Chapter 8
Chapter 8
bakya so sai kije kiyi tayi." Mik'ewa tayi ranta a bace ta fara cire kayan jikinta. Ni ko zama nayi ina duba jikina inda Ya Aminu ya FASA min wani gurin ma har fatar ta kwailaye gefan bakina ya fashe hannu na NASA na shafo jinin , a fili nace " Allah ya Isa Wallahi bazan tab'a YAFE wa, duk abunda nayi ai ba akaina farau ba, ballanta na ma banyi komai ba tunda dai ba kamani a kayi gidan karuwai ba ina zina ko ina cacah,tsabar mugunta da rashin tsoron Allah yayi mutum yawo aikin banza da wofi"!! Da k'arfi na karasa maganar domin ya Aminu yaji na dauka yana gidan, Umma ce ta d'aga labulen dakin tace" Yayi miki kyau! Asma'u wuyan ki ya Isa yanka kiyi ba dai-dai ba kice baza'ayi miki fada ba, lallai kin cika, kuma kin kai munzali Yanzu kin kara tabbatar min da cewar aure kike so bari gobe tayi da kaina zai wanke kafafuna naje gidan Kawun Ku Yunusa muyi magana gwara in aurar dake tun kafin ki jawo min abun kunya." Da sauri na mike na Isa gurin hade da rike mata kakafu ina kuka tare da bata hakuri ina fadin"Umma wai me akace muku nayi a gurun party nan ne, Umma ki lura dani wallahi bazan tab'a zubar da mutumci na ba da kima ta ta 'ya mace, Umma ki yafe min kina kallon yanda Ya Aminu yake duka na kamar zai kashe ni." Umma ta fuzge k'afafunta ta futa daga dakin ba tare da tace komai ba Bakin kofar na zauna ina kuka Mimi tazo ta tsaya a kaina tare da fadin "Bani waya ta,aikin kawai kin karar min da chaji a banza da hotunan ki, kin San ba wuta ake kawo wa ba"Wani irin kallo nayi mata ina gyad'a kai cike da takaici nace" Ki duba wayar ki cikin jakata gata can a tsakar gida. " tsallake ni tayi ta futa, daga dakin. Chaji taje ta kai domin bai zama lallai su kawo mana wuta ba, Ranar ko abuncin dare hanci ba, haka na kwana da cikina tsabar bakin ciki ya hanani bacci sai juyi nake. ***** Kamar yanda ta kwana tana juyi to shima haka ya kwana yana murk'ususu zuciyarsa Sam! Babu dad'i ga uban zazzab'i da ya kwana dashi, ko da asubah ma a daddafe yayi sallah Yana jira gari ya waye musu a can , time din ko wace k'asa daban yake K'arfe Biyar na asubah mun tashi Ya Aminu ne ya tsaya a kanmu har sai da yaga ko wacce ta mike tsaye sannan ya nufi massalaci, motsin Umma Naji a tsakar gida tana alwala da sauri na koma na zauna, domin bana son na futa mu had'u. Mimi ta futa ta barni,, ko minti biyu ba ayi ba kira ya shigo wayar Mimi, daga inda nake in hangowa *Heart beat* sunan da nagi kenan, cikin zafin zuciya na dauki wayar na kashe! A fili nace"Aikin banza da wofi asubar fari za'a damu mutane. " wani kiran ne ya kara shigowa na kashe da sauri,, A'a wani kiran ya kara shigowa na kashe, sai da ya kira sau bakwai ina kashewa, yana kiran na takwas din ne kawai na kashe wayar gaba d'aya. Nashi b'angaran sakato yayi da wayar a hannu lokacin da ya kira suka fad'a masa cewar an kashe wayar ma gaba d'aya, tunani ya shiga yi anya Mimi zata kashe masa waya kuwa? Why!!! Me yake faruwa ne.? Jefar da wayar yayi kan bed ya yunk'ura ya tashi zaune kwalin sigari ya dauko ya bata wuta ya fara fesawa cikinsa hayak'i da sanyi safiyar na, da sauri kuma ya dauko wayar tare da nemo numbar rambow bugu guda tayi ya dauka baki na rawa yace."good morning sir." Bai amsa ba yace." Meye labari ina fatan ka yi aikin da na sanya ka."? Rambow yace." Yes sir Ashe ma ba d'an gari bane yazo bak'unta ne dan barno ne wato mai duguri." Da babbar murya yace."kaje Sanar dashi cewar inji ya bar garin nan kafin in k'araso idan ba haka ba sai da uwarsa ta haifi wani Wallahi. "!!!! Rambo ya tsorata jin furucin oban gidan nasa, ta yaya zai iya zuwa ya fad'awa mutumi haka, amma duk Dan a zauna lafiya yace." Insha Allahu zani yanzu." Kashe wayar yayi yana huci!!! Mimi ta shigo a tsanake ta shimfid'a dadduma ta tayar da sallah, futa nayi daga dakin nima domin dauro alwala. Bayan ta idar Da sallahr ne sai ta dauki wayar kawai ta ganta a kashe alhalin a kunne ta bar ta. Kunnawa tayi tana zargin Asma'u cewar ita ce zata kashe mata waya. Aikuwa ko minti biyar ba ayi ba, kira ya shigo wayar tana dubawa taga *Heartbeat* wani murmushi ta saki had'e da kwanciya kan katifar tana lumshe ido ta d'aga wayar. Tare Da fad'in"Assalamu alaikum." Sama-sama ya amsa murya a kaurare! Yace." Had'a ni da wannan yarinyar." Dai-dai lokacin dana shigo dakin kenan ina jin komai tunda a hands free wayar take.. Cikin tsawa yace." Ko ba kyaji ne."!! Mimi ta tsorata mutuka, muryar ta na rawa tace"Wace yarinyar."? Kai tsaye yace." Asma'u. " jin ya anbaci sunana yasa na zabga tsaki da k'arfi don yaji, aikuwa yaji lokacin da tayi tsaki! Sai ya mike da sauri jikinsa na wata irin tsuma! Kamar Wanda ya sha tsumin 'yan bori ya kwatsawa Mimi tsawa tare Da fad'in "Bata wayar naji ta a kusa dake."!! Ganin yanda yake kurma wata irin tsawa ne yasa na fasa tada sallahr raina a mutukar b'ace na karb'i wayar da take Mik'o min murya sama-sama nace" ta bani wayar meye."!! Tsaye ya mik'e da sauri cikin hargagi yace." Budurwar 'yan daudu yarinya mai aji da kamun kai!! Budurwa me lasisi a jahar kano, duk naga abunda kikayi jiya, ki sani kamar a gabana komai ya faru! Wallahi-wallahi ki kiyayi haduwar mu dake sai kinyi mugun raina kanki!! Ni zaki zubar wa da mutumci...... Katse shi nayi kafin ya k'arasa maganar tashi nima cikin hayaniya nace" Kai!!!! Malam wai me ka dauki kanka ne? Meye ya shafe ka dani? Meye alakar ka dani da kake wannan ihun! To bari kaji naji dad'i da ka gani ka sani jikina ba irin na ko wane lusarin namiji bane irin ka mai aikata sab'on Allah yanzu nayi maka nisa! Kuma tab'a min jiki da kayi kwanakin baya na barka da Allah ehe!!! Ita ma Mimi addu'a nake mata Allah ya tsare ta daga sharrin k........."ShautUp Your dirty mouth."! A zafafe! Tsorata nayi amma saboda taurin kai yasa nace" Ank'iyin shiru d'in duk abunda na fad'a gaskiya ne ai Mtssss." Na buga wani irin tsaki had'e da jefawa Mimi wayar a cinyar ta. Ji nayi yana fad'i" Ok zamu had'u ne zaki San Wanda kike wannan rashin kunya wallahi sai kin maimata min duk abunda kika fad'a kuma, kiyi gaggawar korar wannan mummunar saurayin naki bak'i me kamar alade irin ki, idan ya sake Nazo sai na b'adda shi a duniyar nan."!! Mimi tayi sakato da waya a hannu bayan ya kashe nu kuwa tada sallah ta nayi raina a mugun b'ace! Wani irin tunani take a zuciyar ta, wannan tashin hankali da guy nan yake yi na lafiya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78