Chapter 36
Chapter 36
masa sanyi, sakamakon karatun alk'uranin dake tashi a parlor Granny ta kamo tashar Saudiya tv Jama'a na ta kewaye dakin Allah *(Ka'aba)* zama yayi kusa da ita da carbi a hannunta sai da ta kammala tukkuna ta kalleshi cike da kulawa tace." Iyami ta girki dafaduka shinkafa da daddawa nasan kana son shi, tayi amfani da bussasan kifi yayi dad'i sosai. " Murmushi yayi yace."naji dad'i kuwa domin rabo na da cin abunci me nauyi har na manta. Granny ta mike hade da aje carbin NATA a kan kujera tace." Naga alama kazo kaci ka koshi naga alamun yunwa a tare da kai." Mik'ewa yayi yabi bayan ta, yana 'yar Dariya domin ya kwantar mata da hankali shi kam a irin halin da yake ciki yanzu kome za'a bashi bazai faran ta masa ba Idan ba Asma'u aka bashi ba." ***** Shirye shiryen aure ya kammala duk wani Abu da ake bukata akwai shi a aje idan da kud'in ka ka wuce Matsalar komai, Tun safe su Kawu Yunusa suka yo gayya 'yaya da jikoki suka zo suka kare mana zagi ni da Umma munji bakin ciki da ciwo Abunda suka zo suka yi mana a unguwa amma daga k'arshe muka hak'ura muka cigaba da sabgar mu. Duk Abunda. Amarya take yi nida aunt Hauwa mun sanya Mimi tayi domin me lallai har gida tazo tayi mata ja da baki, aunt ce ta sanya mata man shamfo a kanta, ta had'a kayan gyaran jiki na sanya Mimi a gaba na dinga mulka mata a jiki ina gogewa yinin ranar abunda muka yini kenan, lokaci guda Mimi tayi Wani uban kyau jikinta sai shek'i yake,murmushi kawai take yi ga lallan ta ya futo radau abunka da farar fata. Bayan mun idar da sallahr La'asar ne, muka tafi can yakasai gurin dinki kayamu kala uku duk iri daya dinki iri daya komai iri daya muka karbo a dai-dai muka shiga muka dawo gida sai murna nake Mimi ta saki ranta, Muna Isa gida muka tadda Munnu tazo dakinmu muka shige muka cigaba da tsara yadda zamu gudanar da walima domin lokaci yazo a kurace gobe daurin aure jibi kuma walima kuma a ranar za'a kai Mimi. ***** K'arfe biyar da kwata na ranar alahamis yana zaune a harabar gidan shi jikinsa sanye da kayan motsa jiki Rambo ya shigo cikin gida a mota ya gyara parking ya futo hannunsa rike da ledoji manya manya masu dauke da tambari na sunan company nin sa, karasowa yayi kusa da shi tare da fadin"Sir barka da yamma." Dago kanshi yayi yana kallonsa kana ya amsa, Rambo yace." Komai ya kammala kamar yanda ka Umarta naje har gidansu na kai kayan. " Fuskarsa babu wasa yace." Alhmdullahi ina bunkice da na sanya kayi min." Rbow yace." Mahaifin yarinyar dai kamar yanda aka fad'a talaka ne sosai Dan duk 'yan uwansa sun fi shi rufin asiri yana aikine karkashin company madara ta cowbell bayan rasuwar sa, haka naji daga bakin abokan sana'ar shi ya rasu sanadiyar hatsari a titin sharada mota ta take shi." A hankali yace." Wane company yake wa aiki a lokacin."? Rambo yace." Cowbell ne Sir. Kuma na samu labarin durkushewar company shekaru biyu da suka wuce." Gyada kansa yayi shi bai taba jin sunan company madara wani cowbell ba Niko nace dama yaushe zaka ji tunda k'aramin company k'ananun madara yake kawowa irin ta Leda ta yaku bayi irin 'yar Hamsin a shirin da biyar. Yace." Rambo kasa yara su gyara Wannan gidan nawa na Badawa nasan dai yayi kura sosai a wanke ko ina a tsaftace ka duna kaga inda akwai abunda aje bukata a ciki kayi magana sai a sanya musu, bayan d'aurin aure sai ka kai musu key din gidan." Rambo yace." Insha Allahu za'ayi yanda kace Yallab'ai yanzu za'a sanya yara su fara aiki." Girgiza kansa yayi hade daga masa hannu Rambo ya nufi mota da sauri, shiko Doh! Na bayan shi a tsaye sai zare ido yake. Rambo na kokarin futa da mota ne sai ga motar Hibbah tana kokarin shigowa ciki, Amjad na gane ta ya mike da sauri ya shige cikin gidan domin yana gudun tayi masa shirme gaban ya ransa. Hibbah bata cikin nutsuwar ta tun lokacin da ta samu labarin auran sa take kuka kamar ranta zai futa ta kira wayarsa yafi curin masaki yak'i dauka wani lokacin ma sai taji wayar a kashe, kuka sosai ta sanyawa mahaifin ta, dole ta sanya babu shiri Mai citta ya dinga kiran Amjadu din a waya bai same shi ba, lallaba ta yayi yace." Tayi hakuri insha Allah bata da miji sai Amjad tunda tana sonsa. Gani tayi baza ta iya hak'ura ba ya sanya ta biyo shi har gida. Yana kokarin shiga bedroom d'insa ta fad'o parlor da gudun tsiya taje ta rungume bayansa tana wani irin kuka me shiga zuciya, tace." My Apple Yanzu aure zaka yi ka barni auran ma ka rasa wadda zaka aura sai Mara tushe da Asali wacce ake zargin shegiya ce." Tana kuka take maganar. Fuskar shi a daure ya sanya hannunshi ya jawo ta gaban shi ido ya tsira mata tare da fadin"Waye yace miki matar da zan aura Shegiya CE." Hibbah na kuka tace"A gurin jama'ar gari da gidanan redio." Kara hade fuskar sa yayi yace." Kar in kara jin Kim fad'i haka matar da zan aura tana da asali duk sharrin jama'ar gari ne., cikin kuka Hibbah tace." Nasan duk irin Asalin ta da nasabar ta na fita, ni ya kamata k aura ko don son da nake maka." Zama yayi da ita cikin kujera muryar shi a cunkushe yace."Hibbah bana son wata damuwa a halin da nake ciki, ina me tabbatar miki da cewar duk son da kike min tafi ki nima zan aure tane domin sadaukar wa." Tana kuka tace." Don Allah ka auremu tare, nayi maka alk'awarin zan jiyar dakai dad'i zan kula da kai kamar kwai zan tarairaye ka fiye da tsammani ka, ka taimaka ka aurmu tare." Kallonta yake da rinannun idanunsa yace."Kije ki tambayi Asma'u idan ta amunce shikkenan ko bayan d'aurin auramu da Mimi ne sai mu shirya aure dake." D'ago kanta tayi dake kafadarsa ta rike hannunsa tana murzawa tare da fadin wacece Asma'u." Idanunsa ya lumshe a hankali yac" Tsohuwar budurwa ta CE." Hibbah taji gabanta ya buga daram!!!! Yana nufin tsohuwar budurwar sa zata roka ta sanya shi ya aure ta, lallai da sake shi ko wane irin so yake mata haka, ranta nayi mata suya tace." Shin kana nufin kace da ita itace ta sanya ka auri Wannan din."? Daga kansa yayi alamar Eh. Hibbah ta sunkuyar da kanta tana wani tunani sannan Tace. " zan tambayeta kuma in roketa domin durkusawa wada ba gajiyawa bane indai akan Kane babu abunda bazan yi ba, ka bani numbar ta." Tafad'a tana mik'a masa wayar ta. Karba yayi ya sanya mata numbar Asma'u. Ta maida wayar cikin jakar ta bayan tayi serving numbar. Fuskarsa ta kurawa ido tana kallon dan k'aramin bakinsa idanunsa a lumshe suke yaji kamar ana kallonshi yana bude idonsa ya sauke kan Hibbah ta kura masa ido kamar tsohuwar mayya, mai da idanunsa yayi ya rufe yana jin takaicin ta, a hankali Hibbah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78