Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 77

Chapter 77

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jama'a, can ya kalli Umma tare da fad'in"Ina Asma'u ne? Umma tace"Tana gidan auntku ita da kawayen ta." Ya Aminu yace." Ya kamata tazo muyi hoton tarihi."Umma tace"Kai ta hoto kake Aminu shin wai kasan abunda ke faruwa ma kuwa. "? Aminu yace." Na San komai Umma Asma'u dai ta auri Amjad hakuri ne ya kamace ta domin anyi mata laifi dole a rarrashe ta."Umma tace"Ina gudun abunda zai je ya dawo n........ Kafin ta rufe bakinta suka shigo gidan, hankali jama'a yayi caaaa! Kan Asma'u kowa na fadin albarka cin bakinsa akan ta, murmushi kwai tayi hade da rufe fuska su Maryam suka rufa mata baya, Munnu kuwa dama tun ana gobe d'aurin aure ta koma gida. Maryam ce tace"Wallahi kinyi kyawun da baki tab'a yin irinsa ba a duniya Asma'u wai dama haka kike da kyau!. Hafsa da bata San abunda yake faruwa ba, tunda tun ana saura kwana biyu tazo gudansu Asma'u suka had'u da sauran kwayen su irinsu Alina ake gudanar da shagalin buki tare tace"Wallahi nima haka nifa k'amshin da take yi ne nake bala'in so gaskiya dole idan na tashi aure aunty Hauwa tayi min irin wannan gyaran domin in burge autan maza." Shewa! Suka sa, Alina ta tab'e baki tare da fadin"Yo ke dama Hafsi wannan jikin naki ai dole sai da mugayen turarrika masu karfin gaske. " b'ata fuska tayi tace"Alina bana son iskanci aikin banza kawai." Cikin danne damuwar da nake ciki gami da fuduwar Gaban dake damuna tunda na tashi nace" Alina ki saurara don Allah bana son tashin hankali a bukina." Dariya suka kwashe da ita..... Waya ta dake hannun Hafsa na karba INA dubawa naga 5miscall daga Jahid, kiram shi mayi, aikuwa tana daf da tsinkewa ya dauka muka gaisa a nutse yace." Ganinan zanzo daukar ki zamuyi hotuna da abokaina." Yana gama maganar shi ya kashe wayar .... Tsoro ne ya shiga zuciya ta nace"Allah yasa kar Jahid ya taba ni tunda yanzu yaga an d'aura aurenmu. Sama-sama muke hira dasu Alina Umma ta leko dakin tana fad'in"Asma'u kizo ki daukar muku abunci mana." Maryam ce ta mike da sauri tana fadin"Gaba Umma mu meye aikin mu, amarya guda dama yanzu nake cewa bari in zo in daukar mana towon d'aurin aure. " Umma tace"Nima abunda na gani kenan. Dukanin Ku babu bare a gidan nan duk yan gida ne." Marya ta bi bayan Umma tana fadin Wallahi kuwa.'' Ina kallonsu sun rufu kam abunci suna ci suna shewa cikin farin ciki, sai suka bani sha'awa sosai ko wace mace tana farin ciki da ranar auranta ni kuma na tsinci kaina da bakin ciki komeye dalili oho. Wayar Jahid CE ta katse min tunanin da nake yi yace." Ki fito ina jiran ki amaryar mu." Sam ban fahimci me maganar shi take nufi ba, na miike Alina tace"Ko inzo in raka kine."? Gyad'a kaina nayi kawai na barsu a dakin. Dakin Umma na shiga tana cikin Uwar daki ita da jama'a. Tana ganina tsabar abunda take yi jiki a sanyaye ta k'araso inda nake tsaye, Umma duk a tsorace take tana gudun kar Asma'u ta tsinkata cikin jama'a. A hankali nace"Jahid ne ya kirani a waya yanzu wai inje zamuyi hoto da abokansa." Jim! Umma tayi na minti biyu tace"Anya Asma'u akwai dacewar hakan kwa "? Sunkuyar da kaina nayi tace" Kije tom ban san manufarsa ba amma ki cire wannan yalolon mayafin na jikin ki tunda kinga irin yadin dake jikin ki kamar Net gashi kinyi dinki matsatsatse kamar jaraba idan da hali ma kin sauya kaya kawai. In babu hali to ki sa mayafi babba tunda kinga gurin da zakuje ba shi kadai bane." Nace"Insha Allah Umma." Wata shegiyar liffaya na zare cikin ledar ta fara kal mai golden d'in stones a jikinta tana da manyan zanen fulawa Umma da kanta ta nad'a min a jikina na rike k'aramar pose dina mahadin takamin dake k'afafuna, na futa daga gidan a nutse. Shi kadai na gani jingine a jikin motar sa, yana sakar min murmushin sa nima na mayar masa bude min motar yayi na shiga na zauna shima ya zauna mazaunin sa ya kunna motar muka bar gurin. Kallona yayi da Murmushi a fuskarsa yace." Amaryamu kinyi kyau mutuka Wallahi." Nace"My Jahid kenan Ina maka fatan alkairi a rayuwar ka." Gyada kansa yayi yana jin wani Abu cikin zuciyarsa yace." Alkairi Allah ya dauwama a duk inda kike Asma'u. " Ameeen ameen mijina " abunda nace kenan cikin jin kunyar sa. Shi kam Jahid draving yake yana addu'a cikin zuciyarsa kan bala'in son da yake wa Asma'u wacce a yanzu ta zama mallakin wani Ganin mun dauki hanyar Jambulo yasa nace"Jahid ina zaka kaini ne."?yace." Gidana mana kin San abokai da 'yan uwa sun had'a min walima k'arfe shida na yamma shine na dauko ki ki shirya a gabana idan anjima zan sanya a dauko kawayen ki." Cikin takaicin sa nace"Jahid wannan bayi bane fisabillilahi a ina zan zauna har a wa hudu yanzu." Ya bata fuska tare da fadin''ki zauna gurin granny mana wani abun ne."! Nace"Jahid kasan bama shiri sosai da mai gidan me zai sanya in zauna masa a gida. " yace." Baya gari Amjad ki kwantar da hankalin ki " shiru nayi masa ganin ransa kamar ya soma b'aci a zamana dashi na fuskanci baya son ja'inja." Ko da muka shiga cikin gidan babu kowa a gurin sai masu gadi da karnuka da suke kwance sai dai na lura da karuwar motoci a gurin, kai tsaye part din Amjadu muka nufa har shi Jahid din. Cikin rashin sanin komai na shiga ciki. Amjad Granny Iyami Baba Rakiya da wasu mata uku suna zaune a parlor suna hira. Sai a lokacin kunya ta kamani nayi kamar in koma da baya. Baby dake jikin iyami ta tsandare da ihu!! Wanda ya sanya shi bude limsassun idonsa ya mike da sauri hankalin sa na kan babyn dake zillo dole sai ta sakko tazo gurina. Granny tace da Iyami ta sake ta, aikuwa Iyami na sakin ta ta rarrafo dasauri ta kamani ta mike tsaye da sauri na dauke ta hade da rungume ta tsam a jikina, baby Aysha ta dinga kyalkyala dariya tana kallon Jahud dake tsaye kusa dani yana kallon abun mamaki. Kallo guda yayi musu ya koma ya kwanta kan doguwar kujera da yake kwance lumshe idonsa yayi yana haskon fuskar Asma'u a ganin da yayi mata yanzu, tunani yake yi shi dai iya sanin sa sao dare ake kawo amarya tom ita me ya kawo ta gidan shi da rana tsaka. Jahid ya karasa cikin parlor sosai suna gaisawa da granny cikin mutumci yace." Granny ga alk'awarin mu nan na kawo miki har gida kin gane dai manufata duk Wani Abu da zai biyo baya mai sauki ne." Granny tace"Ka cika d'an halak kuwa ubangji Allah yayi maka albarka ya raba da sharrin duniya." Yace." Ameeen ya rabbi Bari in shiga gida akwai abokanan mu dake jirana, Asma'u zata zauna nan zuwa anjima. " gyada kai kurrum granny tayi domin ita San ya fad'i hakane kawai amma aikin gama ya riga ya gama. Duk abunda yake faruwa a gurin yana jinsu, yayi bakam! Hancin sa ne yake shak'o masa daddad'an kamshi

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});