Chapter 27
Chapter 27
A hankali na shiga motar na zauna ina kauda fuskata. Ya kalle ni na minti uku, kana yace." Wannan kukan da kike yi Sam! Ba zai miki maganin komai ba sai dai ma ya kara sanya miki damuwa da ciwon kai, Yanzu shawara zamu yanke dake idan kin amince ni mai sauki ne." Kallonshi nayi ina d'an ya mutsa fuskata nace"Ina jinka." Shiru na minti biyu bai ce komai ba yana kallona, na dago kaina hade da watsa masa harara nace"Kace lokacin sallah ya kusa amma kuma ka sanya ni a gaba kana kallo kamar tv." Ajiyar zuciya ya sauke hade da lumshe idonsa, k'asa-k'asa naji yace." Asma'u Allah ne kadai yasan ita a dadin kaunar da nake miki a cikin wannan zuciyar tawa, tun da nake a rayuwata ban tab'a furta wa mace WANNAN Kalmar ba sai ke, duk da cewar nayi rayuwa da 'yan mata iri-iri masu kyau da kudi Asali nasaba da wayewa amma babu wacce ta samu wannan Kalmar sai ke." Shiru nayi sauraron shi. Ya cigaba da cewa "Ina da kudi sosai Wanda ban San iya a dadin su ba kuma kullum karuwa suke yi ina zakka da duk wani Abu da Allah yace kayi da dukiyar da ya baka amana, Abu guda ya rage min mata, kuma na samu insha Allah." Shuru Yayi na minti biyu ya cigaba da cewa "Mimi ta bani tausayi mutuka nasan illar so, tabbas tana so na, Wanda naji a zuciyata dama kece kike min irin son da take min da babu namijin da ya kaini dacewa a duniyar nan." Kallonshi nayi jin abunda yake fada. Dauke kaina nayi hade da d'an ya mutse fuskata nace"Me yasa ka yaudari Mimi kasan baka son ta." Shiru yayi yana nazarin magana ta can naji yace." Da farko da wasa nake yi, amma daga baya na d'aura niyyar auranku tare domin in cuzguna miki dalilin yin haka kuwa shine Rashin mutumcin da kika je kikayi gurin pary Ku ya bani haushi shiyasa na yanke wannan shawarar." Murmushi nayi me ciwo nace"Idan domin ka bani haushi kace zaka auri Mimi a lokacin wallahi da baka wahalar da kanka,saboda kasan shi so sai ana kishin mutum ake yin sa, Mimi tana sonka tana kishin wani ya rab'e ka ciki kuwa har da ni, Mimi ita yafi da cewa ka aura bani ba." Fuskarsa ya Dan hade yana kallona tare da k'ankantar da idanunsa yace." Gashi ni kuma ba Mimi nake so ba ke nake so, sai dai idan kin yarda in hada ku, Ku biyu in aura amma duk abunda ya biyo baya kar kiyi kuka dani." Ba tare da tunanin komai ba nace"Ni dama akan wannan k'adami nake, Ya Aminu dole ya janye maganar auran Mimi idan yak'i janjewa nima nace bazan aure ka ba, sai dai duk mu hak'ura dama ni ban damu ba, itace abar damuwa." Gabanshi ya fad'i jin abunda take cewa, tana nufin idan Aminu bai janye maganar auran Mimi ba itama baza ta aure shi ba? Lallai a kwai badakala anan gaba, idan Aminu yak'i janje maganar shima ya kusa fadawa chakwakiya kenan, yanzu zai canza salo domin ya risinar da zuciyarta iya zaman shi da ita ya fahimci yarinya ce me mugun taurin kai da kafiya.Dole ya nema wa kansa mafuta domin bai San abunda zai je ya dawo ba nan gaba. Shiru motar tayi bayan na gama magana ta. Yace." An sanya wata uku na auranmu ina ganin za'a kara sauko da lokacin k'asa saboda gudun wata masifar, ki San yanda zakiyi a gida ki ga Aminu ya janye kudirin sa daga kan Mimi ni kuma zan aure Ku ga ba d'aya." Motar nake kokarin bud'ewa ina fadin"Kai kake damun kanka da lallai sai ka aure ni, nifa idan Ka aure duk d'aya idan baka aure ni ba ma duk d'aya ne, mutukar ka aure Mimi da ka sanya ta fad'a komar ka shikkenan bukata ta tabiya domin likita yace zuciyarta daf take da ta buga." Ina gama magana ta na bude motar hade da fucewa a fusace.!! Kallo ya bita dashi cike da mamakin gaud'ancin ta yarinya mai baud'andan ra'ayi shi a yanzu ma ya rasa in da ta dosa. Jikinsa babu kuzari yaja motar ya tafi zuciyarsa na masa wani irin ciwo idan ya tuno kalaman ta wai bata son sa, wannan kalma ta nayi masa mugun ciwo ya za'ayi ya auri macan da zata dinga gasa masa magana ko wace iri CE, da Alama Asma'u baza ta kula dashi. Mimi ita ke son sa sosai da sauran 'yan matansa tabbas a gurin su zai samu irin kulawar da yake buk'ata. Bayan munyi sallah gari yayi haske sai ga Babansu Munnu ya shigo a sibitin cikin motar sa, dama jiya gida ya koma saboda b'acin ran Aminu. Da sauri muka mike ni da Munnu muka karasa gurin da yayi parking din ya futo muka gaishe shi hade da karb'ar kayan dake hannunshi, k'aton Fula's din tea ne sai wata Leda babba cike da bread da kayan shayi dangin su madara da Milo gaba yayi muka bishi a baya. Cikin mutum ci suka gaisa da Umma aunt Hauwa ta gaida shi Aminu baya nan domin ana idar da sallahr ya tafi gida, kai tsaye..... Ciki ya shiga gurin dector Ni da Munnu ne muka had'a wa kowa tae d'in shi ga manya manyan bread nan kowa ya dauki Wanda yake so, Ni kam tea din kawai nake kurb'a bakina babu dad'i fargabar rashin lafiyar Mimi da tunanin maganganun Amjadu na d'azu, nayi mamakin yanda yake k'aryar min da kai da sanyayyar murya yake fadin Yana sona, mutum me kudi kyau mukami izza da ginshera duk ya na dasu, amma d'azu duk ya aje su gefe, gaskiya na gazgata maganar shi, tab'e bakina nayi kawai na cigaba da kurbar tae din amma lokaci zuwa lokaci sai in ji gabana ya fad'i tsigar jikina ta mike idan na tuna shi. K'arfe Takwas dai-dai wata nursa ta futo tace"An futa da Mara lafiyar yanzu zaku iya shiga Ku ganta duk da cewar ma yanzu za'a baku sallama." Da sauri muka mike dukaninmu muka fara turereniyar shiga duba Mimi. Tana zaune kan gado tayi wani firgai-firgai da ita fuskarta ta kode ta kara wani ufan haske Mimi da ma ba jikin arziki ba tayi wata irin rama lokaci guda. Umma na ganin ta sai hawayen ta ya dawo ta zauna kusa da ita hade da iri hannunta tana fadin"Mimi ke ce kika dawo haka lokaci guda." Ganin Umma na zubar da hawaye Mimi ma ta fashe da kuka kamar zararriya ta hau dukan k'irjinta tana fadin"Umma k'irjina ciwo da nauyi na rasa wace irin masifa ce wannan? Umma na rasa me yake damuna gwara in mutu in hutaa!!!!! Aunt Hauwa ta buga mata tsawa Cikin jin haushin ta tace"Don Allah ki daina wannan kukan da kike yi kiyi tawakkali mana ita rayuwar ai duk hakuri ake yi, kina kuka kina bugun k'irji dole hankali Umma ya tashi, ko me kike ji a zuciyar ki sai ki dinga fadin "Innalillahi Allah zai miki magani." Leb'anta na rawa tace"Aunt Hauwa baza ki gane ba ne, bana fata Allah ya dora wa wani masoyina abunda nake ji a zuciya ta, gwara in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78