Chapter 61
Chapter 61
wane hali yake ciki. Sunkuyar da kansa yayi cikin tawakalli yace." Allah ya kaimu lafiya Jahid ina cikin halin damuwa ina bukatar rarrashin." Kafadunsa ya dafa yana rarrashin sa da kalamai masu sanyi. Amjadu Rambo ya sanya ya je can *Mai takobi* ya karb'o nau'i kan abunci da abun sha, duk ya sanya ya shiga dasu gurin mu, tsabar damuwa da fargaba bata bari munci komai ba, ko da asubah ruwa kawai muka sha fafur abunci yak'i samun shiga a gurin mu, Ya Aminu dama ya tafi gida ni da Umma ne kawai sai granny Ko da muka yi sallahr asubah bamu koma ba, muna zaune daki daya muna jiran hukuncin ubangji, granny na zaune kan dadduma da carbi a hannu Umma na kwance gefan ta. Itama dai carbin ne a hannunta tana ja, cikin damuwa, ni kam ai fad'ar halin damuwar da nake ciki sai a hankali, a Dan baccin da ya kwashe ni ne nayi mafarkin gani ga Mimi a tsaye a wani gurin tana sanye da wasu fararan kaya duk jikinta fuskar ta dauke da wani irin annuri ta kara haske mutuka, hannu nake mik'a mata tana mik'o min NATA hannun tana min murmushi, so nake in kamo hannunta na kasa gani dai a kusa da ita amma na kasa kamo hannunta, gani nayi ta juya da sauri ba tare da tace min komai ba ta fara d'ago min hannunta kafin in Ankara na nema ta na rasa. Ni da kaina na fassarawa kaina wannan mafarkin tabbas Mimi zata yi nisa da rayuwar mu Mimi zata yi nisa damu. Shine fa tunda na tashi na kasa sukuni ina kwance kan wani k'aramin gado nayi lamo wasu irin hawaye masu zafi suna zubo min. ***** K'arfe bakwai dai-dai Jahid ya shigo a sibitin cikin mota ya tadda Amjad yana bacci a zaune ya bashi tausayi mutuka ya kalli su Rambo dake tsaye jikin motar yace."Kar Wanda ya tashe shi Ku k'yale shi ya samu bacci shima Hutu ne. A gurin shi." Gyada kai suka yi alamun sun amsa. Kai tsaye dakin da Mimi take ya nufa, lokacin mu bamu futo ba, shiyasa bamu ga zuwan shi ba, abun mamaki yana shiga dakin yaga nurses tsaye a kanta d'aya na goge mata baki daya na kokarin gyara gadon, yaji dadin yanda ya same ta, gaisawa yayi dasu, suka futa da sauri, shi kuma ya kalli Mimi fuskarsa a sake yace." Madam ya jikin ki."? A hankali tace"Da sauki." Yace." Me kike ji yana miki ciwo a jikin ki." Cikin ta ta nuna da hannunta." Yace." Kiyi hakuri zaji sauki insha Allahu." Mimi ta gyda kanta, gurin yayi shiru na minti biyu dago kanta tayi, cikin sanyin murya tace"Sun kashe shi ko."!!!? Jahid ya girgiza kansa alamar a'a saboda ya San ko wa take nufi.... Bude baki tayi zata yi magana yace." Ko in kira miki shi ne."? Gyada kanta tayi, ya mike da sauri ya futa, lokacin mun futo, muna zaune a wasu kujeru, granny ce ta tare shi tare da fadin"Kai Mujahid ka futo zigwi-zigwi ko kallon mu naka yi ba kun barmu cikin alhini da tashin hankali ko." Jahid shiru yayi mata kawai ya futa. Mik'ewa tayi tana gyara d'aurin zanin ta tace"Ku tashi mu shiga ciki muna da kafafunmu sai anyi mana iso Ku muje muga halin da take ciki baiwar Allah." Aikuwa bayan ta muka bi, ni da Umma. Mimi na zaune kan bed kanta a kasa hawaye na zurarowa a kuncin ta kuka take sosai, muka shiga, da sauri naje na rungume ta, tare da fashewa da kuka INA fadin "Mimi ALLAH ya saka miki dukanin Wanda ya cuce ki." Rungume ni tayi tana kuka sosai. Umma da granny suka k'araso gurin suna rarrashin mu, mussaman ita Mimi din. Zama nayi kusa da ita hannuna cikin NATA, Yanzu zuciya ta tayi sanyi sosai na yarda mafarki karya ne tun daga Mimi zaune a gaba muna magana da ita..... Dakin suka shigo hade da sallama. Tunda nayi masa kallo guda na dauke kaina ina mamakin yanda hallintun sa suka jurkita mutum Dan gaye Dan kwalisa mai kudi mai kyau mai jiji da kansa amma lokaci guda kamanin sa duk sun sauya ya fyade lokaci guda, fuskarsa Tayi fururu, shi kanshi takalimin dake k'afafun shi na wanka ne, kayan jikinsa ne kawai masu kyau. Kai tsaye gurin Mimi ya nufa ya zauna kusa da ita inda bayana da nashi ya kusa haduwa sai nayi saurin mik'ewa daga gurin, na koma kusa da Umma na tsaya, shi da Mimi kallon juna suke yi sun kasa magana shine ma yayi k'arfin halin fadin "Momy ya jikin ki hope yanzu ba kyajin ko wane irin ciwo ko."? Gyada kanta tayi har yanzu hawaye bai daina zuba mata ba. Sosai yake rarrashin ta da kalamai masu dad'i ko kunyar Umma baya ji har sai da yaga ta saki tana dariya sannan ya daina shima ya saki jikinsa sosai ana hira dashi sama-sama shi da Umma granny na sanya musu baki. Kimanin Rabin a wa yayi ya mike tare da fadin zai je gida yayi wanka zai dawo bayan sallahr azahar. Sallama yayi wa su Umma ni bishi da wani mugun kallo na tsana da kyama ji nake bani da babban makiyi a duniya karma shi saboda guy a fiye son kanshi a duniya. ***** Takardar scanning ta futa Dr Jahid ya shiga damuwa sosai da yaga abunda yake faruwa wato baby girl dake cikin Mimi ta juya ma'ana kwanciyar ta ta sauya daga inda ake bukata tana zaune daram! Cikin Mimi gashi cibiyar ta ta nade mata wuyan ta, amma tana rayuwa a haka Cikin hukuncin Allah, lafiyarta lau, cikin ya nuna wata shida da kwana takwas wato ya shiga wata na bakwai duk wasu hallitu ubangiji ya gama abun shi, wahudun kahar Dole ya kwantar da Mimi a asibiti domin kula da cikin ta da ranar haihuwa, domin kar hankalin su ya tashi ya sanya yak'i fada musu abunda yake faruwa ganin yanda duk suka saki jikinsu har shi Amjad din da ya dakatar da komai na rayuwar sa, yanzu ta lafiyar matar sa yake. Ko da ya fada musu maganar bata gado basu kawo komai ba, har shi Amjad din ya yarda saboda Jahid din yace masa yana so Mimi ta samu cikkakiyar kulawa har ta haihu, shiyasa ya yarda da hakan. Kwananmu bakwai a sibitin Mimi ta warware sosai babu inda bata zuwa, domiin Jahid cewa yayi muna futowa da ita tana zurga zurga saboda shi yana gani kafin lokacin haihuwar tata kwanciyar baby ya dawo dai-dai kamar yanda ake so. Ganin ta warware sosai ya sanya na tafi gida saboda makaranta Mimi bata so tafiya ta ba amma da na rarrashe ta na kawo mata misalai sai ta hak'ura. Umma da Granny ne suke jiyyar ta sai Ummansu Munnu dake zuwa kullum tana kawo musu abunci bayan an sha ruwa, duk da cewa Amjadu yana iya bakin kokari su akan su, komai sai ya sanya an kawo musu na ci da bukatar rayuwa. Ni ma ina zuwa amma ba kullum ba, watarana idan muka taso daga makaranta ni da Munnu sai mu wuce aikuwa Mimi tayi ta murna, ranar yini muke ni da Munnu muna sanya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78