Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 58

Chapter 58

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da masu gadi dole sai sun shigo Estate din......... Rambo ya koma ciki da sauri yana fadin "Sir babu lafiy!... Kafin ya rufe bakin sa saga Mujahid da Khalid sun shigo da sauri. Mujahid yace." Meye abun yi ne? Idan fa suka shugo gurin nan zasu yi barna domin dukanin su 'yan daba ne da 'yan Sara suka."!!! Amjad yace." Ni suke nema baku ba, zan futa su kashe ni kan abunda ban aikata ba." Da sauri yayi nufin futa. Mimi tq buga wani irin ihu!!! Da gudu tayo kansa tana fad'in"Kar ka futa su kashe ka."!!!!!!!!! Hannunta ta mik'a tana son rik'o shi santsin tayal ya kayar sa ita ta fad'i a kan cikin ta hade da sakin wata razananniyar k'ara! Hankalin su duk ya koma kanta suna salati, Hakan ya bashi damar fucewa da sauri! Ba tare da ya juyu yaga me yake faruwa ba. *23/11/2019* [11/24, 12:07 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *61* Wani irin nishi! Mimi take yi idanunta na lumshewa yayin da bakin ta yake motsawa tana so tayi magana amma babu hali hannunta biyu tasa ta damk'e cikinta dashi da kyar ta fad'i"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!! Sharaf! Ta zube a jikin granny. Rungume ta tayi ta fashe da kuka hade da d'ago kanta tana Neman Amjad, wayam babu Shi a gurin, da sauri ta kalli Mujahid murya a sark'e tace" Ya futa shima zasu kashe shi."! Dukaninsu hankalin su ya dawo jikin su, take suka fara rige-rigen futa, suna salati. Granny kuwa rungume Mimi tayi tana kuka duk basirar ta ta toshe a lokacin. Yana futa ya hangosu sun samu nasarar shigowa, ciki dake akwai tazara mai mugun tsayi kafin su gurin shi, sai suka yanko da gudu suna ihu! K'ik'am ya tsaya had'e da hard'e hannunsa a kirjin sa yana jiran k'arasowar su. Mujahid Khalid da Su Rambo sun tsorata mutuka suka fara Jan rigar shi. Fuzgewa yayi a zuciya! Yace. " Ku jira Ku ga abunda zai faru, wallahi duk Wanda yazo gurin nan to sai dai Uwarshi ta haifi wani." Ja da baya suka yi cike da tsoro! Fito yayi sai ga DOG dinshi ya shek'o a guje! Yana wani irin haushi!!! Magana yayi masa da ido. Aikuwa sai ya buga wani uban tsalle ya tunkari su yana wani danbanzan zufa ya cafki k'afar daya daga cikinsu sai da ya huda ta tukkuna ya sake shi. Kafin kace kwabo ya fad'i a gurin yana nishi ga jini ya fara zuba. Wani tsagera ne ya kawo sharb'eb'iyar wuk'ar zai dab'a masa, da sauri yayi sufa ya datsa masa hak'oran sa a fuskar sa, dai-dai hancin sa, ya yago Innalillahi sai ga rabin hancin sa da naman kumatun sa a bakin DOG din. Kwanciya yayi a gurin yana ihu! Shi kuwa Amjad nad'e hannun Riga yayi ya tunkare su, yana wani zare idonsa! Tsoro ne ya shige su dukanin su ganin yanda dog din yake barna har ya jikkata mutum biyar gasu nan a kwance a gurun. Take suka fara guduwa domin ceton ransu. Amjad ya buga musu wata irin tsawa! Tare da fad'in"Ku tsaya mana ku kashe ni kamar yanda kuke bukata."!!! Ko juyo wa basu yi ba, gudu kawai suke su Isa bakin gate. Daga murya yayi sosai Wanda sai da gurin ya amsa yana magana da masu gadi cewar maza su rufe gate din nan, kar su bar kowa ya futa." Aikuwa suka mike da kuzari suka ja gate din da k'arfi suka datse A nutse yake tafiya hannunshi goye a bayan shi, fuskar sa a murtuke ya k'araso gurin su: One by one yake kallonsu tsawon five minutes, murmushi yayi mai ciwo yayi gyaran murya gami da gyad'a kansa har sau biyu murya sama! Yace." Kun shigo da shirin aika ni barzahu ko."? Shiru su kayi suna muzurai! Gefe guda kuma ga *Tegar* na wani irin haushi!!!!! Shiru suka yi........ Ya cigaba da cewa"Zaku kashe ni kan abunda kuke zargina dashi, Wanda ni nasan ban aikata ba hakane ko ba haka bane."? Sunkuyar da Kansu suka yi cikin mutuwar jiki. Girgiza kansa yayi cikin takaici da tsabar bakin ciki yace." Gani ga ban Ku Ku kashe ni, ni Ku kashe banza kamar yanda kuke fad'a. "! Tsit! Suka yi. Yace." Duk Ku aje makaman hannun Ku." Aikuwa suka aje da sauri! Yace." Kuna so Ku kashe ni Wanda baku San in kuka aikata haka ba, to babu shakka hukuma zata dauki mataki akan Ku, tunda ba ita ta sanya Ku ba,hakane ko ba haka ba." Duk suka ce "Hakane."! Yace." Duk abunda kuke zargina dashi ban aikata ba, sharri ne kawai, akai mun. " Shiru suka yi ya cigaba da cewa"Kuma Ku zuba ido zaku ga irin hukunci da za'a dauka a kaina, tunda dai kun k'one company na kunji dad'i shikkenan, amma babu shakka sai na binciko Wanda aka had'a baki dasu aka kullamin wannan k'azafin." Duk sai suka ji jikin su ya mutu, take suka zube suna bashi hakuri. Murmushi yayi yace." Ba wai na fad'a muku Wannan maganar ba ne domin Ku yarda da ita, A'a duk wani hukunci da zaku yanke kaina Ku yanke Ku kashe ni ku kashe banza."! Ya fada da wani murmushi a fuskar sa, na tsantsar takaici. Hakuri kawai suke bashi cikinsu kuwa har da masu kuka saboda tausayin sa. Yace." Mutukar nakama mutanan da aka hada baki dasu cikin ma'aikatana tom ni da kaina zan hukunata su da kaina in yaso nima a kashe ni saboda kishin Allah da manzon sa." Ya nagama maganar shi ya juya bayan ya bada umarnin a bude musu k'ofa su futa. *Tega* ya bishi a baya Yana shinshina m asa jiki: Wani irin salati Granny take yi,lokaci kank'ani jikinta ya kama rawa ganin wani irin jini yana malalowa k'asa daga jikin Mimi. Kuka ta fashe dashi tana salati ta janye Mimi daga jikinta Ta mike Da sauri ta nufi kofar futa. Karo suka buga dashi ya shigo. Hannunsa ta rike takasa cewa dashi komai sai dai nuna masa gurin da Mimi take kwance take. Da sauri ya kalli gurin, jini duk ya kwaranya kan tayal din gurin. Wani irin ihu! Ya kurma! Ya saki granny da gudu ya k'arasa gurin Mimi ya dauke ta kamar zautacce yake kiran sunan ta"Momy na."!!!!!!! Ina Mimi bata San wace duniyar take ciki ba, da gudu ya futa daga Palo, mota ya nufa da gudu su Rambo dake tsaye suka bishi, Mujahid ya bude motar da sauri ya shiga mazaunin dravar, jiki na rawa Rambo ya bude masa mota ya shiga rungume da Mimi a jikinsa jini duk ya b'ata shi har ila yau bai daina zuba ba.!! Da gudu Jahid ya figi motar masu gadi suka bude gate din tun kafin motar ta karaso. Wani irin gudu Jahid yake yi kamar zasu tashi sama, Allah yasa titi akwai saukin motoci kasancewar kowa na gida an sha ruwa an gaji wasu kuma na massalaci suna sallahr

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});