Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ma haka. Addu'a da fatan alkairi babu irin Wanda bai sha ba abakun mutanan gari Yau saura kwana bakwai sallah. Muna ta shirye-shiryen sallah. Lokacin Cikin Mimi ya futo sosai tunda yana matakin watanni shida tayi kiba sosai sa sosai kuma ta kwantar da hankalin ta. TV muke kallo inda muke kallon tafsiri daga bakin Marigayi shak Isa Waziri Allah ya jikansa. Kawai. Umma ta kunna redio murya wani shararan Dan jarida muka ji yana fadin"Salamu alaikum jama'ar jahar kano, labari da dumi-dumin sa, an yaka dai ta tashi yanzu-yanzu muka samu labari daga majiya me k'arfi shararar mutumin nan Wanda yayi suna a jahar kano, wato *Young millionaire Amjadu Abul Abbas mai nasara* wato mamallakin wannan shararan company me kawo muku nauin kayan sawa kama daga atamfoffi yadiga lesuka mayafai dogwayen riguna bulawus kayan yara hijab da sauran su, wannan company mun samu labari yanzu yanzu daga bakunan wadanda suke sari a cikinsa, cewa company ya hada baki da yahudawa nasara masu yak'i addinin musulunci masu adawa da fad'ar Annabi Allah wato Annabi Muhhamadu Slw a takaice dai an samu jikin takalman da company ya ke kerawa kasan takalmi an rubuta sunan Allah da manzon sa wato Allahu Muhammad, Jama'ar gari me zaku ce da wannan shirkar da wannan yaro da kuka amunce masa ya aikata."" "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un shine abunda Umma take fad'a, take ta fashe da kuka tana gyda kanta take fad'in" Wannan zan sharri ne tswagaran sa na tabbatar yaron nan bazai aikata wannan danyan aikin ba." Nima jikina wani irin shocking yake jin abunda Dan jaridar yaje fad'a, Cikin zuciya ta nace"Anya kuwa guy nan zai aikata Wannan Abu, duk da dai nasan Duk ak'idun shi na nasara ne kuma Duk yawanci abokan shi turawa ne, wata zuciyar tace min tabbas zasu iya rinyarsa dama ba wani tsoron Allah yake ba, tunda yana aikata zina." Kuka Umma take yi sosai da sosai Ya Aminu ya shigo gidan hannunshi rike da Leda me zane-zane da Lemo da a yaba a ciki. Ganin Umma na kuka ya tabbatar labari ya same su Umma tace"Kaji sharrin da jama'ar gari sukaiwa wannan yaron mijin Mimi ko."? Ya Aminu ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya yace." Duk naji Umma gashi can ko ina ana surutu zancan ya cika gari. Matasa sun fara gazgatawa domin wani Dan kasuwa ya futo da takalma na company an duba an ga gaskiya al'amarin. Umma tace." Karya ne sharri ne aka shirya masa ni na tabbatar. Ya Aminu yace." Umma sai ta iya kasamcewar gaskiya ne Wallahi mutane da basa tsoron Allah, ni dama wannan uban kud'in sa suna tsorata ni, akan ya samu duniya babu abunda ba zai yi ba." Nace"Wallahi Ya Aminu nima na gasgata saboda d'abi'un sa duk na turawa ne. Gaskiya gomnati ta shiga maganar kuma kamata yayi a dauki mataki akan sa, domin Allah da manzon sa ba abun wasa bane." Ya Aminu ya bude baki zai yi magana kawai mukaji ihu!!! Da hanayi ana gudu radadada!!! Da gudu nayi waje ya Aminu ya biyo ni a baya. Gungun matasa majiya k'arfi ne suke tada k'ura ko wanne hannunsa rike da makami wasu jarkar fetur da kalamzir da tayoyi suna fadin "Billahillazi sai mun k'one company mu zai yaudara! Sai mun konashi mu kashe shi!! Mu kashe banza."!!!!!!!!! D'uuuuuu suke wucewa sunfi su Dari ga magariba ta gabato ana shirye-shiryen shan ruwa Umma ta tsorata mutuka fad'i take" Asma'u maza buga wa Mimi waya ta tawo gida innalillahi wa'ina ilahi raji'un. " Jikina na kyarma! Na koma cikin gida zuciya sai harbawa take yi mutukar wad'annan matasan sukayi arangama dashi to babu shakka sai sunga bayan sa, hannuna na rawa nake Neman numbar Mimi, kiran duniya taki shiga. K'afafuna na rawa na futo in na fadawa Umma halin da ake ciki. Hannunshi rike da jarida yake zagaye parlor bashi, Rambo da doh Mimi da granny duk suna tsaye suna tararrabi da al'ajabin wannan Abu.wayoyinsa kuwa tuntuni ya sanya rambo ya kashe su, saboda a halin da yake ciki magana ma bazai iya yi ba. Shin wai me ya tsarewa mutane ne a duniya.? Granny kuka take yi tana fadin"Wannan kaddara da masifa Allah ka ije mana ita, Ubangji kaga zuciyoyin mu bamu aiktaba Allah ka tona asirin masu San su ga bayanmu. Granny ya rungume a jikinsa yana d'an dukan bayanta da hannunshi ya ma kasa cewa komai, idanunsa sunyi wani irin jajazur! Tsabar tashin hankalin da yake ciki. Tv suka k'urawa ido inda suke ganin jama'ar gari kofar company sa sune turareniya da rigima da masu gadi kan lallai sai sun shifa ciki wasun su kuwa tuni sun soma k'ona tayoyi suna watsa fetur da kalanzir jikin company, ihu! Da hayaniya ya cika gurin, 'yan jarida sai dauka suke yi. Tuni wani tsagera daga cikinsu ya k'yatta ashana ya yi wani tsalle hade da jefa ashanar sama, kafin k'iftawa da bisimillah wuta ta kama fa!fa!fa! Jikin gatangun company har ta soma haurawa ciki, hucin wuta yasa jama'a darewa kowa na gudu domin ceton ransa, ciki kuwa har da masu gadi. Tuni matasan suka samu damar shiga ciki kasancewar gurin ya hargitse kowa na ceton ransa. Take 'yan jarida suka rufa musu baya domin dauko rahoto. Lungu da sak'u ko ina sai da suka bi suka watsa fetur ko zafin wuta basa ji, da gudu ma'aikatan suka dinga futowa suna kama Katanga suna haurawa domin ceton rayukansu, ganin yanda wuta take ci ne ba!ba!ba! Yasa 'yan jaridar dasu matasan suka dinga gudu suna kama Katanga suna dura kasa, duk da haka wasu sun jikkata kuma sun k'one cikinsu sudai kawai burin su ya cika ganin sun rusa company. ****** *"Hahahahahaha"* wata mahaukaciyar dariya na juyo a ofis din me girma governor, da sauri na lek'a ta k'afar mukuli, na gansu sun fi su goma zaune Cikin kujeru tsakiyar su kwalebe ne da cup reras kan wani makeken teble. Mai citta ya dauki abunda yake cikin cup din gaban sa ya kurba tare da ajewa fuskarsa cike da annuri da farin ciki, naji yana fadin"Shegen kaya! Wa yaga masa barno gabas take! Ai sai ya daina motsi a duniyar nan sannan zamu saurara masa."!! Dariya suka shek'e da ita "Hahhahahahahaha."!!!! ***** Har aka sha ruwa yana tsaye a tsakiyar parlor babu yanda granny bata yi dashi ba kan yazo ya karya yak'i kamar ma kurma ya zama Wanda baya ji ba ya gani, kawai ya zubawa guri guda ido .Su Kansu Rambo da doh-doh sun tausayawa masa. Mimi na kuka tazo ta rungume shi tana rarrashin sa, da sauri ya juyo jin tsinin cikin ta yana zungirin shi a bayan sa. Tsungunawa yayi ya kasa kunnesa cikin NATA yana lumshe ido. Kamar wani zautacce ya d'aga rigar ta yana shafa cikin nata, a hankali yace." My boy ina cikin damuwa!!!! Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!! Kalmar da ya kamata ya fad'eta tun farko fara abun bai fada ba sai yanzu Allah ya bashi iko. Mimi kuka granny kuka an rasa me rarrashin wani a cikin su. Wata irin hayagaga! Da hayaniya! Suka ji ta cika gidan. Zumbur! Ya mike yana niyyar futa Rambo da doh-doh suka dakatar dashi da sauri suka futa. Gungun! Jama'ar gari suka hango suna kokawa

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});