Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Doh_ doh ya fafuri motar da guda! Lokaci guda suka watse amma duk da haka wasu daga cikinsu sai da suka dinga d'aukar motar tashi hoto masu vedio ma nayi kamar bala'i suka bi motar da gudu suna fadin"Yallab'ai me zaka ce a game da jita-jitar da jama'ar gari suke a kanka wai zaka auri shegiya Mara Uba shin hakane ko karya ne, Yallab'ai muna so mu ji ta bakin ka." Ko kallonsu bai yi ballanta su saka ran zai amsa musu motar ta b'acewa ganinsu. Sai da sukayi nisa sosai sannan yace." Doh ka kaini makarantar FCE Yanzu." Doh yace." OK Sir. motar na shiga makarantar samari da 'yan mata suka yi mata Caa! Da ido kasamcewar duk inda motar shi take an Santa saboda tambarin da yake bayanta. Doh.. Yayi parking inda aka tana da kana ya futo da sauri ya bude masa kofar motar. A hankali yace." Ka shiga ciki makarantar ka bunkita min ofis din Muktar Inuwa Gyaranya." Shine ai nihin sunan Kawun Mimi wato Baban su Munnu kenan. Nan da nan doh-doh ya tafi cika umarnin da aka bashi ***** Muna cikin tsananin tashin hankali da rud'u tun lokacin da Umma taji labarin abunda jama'ar gari suke fada a kan Mimi take kuka ta tana fadin"Yarinyar sinna ake shigantawa ni Mariya Innalillahi kuka take sosai tun muna daurewa har muma muka fara taya ta, Ya Aminu ya shigo gidan shima ranshi a bace domin yaga sai Wani irin kallo jama'ar gari suke masa sai kace Wanda yayi sata ko maita Mimi ya kalle ranshi a mutukar bace yace." Kukan karya kike yi Mimi, ko kin dauka auran Wanda ya shahara a duniya wasa ne? Kin dauka in kin auri Young millionaire zaki samu irin kwanciyar hankalin da kike so, to bari kiji auran irin su Sai kayi ta fuskantar kalubale kinga ishara yanzu da Uwar ki da ubanki jama'ar gari suna kiran ki da shegiya, tom me zakice game da wannan zargin da suke miki, ku sani ga 'yan jarida can a waje suna kokarin shigowa cikin gidan nan nine na hana su na rufe kofar gidan da sakata. " Mimi kukan ta ya tsananta ta inda ta fara karkarwa tari ya sark'e ta har tana kokarin kifawa k'irjinta ta rike tam da hannu biyu sai tari take ga hawaye na zuba daga idonta. Hankali a tashe nayi kanta ina kuka wurjajan ina ji kamar in tashi in gaggaura Aminu mari, murya ta a sama nace." Ya Aminu ka k'yaleta mana baka ga tari ya sark'e ta ba."!!!! Ko kallona baiyi ba ya futa daga rumfar a fusace,!! Ni da Umma muka rike ta sosai muna dukan bayan ta duk mun gigice.! Wata irin zufa ce take keto wa Baban su Munnu bayan ya gama sauran maganar da Amjadu yaje masa da ita, to son ya San meye dalilin da yasa Uban Mimi ya gudu ya barta ko zancan da jama'ar gari suke yi gaskiya ne.". Hankali a tashe Baban su Munnu ya fara magana kamar haka. "Hak'ika Aishatu yar halak ce mahaifin ta Dan uwana ne cikin mu daya, mu 'yan kano ne gaba da baya yan Asalin unguwar Gyaranya dake k'aramar hukumar Dala, tun bayan rasuwar Matar shi wato Aisha mahaifiyar Mimi kenan ya ji zaman garin ya ishe shi bayan sadakar ar'abain ya tafi Neman kudi a cewar sa, yau shekara goma sha shida kenan, ban sanya shi a idona ba sai dai labarin sa yana zuwar mana sa'i da lokaci kuma kullum yar shi tana ranshi yana yi mata ake akai akai, Mariya yar mahaifiyar ta Itace ta dauke ta shayar da ita nonota lokacin tana goyon 'yar ta Asma'u sai ta had'a ta shayar dasu tare babu abunda zamu ce da Mariya domin ta cika jajurtacciyar macace. Wannan shine ainihin abunda yake faruwa." Kawu ya k'arashe maganar sa yana goge zufa.!! Shima Nashi b'angaran wani irin faragaba da fad'uwar gaba ne ya riske shi lokacin da ya gama jin abunda Babansu munnu yake fada, hannunshi na rawa ya Ciro hankici daga aljuhunsa ya fara tsane gumin dake saman goshinsa, minti goma babu Wanda yayi magana a cikinsu, da kyar ya bude baki yace." Kana so ka fada mun cewar *Asma'u da Mimi* sun sha nono d'aya kenan."? Kawun su Munnu ya gyada kansa tare da fadin"k'warai kuwa." Amjad ya sauke gwaron numffashi yace." Aurena da Mimi ya haramta idan Asma'u zan aura idan kuma Mimi zan aura aurena da Asma'u ya haramta.!!!!!!! Babansu Munnu ya tsinci kansa da shiga rud'u da fargaba Sam!! Ya manta da wannan k'aulin *Innalillahi wa innailahi raji'un* *K'ak'a k'ara k'ak'a tsara* *13/November/2019* [11/14, 7:52 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *51* Cikin yanayin damuwa Babansu Munnu yace." Wannan abu akwai rikita-rikita a cikinsa akwai daure kai, tunda ake wannan sabgar ban tab'a tunanin wannan alak'ar ba, Babbar magana ce wannan, tsarin na addini islama babu aure a tsakanin mutum biyu sai dai ka dauki daya ka bar d'aya, sun Riga sun tsotsi nono d'aya mutukar ba d'aya ce ta mutu a cikinsu ba, to baka da damar auran 'yar uwarta har abada, amma kasan ko wane ijma'in malamai da nasu k'aulin, Allah ne dai masani." Babansu Munnu ya kare maganar sa cike da tararrabi yanzu idan Amjadu ya zab'i Asma'u ya bar Mimi wand irin hali zata shiga? Watak'ila ma karshen rayuwar ta yazo." Amjadu jikinsa yayi wani irin sanyi tunda yake bai tab'a shiga rud'u da fargaba ba irin na yau, ko mutuwar iyayen sa bai shiga wannan halin ba duk da cewar mutuwar ta girgiza shi sosai wannan yasan dole ce ko wa sai ya d'and'ane ta. Kusan mintuna goma babu Wanda yayi magana a tsakaninsu dukaninsu suna tunanin ya za'ayi su warware Matsalar, Mik'ewa yayi hade da mik'awa Baban su Munnu hannu sukayi sallama, ba tare da yace masa komai ba ya futa daga ofis din. Yana shiga mota ya fara kiran wayar Kawu Yunusa buga daya ya dauka hade da yin sallama kamar zai masa sujjada, saboda kwantar da murya. Yace."Aure tsakanina da Mimi ya haramta saboda sun sha nono d'aya da Asma'u tun farko Asma'u ce zab'i na saboda haka na janye Neman auran Mimi ina rokon Allah ya fe min kuskurana, ita kuma Allah ya bata miji nagari." Kawu Yunusa ya share gumin fuskarsa shima sai yanzu ya tuna da wannan alak'ar mamaki yake sosai me ya hana su tuno da haka sai da magana tayi nisa, idan hakane Ashe Aminu duk abunda yake akan yarinyr babu aure a tsakanin su." "Kawu Yunusa yayi gyaran murya tare da fad'in "Idan ban da ka tsaurara bunkice a kan al'amarin da sai dai muyi ta tafiya a haka domun idanun mu sun rufe akan al'amarin ta inda muka mance da wannan alak'ar saboda haka yanzu zab'i na gare ka, Kaine zaka zab'awa kan ka matar aure cikin su biyun." Ranshi babu dad'i yace." Matar aure tuntuni na zab'e ta Kawu Asma'u

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});