Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 76

Chapter 76

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Jahud yace." Granny Amjad yafi k'arfin komai a gurina wallahi." Tace"Yanzu abun damuwar shine ita Asma'u kana ganin ba'a shiga hakkinta ba."? Murmushi yayi yace." Nasan inda zanyi da ita itama baza tasan abunda yake faruwa ba har a d'aura aure zanje cigaba da zuwa gurun ta babu abunda zan FASA, gefe guda kuma zan je na nemi Kawun ta mu kashe magana." Granny tace"Kayi nufin alkairi Allah yayi maka jagora Kai kuma ubangiji Allah ya sanja maka mafi alkairi. " murmushi yayi ya cigaba da driving har ya sauke ta gida ya wuce ofis din mahaifinsa domin ya Sanar dashi abunda ya yanke, to shima bai Wani jayyaya ba tunda dai Shi Jahid din yace ya hak'ura to shi meye bashi sai fatan alkairi yayi yace inda Allah zamu cigaba da shirye-shiryen d'aurin aure kamar yanda muka tsara, Cike da kwaran gwiwa Jahid ya nufi gurin Kawu Yunusa, duk abunda yaje faruwa ya Sanar dashi a bazata Kawu yaji al'amarin dad'i kamar ya kashe shi sai ya dinga shiwa Jahid albarka kamar me."take ya shaidawa 'yan uwansa suka soma shiri amma ya gargadesu da cewar bayaso maganar ta futa har Asma'u taji. Suka ja bakinsu suka yi shiru. Duk wasu shirye-shiryen Jahid ya kammala su dai-dai da kayan da zasu sanya ranar d'aurin aure suna hannunsa hakanan kayan lefe na kece raini da ya yahadawa Asmay an kai kwanaki uku da suka wuce, shi ta b'angaran sa komai ya dai-dai ta. A zahiri ya nunawa Momy nsa ya janye maganar shiyasa ta saki ranta, kuma Mijin ta bai kara tayar mata da maganar ba sai ta yadda da maganar. Saura kwanaki uku d'aurin aure aunt hauwa ta bude mans wuta kullum cikin durkar magani kullum INA kwana da ciwon ciki da wata muguwar Sha'awa Mara fasali sai in sanja pant sau uku a rana, maganar gyaran jiki ba'a cewa komai aunt Hauwa na da abokai iri-iri wata kawarta ce ta tsaya a kanmu ni da Munnu ta hado mana kayan gyara jiki kullum sai munyi dake aunt Hauwa ta iya hadawa sosai take samu a daki muna murje jikinmu bayan mun kama wani irin turare ne mai k'amshin tsiya shima zata sanya mun mulke sako da loko na jikinsu dashi sai munyi a wa daya tukkuna zamu wanke jikinmu tuni wani sihirtaccan kamshi ya kama fatar jikin mu, duk inda muka zauna sai kamshi ni kaina bala'in son k'amshin jikina, kullum muna tare da Jahid a waya, duk wasu k'awayenmu na nesa da na kusa mun gayyace d'aurin auramu, Alina sai wani shishshige min take Sam ban Wani saki jiki da ita ba duk sabgar buki da ita akeyi taki yin zuciya. *Ranar d'aurin aure* Amjad Jahid Khalid Ma'aruf suka futo cikin shiga iri daya shadda CE fara tas dinki babbar Riga da 'yar ciki fad'ar tsadar shaddar bata lokaci ne, takalman su iri daya hulunsu irin daya agogonsu iri daya komai iri daya sukayi amfani dashi kamar yanda suka yi ranar d'aurin auran Amjad da Mimi mota suka shiga guda Khalid ne take draving har suka isa gurin d'aurin auran dake cike makil da jama'a take wani maroki ya saki wata shegiyar gangarsa ya fara wasa Amjad da fadin"Ango Na Asma'u sarauniyar mata gwarozo a cikin maza! Sai Amjadu! Hak'ika Wannan yarinya tayi dace da miji na nunawa sa'a fari mai farar aniya yaro mai halin manya gugan k'arfe sha kwarafniya gaba salamin baya salamun.!!!!!!!!! Jama'ar dake gurin suka dinga mamaki yaya ga ango kuma maroka na wasa abokin ango wai meye yake faruwa ne."! Shi kuwa Amjad Sam! Bai Kawo komai cikin ransa ba, kawai dai yafi tunanin ko don yanayin sunansu daya sa Jahid din yasa marok'an suka kasa ganewa wanene angon a cikinsu. Kawu Yunusa sai kaiwa yake yana kawo wa ya sha babbar rigar shi, kana ganinsa kasan yana Cikin farin ciki, Liman yayi addu'a kamar yanda addini ya tanada Alhaji Isa mahifin Jahid ya mik'a sadaki Asma'u dubu Dari cif kana Liman ya fatiha tare da shafawa duk Wanda ke kusa da Liman a lokacin ya shaida Amjad da Asma'u Aka d'aura aure ba da Mujahid ba kamar yanda suka gani a rubuce a invitation, tofa wani maroki sake kusa da Liman ya kururuce! Fad'i yake." Allah ya tabbatar da Alkairi yau an d'aura Auran Amjad da Asma'u kan sadaki dubu Dari cif ladan ba ajalan ba, tabbas wani kaya sai amale muna rik'on Allah ya sanya alkairi badi iwar haka mu dawo suna." Take guri ya rikice jama'a da dama da su kasan Amjadu din suka rufu a kansa suna yi masa Allah ya sanya alkairi duk ya rikice a lokacin domin al'amarin ya gigita shi kuma yazo masa bazata! Wato abunda Jahid zai masa kenan, yawan jama'ar dake kansa yasa ya nemi su Mujahid din ya rasa, haka dai ya dinga gaisawa da jama'a babu yabo babu fallasa a tare dashi, shi tunani. Yake meye munufar Jahid din akan haka. Kafin kace kwabo 'yan jarida sun rufu a kanshi kowa naso yaji ta bakinsa da kyar ta sub'uce dafa hannunsu ba tare da tace musu komai ba............... Kawai Yunsu da saurn yayyan babanmu suka shigo gidanmu lokacin INA gidan aunt Hauwa mai kunshi nayi mana Dana tunda na tashi nake jin fad'uwar gaba, Kuma ina kallon wani irin kallo da aunt Hauwa take min sai ta gyad'a kanta, Mamakin ko kallon me take min oho, ita aunt hauwa tasan da faruwar abun domin Ya Aminu ya sani shima Kawu Yunusa ne ya fada masa yace masa kuma yayi shiru da bakinsa shine shi kuma ya Sanar da aunt Hauwa din, to dukaninsu sunyi murna da farin ciki sun San Baby Aysha baza tayi maraicin uwa ba. UMMA ta shimfid'a musu ta barma suka zazzauna bayan gaishe-gaishe Kawu Yace." Ga sadakin 'yar kinan Asma'u an d'aura aure." Umma tace"Alhamdullahi Allah ne abun godiya ina yi mata fatan alkairi da samun zaman Lafiya gidan minjinta." Kawu Yunusa yw zakud'a tare da bata fuska yace." Ba da Wanda kike tunani aka d'aura mata aure ba, yarinyar mu Mun d'aura mata aure ne da yaro Dan kirki Wato Amjadu bisa fa yardar shi wancan yaron wato Mujahid mun b'oye muku faruwar al'amarin ne saboda kar Ku kawo mana nakasu a kai saboda haka shi Mujahid din yaga cancantar ya barwa Amjad din Asma'u saboda wasu dalili NASA,saura Wannan karon ma ki zugata ra bujirewa Umarnin mu."!! Yana gama maganar sa ya Mike yana wani baza babbar Riga, take sauran ma suka mike suka futa daga gidan. Suka bar Umma da kudi a hannu tana mamakin Wannan al'amari. *31/11/2019* *BABBAN YARO* *MALLAKAR BINTA UMAR *70* Wannan al'amari ya d'agawa Umma hankali sosai ta inda ta fara tunani. Artabun da zata sha da Asma'u saboda tasan halin taurin kanta da kafiyar ta, Amma itama taji dadin wannan Abu ko babu komai baby Aysha ta samu uwa baza tayi maraici ba. Tanan zaune har jama'a suka fara cika gidan sai ta saki fuskarta ta dinga karb'ar baki. Har lokacin da 'yan d'aurin aure suka shigo Aminu ya shigo gidan da gayyar abokan shi sai fama vedio da hutana suke yi. Dole Umma ts fito aka yi hoton da ita saboda tarihi.Aminu sai washe Baki yake yana gaisawa da

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});