Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a gaskiya Baba babu mahalukin da zan iya barwa Mimi domin nima idan nayi haka zan iya shiga cikin tashin hankali watak'ila ma nawa yafi nata tunda kowa ya shaida nafi sonta ita bata sona saboda haka ni ina gani kawai daga nan zuwa jini a d'aura mana aure da ita ba sai an jira lokacin da aka sanya ba, idan taji labarin haka nasan dole zata hak'ura ta fawwala Allah kasan dama ance kiyyayyar 'ya mace bata tasiri ina ganin Mimi zata hak'ura ta zauna dani."! Kawu ya gyada kansa yana Nazarin maganar Aminu Yaro Yaro ne, murmushi yayi yace." Aminu kenan, kamar ka manta abunda Dr yace akan Aishatu, Jin labarin d'aurin auranku zai iya sanyawa zucuyarta ta buga gaba daya ta mutu lokaci guda, kaga kuwa wannan sha'awar taka ba abun dubawa bace." Aminu ranshi ya b'aci da jin abunda Kawu yake fada murysrshi a kaurare yace." Kai ya kake ganin za'ayi." Kawu ya kalleshi cike da mamaki jin yana yi masa magana kazar-kazar babu Wani ladabi. Yace." Abunda za'ayi shine mu samawa Aishatu abunda take so domun samun ta da tabbatuwar lafiyar ta. Aminu ya watsa masa wani kallo tare da fadin"Kawu in na fahimce ka anan shine kana so kace min in hak'ura da Mimi in yaso Ku bats Wanda take so kome."? Kai tsaye..... Kawu yace." Shine abunda nake Nufi." Aminu ya guda kansa yana murmushi me ciwo yace." Impossible, bazai tab'a yiwu wa ba Kawu Mimi 'yar kace nima inda kara d'an ka ne nasan baza ka bawa Mimi bare ba gani a zaune, ina so saboda haka yanda aka karb'i kud'in aure na da Mimi to babu mahalukin da ya Isa ya hana tabbatuwar auramu idan ba Wanda ya hallice mu ba." Cike da d'umbun mamaki Kawu yake kallon Aminu ganin yanda yake wani irin huci!! Yace." Aminu ka fahimce ni mana ba wai ina k'in ka ban......... Kafin ya karasa Aminu ya daga masa hannu a fusace.!!! Yace." Kawu ga magana nan ta futo kanunamin bakai ka haife ni b.... Cike da b'acin rai Kawu yace." Rashin kunya zakayi min Aminu. " Daga kafad'a yayi tare da fadin "Babu maganar rashin kunya anan Kawu gaskiya ce ni nayi rantsuwar babu Wanda ya Isa ya hanani auran Mimi." Ganin tsageran cin da Aminu yake masa ne yasa ya fusata shima yace." Aminu indai nine waliyin Aishatu to baza ka aure ta ba." Aikuwa sai ya ingiza Aminu ta inda ya shiga sirfa masa rashin kunya wanda ya jawo hankalimu Kansu dukanimu mu k'araso gurin tare da tambayar ba'asi Abunda Aminu yake yi yayi bala'in konawa Umma rai ta cire hannunta ta zabga masa mari cikin tsawa tace"Na kara jin bakinka a gurinan Aminu sai na tsine maka, a tunanin ka wannan tsagerancin da rashin kunyar da kake yi shine zai sanya a baka auran Mimi ko meye."? Kawu yace." Kyaleshi ya zage ni son ransa lokacin sa ne." Wuce mu yayi tafi can bakin get ya zauna tare da masu gadi Fada sosai Umma take wa Aminu Tace" Haka ake soyayya da hauka Aminu ka futo da son zuciyarka a fili kana ganin mawuyacin halin da yarinyar nan take ciki shine zakaje gwara ta mutu a kan ka janye kudirin ka a kanta, me yasa ita lokacin da ka fad'i har ka kwanta a asibiti tace"Zata aure ka alhalin ga Wanda zuciyar ta take so Mimi yarinya ce me ladabi da gudun b'acin rain wani ta so ta faranta maka ta faran wa zuciyata ba tare da ta damu da nata farin cikin ba, shine yanzu tana cikin halin rai da rayuwa kake mummunan magana a kanta Aminu wannan ba soyayya bace."!!!! Umma ta karasa maganar ta tana haki! Kana ganinta zaka fahimci tana cikin tsananin b'acin rai da damuwa Cikin kuka na futar hayyaci nace"Wallahi tallahi Umma mutukar Ya Aminu bai janye kudirinsa ba nima bazan aure shi ba, sai dai mu zauna a haka, kawai a aura mata Wanda zuciyarta take so ta huta da wannan azabar da take sha." Umma tace." Ki kwantar da hankalin ki insha Allahu Mimi bata da Miji sai Amjadu dole a bawa zuciyarta hakuri abata abunda take so." Ya Aminu ya kalleni ya kalli Umma zuciyarsa nayi masa wani irin ciwo yace." Umma don bani da kudi bani da aikin yi bani da mota bani da babur bani da keken hawa kana bani da kudi a banki kuke mun haka,? Meye laifi na meye? Aibuna anan Zan kula da Mimi zan tsare mutumcin ta zan sanya ta farin ciki! Umma kar Ku kware min baya akan Mimi Ku duba halin da zan shiga a kanta soyayyar ta tana iya kashe ni!!!!! Umma ni danki ne baza ki so wani bayan ni ba, Umma ki dube ni da idanun rahama!! Ki tuna so da kaunar da kike min Umma ki bani Mimi domin itace farin cikin rayuwata."!!!!!!!! Ya k'arashe maganar sa hawaye na zubowa daga idanunsa Umma ta zube a gurin Tare da dafe k'irjinta tana salati aunt Hauwa da Ummansu Munnu suka rike ta hawaye ne ya fara zirarawo daga idanunta muryarta na rawa tace"Ya Allah ka ije mun wannan masifa da ta tun karo ni, Allah ka sanyaya min kasa kawo karshen wannan badak'ala!! Sai hawaye sharrrrrrrr-sharrrrrrrr suka fara zuba a kuncinta. Duk taurin zuciya irin ta aunt Hauwa hawaye ta fara sharewa ganin Umma tana kuka abunda zai sanya Umma kuka ba Karami bane hakuri kurum suke bata Ni ko da sauri na bar gurin bayan na warce wayar Munnu dake tsaye, wani d'an korido na nufa dake Cikin asibitin na fara Neman numbar sa, sai da tayi ringing sai uku ba a dauka ba, Sai ana hudu ne ya dauka muryarsa da yanayin bacci yayi sallamsa da sauri nace." Kanwa ta kar tsami! Kwarna fi ya kwanta. "!!!! Jin muryar yarinyar ya sashi mik'ewa zaune da sauri hade da yaye blanket din jikinshi na ci gaba da cewa " Yanzu haka muna babban asibiti na zana Mimi a kwance rai a hannun Allah bayan tafiyar ka, jini ya tsinke mata ta baki ta hanci!!!! Ta galabaita mutuka duk ta dalilin ka!!! Ina kara fada maka duk abunda ya same ta Kaine sila Kaine! Mujaza!! Mahaifiyar mu ta zubar da hawaye akan haka, mun zubar da hawaye a kan haka, duk wani mai imani ya kalli Halin da Mimi ta shiga a yanzu sai ya tausaya mata, insha Allahu duk wani sharrinka sai ya koma kanka ka cuce mu, ka yaudare mu, Ka azabatar da zuciyar Mimi akan sonka kullum kana fada cewar zaka aure ta, alhalin karya kake!!! Wallahi mutukar ka bari Mimi ta mutu baka yi Wani Abu akai ba nima sai na kashe ka."!!!!!!!!!!! Kamar wata mahaukaciya haka na k'arashe maganar..... Wata irin zufa ce ta keto masa duk da cewar akwai AC a dakin Muryarshi sanyi k'alau yace." Asma'u.!!! " saurin kashe wayar nayi na zube a gurin hade da fashewa da kuka mai cin rai. Mik'ewa yayi da sauri ya duro daga bed din toilet ya nufa ya dauro alwala ya futo yana kallon agogo bango uku shaura na dare, Jallabiya ce a jikinsa sai garan wando ya dauki wata rigar sanyi sa mai hula ya sanya

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});