Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yau zanci abunci me gamsarwa domin girki tsaffi daban yake da 'yara." Granny ta sa Dariya domin duk tana jin hirar su tana parlor a zaune. Ni kuwa tun shigowar sa na mike da sauri na bar gurin, Saboda tun kafin ya zauna naga kallon wulakancin da Amjad din yake masa Simi-simi ta Mimi ta hada masa abincin ta bar gurin. Domin itama ta lura da kallon rainin da Amjad din yake masa Sam bata so ayi abun kunya. Mujahid bude ciki yayi yaci abunci sosai suna hira sama-sama, Wanda shi Jahid din ne yafi magana Amjad sai ya ga dama yake amsa masa. Tsaf suka kammala ko wanne ya goge bakin shi da tissue, Mujahid ya kalle shi, cikin nutsuwa yace." K'warai naji dadin dawowar ka wallahi." Gyara fuskarsa yayi yace." Alhamdullahi, nima naji dadin dawowa Cikin nagode K'warai da kulawa Allah ya kara zumunci." Jahid yace." Kar ka damu Aboki duk yiwa kai ne, nima ban sani ba ko akwai ranar da zaka yi min nan gaba." Murmushi Amjad yayi halin Jahid yana burge shi guy akwai saukin kai Sam! Bai dauki duniya komai ba. Mujahid yace." Cikin madam wata uku ne, amma hakikanin gaskiya tana cikin hadari tare da yaron dake cikin ta, domin NASA anyi mata scanning kuma Abu guda yake nuna min. Twins ne daya cikin mahaifa daya bayan mahaifa, to amma kasan ba yadda Allah baya tsara al'amarin shi."" Wani irin shocking jikinsa yayi lokacin da yaji abunda Jahid yake cewa, da sauri yace"Please ka fada min in fahimta Dr akwai k'wayaye na cikin Mimi sai me kuma kace."? Ganin Amjad din ya gigice lokaci guda yasa Jahid din yace." Tabbas hakane amma gurin kwanciyar kowa daban. Ma'ana kowa na da mahaifar shi, kuma d'aya yana zaune a wajen da ba'a so." Wata irin zufa ce ta ke to masa. Take ya ci wata irin fad'uwar gaba ta rikito masa. Baki na rawa yace." Jahid meye abun yi yanzu, Ina son baby's dina duka." Cikin damuwa Jahid din yace." Ka kwantar da hankalin ka, insha Allahu komai zai zo da sauki, aiki kawai za'a yi mata mugani tunda cikin bai yi k'wari ba, sai a cire shi akwai a huta." Jim! Yayi yana tunani yace." Dr babu yadda za'ayi dole sai abunda ka fada." Jahid yace." K'warai kuwa shi ne zamu samu Madam insha Allah Amma tabbas idan cikin jikinta ya kai wata biyar tabbas tana cikin hadari ita da baby." Kamar zai yi kuka yace." OK amma babu abunda zai samu d'ayan ko." ? Murmushi Jahid yayi yace." Babu insha Allah mu fatan nasara muke yi." Amjad duk ya rud'e Allah da ya hallice shi yana da mutukar son yara mussaman Twins shiyasa yanzu duk ya damu, wani irin tausayin Mimi da kaunar ta suka dura a zuciyarsa. Ya manta ma da haushin Mujahid din da yake ji. Nan suka zauna suna tattauna maganar, cike da tausayi da al'ajabi. A nutse na futo ina Jan jakar kayana. Duk suka bini da kallo har shi uban gayyar. Granny tace"ke 'yar nan ina ce ba mun kashe magana ba, ya kuma na ganki da jakar kaya a hannu." Tsayuwa nayi bakin kofa babu yabo babu fallasa nace"Granny kiyi hakuri Don Allah, Umma babu lafiya zanje in kama mata aiki. Dama saboda mijinta baya gari ya sanya na zo, to tunda ya dawo zan tafi." Mimi ta k'araso gurina da sauri ta rike jakar kayan, tana fadin "Me ye haka Habbity."? Tab'e bakina nayi nace" Abunda kika gani sakar min don Allah in tafi gida haka." Rau-rau idonta yayi tace." Please Asma'u wallahi in ina ganin ki cikin gidanan nafi walwala ina jin dad'i don Allah kar ki tafi." Mujahid ne ya k'araso kusa damu ya Dan bata fuskar sa tare da kallona cikin tuhuma yace." Ya muka yi dake."? Marairaice fuska ta nayi cikin sigir shagwaba da han hankali nace."My Jahid please Umma bata ji dad'i ba, zazzab'in nan da ake fama dashi, Yanzu ina shiga daki Ya Aminu ya kira ni a waya Dole ce ta sanya ni tafiya please. " Jakar kayana ya rike yana kallonta kurr! Nasan sigar da nayi magana dashi ne yaja hankalinsa. Murmushi nayi masa nace"Kayi hakuri kullum ai muna tare a waya ko."? Daga kansa yayi kamar wani yaro Karami. Amjadu yana zaune a daining duk yana ganin abunda yake faruwa haushi duk ya k'umshi ganin yanda Mimi take rarrashin Asma'u tana bata hakuri amma tayi buris da ita. Da kuzari a jikinsa ya mike gami da Isa inda suke tsaye, Mimi yazo ya kama ya rungume yana rarrashin, shifa yanzu duk wani Abu da zai b'ata mata rai bai so, sosai yake rarrashin ta. Tace"Hobby kace da ita kar ta tafi." Kallona yayi da Jan ido ko bata fada masa ba yasan abunda zai sanya ta bar gidan Yace."wai ke dole sai da ita zaki iya rayuwa ne? Uhumm! Kinyi aure kina da 'yan kin fita daraja ta ko wane fanni kike zubar da hawaye ki a banza ki daina wannan kuka kina ganin lafiya bata is he ki ba." Jahid ne yayi masa wani irin kallo yace." Kalaman ka sunyi tsauri malam, itama Asma'u ta kusa shiga wannan sahu."!! Yanda Jahid ya fad'i maganar ne ya tabbatar masa da cewar ransa ya b'aci Dariya yayi kad'an Dan ya kara tun zura musu zuciya yace." Ai ba karya bane sai ka bari idan ta hau wannan matakin kayi magana." Ni kam nan tsaya jin karshen maganar sa ba na futa da sauri domin idan na tsaya zuciya ta tana iya mutuwa saboda yadda nake jin bakin cikin bak'aken maganganun da yake tafka min Bayan ta Mujahid ya bi da sauri ba tare da yayi musu sallama ba, wani irin tsaki Amjadu din yaja ya ja hannun Mimi dake kokarin mayar da hawayen ta suka koma parlor Granny tace." Ai yarinyar ma tayi kokari wallahi kam bana ganin laifin ta, ka shigo gida kamar wani mala'ika sai muzurai kake dole taji zaman gidan ya gundure ta." Ba tan ka mata ba ya ja hannun Mimi suka shige dakin shi shi da ita zuciyoyonsu duk babu dad'i Shi kanshi bai so tafiyar yarinyar ba a wannan lokacin Zata d'ebewa Mimi kewa sosai. Mujahid ne ya kaini har gida muka yi sallama dashi cikin so da kauna alk'awari yayi min zai zo a sati nan, sai sa motar shi ta bar gurin na ja jakar kayana na wuce gida Umma na zaune a tsakar gida tana d'aurin kayan miya duk da dare ne amma yara sai shigowa siyan kalanzur suke yi, nayi sallama na gidan. Cike da mamaki take kallona tace"Kece da daddaran nan." ? Zama nayi kusa da ita INA fadin"Wallahi kuwa Umma ya dawo me gidan dama nagani da zama ." tace"Dama ba kyaso a tursasaki." 'Yar dariya nayi tace"Ya jikin Mimi INA fata da sauki kuma tana cin abunci." Jim! Nayi ina tunanin maganar Da Jahid yayi min a mota game da Mimi ni tsoron fadawa Umma nake yi saboda nasan halinta Yanzu zata tada hankalin ta. Kallona tayi tace" Kinyi shuru."? "Umma jikinta da sauki Alhamdulilahi amma Jahid yace." Dole ayi mata aiki fa."! Cikin fad'uwar gaba Umma ta aje farar ledar dake hannunta, tana kallona

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});