Chapter 65
Chapter 65
yana dubawa yaga Jahid ne, murmushi yayi hade da daga wayar sallama yayi Jahid yace." Kana gida ne." ? "Eh ina Gida yanzu amma k'arfe biyar dai-dai zanje government house." Jahid yace." OK ganinan zuwa nima ina Gida kasan yau Sunday muna Hutu. " Amjad yace." OK sai ka shigo din." Kashe wayar yayi ya cigaba da abunda yake yi. Minti goma tsakani sai ga Jahid ya shigo parlor yana zama yace." Ina baby Aysha take." Amjad ya rufe loptop tare da fad'in"Tana gurin me raino yanzu kuwa ta dauke ta suka bar gurinan granny ma yanzu ta tashi." Jahid yayi Dariya tare da fadin "Babu wasa cikin al'amarin muna so ka bamu baby Aysha fa."" ! Amjad yace." Ai gatanan ga kanan Aboki baby Aysha taku ce kai da Madam." Jahid yace." Thank you my friend, wallahi Asma'u ce tun jiya ta dame ni lallai a basu ita shine nace zanyi maka magana nasan dai baza ka hana ba." Tunda ya ambaci sunan Asma'u ranshi ya b'aci don har sai da fuskarsa ta nuna ya kalli Jahid din babu alamun wasa a tare dashi yace." Babu wannan maganar my friend babu Wanda zan iya bawa sweet heart gaskiyar magana." Jahid yace." Kuma yanzu kace ka bani ita." "Yes Ni nace na baka ita saboda nasan muna tare da Kai har abada, naji ka sanyo min zancan wata Asma'u ne, am sorry my friend Asma'u bata da haleyan K'warai Wanda zata iya tarbiyan tar da d'an wani. Bana jin Zan iya bari baby Aysha ta yini a gidansu ma balle har ta kaita ga kwana gudun ta d'auko d'abiun yarinyar." Jahid ya sha kunnu mutuka yace." Kayi dai-dai Asma'u kake ciwa fuska a gabana ko."? Dariya Amjadu ya sanya tare da fad'in"Sorry halin ta ne fa, amma da baka yimin wannan maganar ba ni babu ruwana." Jahid ya bude hannunsa dake kan kafad'un sa yace." Wato kana nufin matar da zan aura bata da tarbiya ko me."? Hannu Amjad ya d'aga cikin sigar bada hakuri fuskarsa da murmushi yace." Ban fad'i haka ba my friend......................... *26/11/2019* [11/26, 9:01 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *64* Sosai Jahid yaji babu dad'i saboda yana k'aunar Asma'u tsakani da Allah kuma sam baya kaunar yaji wani ya fad'i mummunar magana a kanta, kokarin mik'ewa yake Amjad din ya mai dashi ya zaunar, gyara fuskar shi yayi babu alamun wasa yace." Karfa kayi magana ta wata fahimta ta daban, ba wai na fad'i wannan maganar bane domin ranka ya b'aci ko kuma kaji wani fargaba a game da k'udirin ka kan yarinyar kace zaka janye auran ta. No kawai na fad'i iya abun da nasa ni a kanta, kuma kasan ko wane mutum Tara yake bai cika goma ba, amma hak'ika ka cancanci yabo da godiya a gare ni abokina babu abunda zaka nema a gurina na kasa yi maka shi, misali kace min in baka Baby Aysha zaka had'a ta da Salim ka rike min, wallahi babu abunda zai hanani in baka saboda nasan Maman Salim macace da take da nutsuwa gami da tarbiyya sai ince maka ma kusan halayen su d'aya da Mimi Allah ya jikanta, amma maganar In bawa Asma'u baby ka aje ta gefe guda a halin yanzu babu ita." Jahid ya Dan ji sanyi a ransa, amma duk da haka bai hak'ura ba saboda kwata kwata baya son b'acin ran Asma'u yace." Yanzu idan Allah ya kaddara auramu da Asma'u zaka bamu ita ko ? Tunda kana ganinta a kusa dakai sai kayi mata tarbiyar da kake so." Amjad yayi Dari hade da Sosa kansa yace." Mai zai hana kuwa zan baku wannan nasan muna kusa kuma kai ma zaka samin ido sosai." Jahid yaja tsaki tare da mik'ewa tsaye yace." Baza ka fasa ba kenan ? Ni kaga tafiya ta." Amjad ya mike tsaye shima yana dariya ya rufa masa baya. To kafin suyi sallama ma sai da suka d'an jima a tsaye sannan suka rabu, dama kuma tun Asali cikin makotan sa, sunfi shiri da Mujahid din saboda saukin kansa. **** K'arfe takwas dai-dai Mujahid ya kirani a waya cewar gashinan a waje yana jirana, a shirye nake saboda nasan da zuwan sa, cikin motarsa na same shi, Duk sanda zai zo gurina da sabbin kaya a zuciya nace Jahid ba dai gayu ba, budewa nayi na zauna sosai ya sakar min murmushi tare da fad'in "Yau kin futo da Wuri." 'Yar dariya nayi nace"A shirye nake dama ya maganar mu da kai." Fad'uwar gaba yaji amma dake namiji ne sai ya dake yace." Kya bari mu gaisa ko."? Rife fuska ta nayi da tafin hannuna ina dariya, shima dariyar yake yace." Ke kinfi baby Aysha rigima ma." Bude idona nayi har yanzu da murmushi a fuskata nace"Wallahi na damu na ga babyn ne." Yace." Kina da gaskiya amma kin san me."? Girgiza kaina nayi, yace." Babanta ya hana wallahi yace ki Bari tukkuna muyi aure zai bamu ita." Raina a bace nake kallon Jahid din nace"Ban gane ya hana ba."? A hankali yace."Shima baya so tayi nisa dashi a yanda na fahimta yana kallonta baby ne yaji sanyi a ransa duk lokacin da ya tuna matarsa. Nace." Jahid abun da bangane ba shine, shi kad'ai ne yake da hakki da yarinyar? Mu da muke a matsayin iyayen ta bamu da amfani kenan Jahid gani ba ci ba, dama baby 'yar shi waye yace ba tashi ba."! A zafafe na k'arashe maganar. Jahid ya gyad'a kansa ya San zai fuskanci haka daga gurin ta, yace." Matsala ta dake saurin d'aukar zafi kiyi wa magana ta kyakyawar fahimta mana." Cikin takaici da jin haushin sa nace"Na lura kamar bakin Ku d'aya Jahid baka San yanda nake ji ba Wallahi tallahi tunda naji kuna fadin baby suna kama da Mimi naji ina mugun kaunar ta." Cikin rawar murya ta karasa maganar, cike da tausayin ta yace." Kiyi hakuri dai yanzu dai kar kiyi min kuka Jahid UA fad'a cikin rarrashi. Nace"Wallahi na saki jiki zangan ka da tare da ita." Cikin shagwaba take maganar,Jahid yaji kamar zai suma a gurin hannunsa na rawa yace." Bari kiga hotonta hankalin ki ya kwanta, nima dai kin kusa bani nawa babyn ko."? Murmushi kawai nayi masa ina Allah-Allah ya mik'o min wayar in gani.. Da sauri na karb'a ina dubawa sosai baby Aysha take kama da Mimi sai da tafi ta haske kamar yanda naji suna fad'a ta murmure sosai da gani ma hoton tana jikin babanta aka dauka don ga jikin shi nan ya futo da hannunshi guda da ya rike ta, Dole in gane saboda manya manyan azurfan dake bisa yatsun sa. Wayar na rungume a k'irjina ina sakin ajiyar zuciya nace"Jahid baby Aysha na kama da Mimi wallahi ka bani wayar nan yau ta kwana a hannuna in kwana ina kallonta kaji. " dariya yayi yace." Kece kin ki ki bude whatsp da sai na turo miki hoton." Da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78