Chapter 10
Chapter 10
Aunt tace"K'warai kuwa Umma wai sonta yake yi shine ya bata waya." Umma tace" Ni abunda na kasa fahimta a nan shine, shin da ke da ita Asma'u wa yake so a cikin Ku? Ke ya baki waya mai tsada ita kuma ya bata KUDI da kaya dukanin Ku akwai alamun tambaya a tare daku." Aunt tace"Shine maganar wallahi nima kaina ya kulle sosai." Hannu Ya Aminu ya mik'a tare da fad'in"Bani wayar." Mimi ta mik'a masa wayar jikinta a sanyaye . tashi yayi ya futa ranshi a mugun b'ace! ********* Yinin ranan haka yayi shi babu dad'i ko da suka futa da Anthony ma shi kad'ai ya dinga zurga-zurgar sa, sai sa komai ya kammala sannan suka dawo gida. Wanka kwai yayi ya futo parlor inda Anthony yake zaune yana aiki da loptol firji ya nufa ya dauko ruwa na gora ma sanyi tsiya yazo ya zauna kan kujera hade da bud'e ruwan ya fara tuttulawa cikinsa. [11/4, 5:34 PM] .: Ko da wasa bai kara kallon pictures din nan ba, yana ganin idan ya k'ara kallonsu zai iya had'iyar zuciya ya mutu. Wayar shi ya bude hade da bude data ya shiga whatsp yana dubawa, Alina ya ga ta turo masa da pictures, domin kwana biyu baya d'aukar wayarta ko ta kira, ko wancan karon ma da yaje birthday din ta cin sa'a tayi. Yana bude wa gaban shi Yayi wani irin bugawa ganin da yayi Asma'u tsakiyar 'yan iskan abokan Alina sunyi hoto*innalillahi wa'inna ilahi rajun* shine abunda ya furta ya mik'a zaune sosai zufa!! Na keto masa hotonan yake dubawa sosai lallai yarinyar tayi nisa, shi a ganinshi kamar jarabar ta ce ta sanya take shiga cikin maza ko zata rage wa kanta damuwa amma idan ba haka ba mace d'iyar Hausa Fulani tayi irin wannan d'inki Wanda dashi babu maraba da tsirara ta dinga keta maza, lokaci guda yaji zuciyarsa tana wani zafi tare da muguwar tsanar yarinyar, gani yake shine ya cuci kansa kwanaki baya da ta kawo masa kanta har gida, da ya sani ya biyawa kansa bukata tunda ita bata tausayin kanta. Pictures da Mimi ta turo masa yake dubawa, du Rabin su ita da Asma'u ne sai wannan budurwar da ya tab'a ganinsu tare wato Munnu, kayansu iri d'aya haka ma Dinkin su iri daya to wai me yasa d'inki a jikin Asma'u yafi nuna tsaraci. Shi kadai yake WANNAN tunanin, wata zuciyar tace masa ai duk tafi su ciki ta ko wane fanni.. Fuskarta yake kallo kamar zai lashe ta, har kara zomming din pic din yayi dai-dai ita yana kare mata kallo, ajiyar zuciya ya sauke tare da fadin"Zaki gane Baki D's wayo yarinya, wani pic din ya bude ,sai da wayar ta kusa fad'uwa daga hannunsa, ganin guy nan shi da ita suna kallon juna kamar masu kallon love. Ji yayi duk duniyar tayi masa zafi, ya kalli Anthony da jan ido cikin turanci yace." Gobe zan wuce najeria Tunda komai ya kammala anan." Anthony ya gyad'a kansa gami da cigaba da aikinsa Mik'ewa yayi da sassarafa ya shige bedroom din, kan wata duguwar kujera ya zube hade da dafe kanshi, yana cije lips din sa tunani kawai yake wane irin hukunci ya kamata yayi wa yarinyar nan. [11/4, 5:47 PM: ***** Kwanan bakin ciki da damuwa yayi a ranar, washe gari kuwa da wuri ya gama sallamar duk Wanda ya dace, ya bar amanar komai a hannun Anthony ya nufi k'asar sa ta gado wato Najeria. Sha biyu dai-dai jirgin su ya sauka a filin jirgi na Malam Aminu kano, su Rambo na gefa suna ganin saukowar sa suka k'araso da sauri Rambo ya karb'i wayoyinsa shi kuma doh-doh ya karb'i 'yar jakar sa. Suka nufi mota. Satar kallon fuskar sa suke ganin fuskar ogan nasu kamar Wanda aka aikowa masa da mutuwar iyayensa, Tunda ya shiga motar babu Wanda ya kula a cikinsu har suka isa gida. Get Man yana ta d'aga masa hannu tare da fatan alkairi ko kallonsa bai yi ba Doh-doh na gyara parking ya bude motar ya futo ba tare da ya jira rambo ya bude masa ba. Kai tsaye ciki ya nufa suka rufa masa baya, nan parlor suka aje masa wayoyin shi hade da jakar shi, suka futa da sauri. Yana shiga bedroom dinshi ya fada toilet Wanka yayi ya futo ko mai bai shafa ba, parlor ya futo masifa na cin sa, zama yayi hade da kiran Rambo a waya domin yaji meye labarin guy nan yana ganin ta kanshi zai fara. *4/November/2019* [11/5, 11:28 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *Mallakar_BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.* *41* Rambo ya shigo cike da Ladabi yace. " Sir g... Gurin zama ya nuna masa Rambo ya zauna jikinsa a sanyaye saboda yanayin da ya ga ogan nasu ya bashi tsoro. Cikin dakakkiyar murya yace." Wannan guy ya bar garin nan ko kuwa."? Rambo yace." E to jiya da na ga gilmarsu a mota shida abokina sun wuce can Titin rimin gata, ina kyauta ta zaton can masaukin sa, yake." Mik'ewa tsaye yayi hade da goya hannunsa a baya, ya kalli Rbow da jajayen idonsa yace." Kaje kazo min dashi, nan." Rambo ya mik'e jiki na rawa ya futa daga d'akin. Shi kuma ya cigaba da kaiwa da kawo wa cikin parlor Rambo da doh-doh sun jima a tsaye suna tattauna maganar kafin Rambo ya shiga mota ya tafi, yanda suka tsara shine baza su biyewa Ogansu ba, zasu yi masa dabara ne kawai saboda suna ganin a yanda yake kan dokin zuciya zai iya kashe guy nan kamar yanda ya fad'a. *Amjad* yafi a wa guda a tsaye a parlor sai kace wani soja, bedroom dinshi ya nufa wayar shi ya dauko ya dawo parlor ya zauna numbar Mimi ya kira yaji wayar a kashe, ranshi a bace ya aje wayar yana tunanin ta yarda zaiyi ya gansu. Minti ashirin a tsakani ya k'ara kiran wayar kamar da wasa aka dauki wayar, Muryar Namiji yaji yana sallama.Amsawa yayi Tare da gyara zaman sa, Ya Aminu a nashi b'angaran ya gane muryar Amjadu da sauri ya gaishe shi, ya amsa babu yabo babu fallasa, yace." Yallab'ai Ashe dai yaran nan da gaske suke yi." Amjadu yace." Menene ? Aminu yayi masa bayanin yadda suka tada hankalinsu ganin wayar a hannunsu. Murmushi yayi yace." Nine na bata domin mu dunga gaisawa, Ya Aminu yace." Allah ya saka da alkairi gaskiya akwai alamun tambaya anan Yallab'ai idan banyi rashin kunya ina so in San cikinsu wacece tayi dace da samun gwarzo miji irin ka." Kai tsaye yace." Dukaninsu nake so zan aura lokaci guda idan zaku bani." Aminu yaji gabansa ya fad'i yace." Yallab'ai a yi haka kuma."? Murmushi yayi yace." Anyi an gama ni dai a gurina saboda haka ina so ka sanar da manya kafin in turo magaba tana a tsai da magana domin baza a ja lokaci me tsayi ba." Yaya Aminu yace." Insha Allahu Yanda kace haka za'ayi mungode sosai da wannan karamcin." Sallama sukayi hade da kashe wayar. ******** Yaya Aminu ya dad'e zaune a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78