata, da kyar na samu tayi shiru dadin da naji ma Umma ba taji ba yara sun cika gidan suna siyyaya. ********* K'arfe shida dai-dai ya futo cikin kyakyawan shiri yau, shigar manyan kaya yayi wata lafiyayyir galila ce a jikinshi skyblue dinkin babbar Riga da 'yar ciki taji lafiyayyan sirfani na masu hannu da shuni yau mutumin Ku ya sanya hula inda ta kara futo masa da ainihin kyawun sa hade da kwarjinsa, hannunsa daure da agogo shi mai tsada sai zabbuna na azirfa guda uku a ya tsunsa masu wani irin

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});