Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Jambulo sosai na murtuke fuskata hade da futowa daga motar, Kai tsaye kofar parlor na nufa. Rambo dake tsaye bakin kofar ya bude min ba tare da nace masa komai ba na shiga. Yana zaune a farlor da cup din tae a hannunshi yana kurb'a kad'an-kad'an nayi sallama na shiga, kanshi ya d'aga yana kallonta har ta k'araso ciki sosai. Babu yabo babu fallasa nace." Ina kwana." Shiru yayi yana binta da wani kallo shi ba na tsana ba shi ba na so ba, mugun haushi ya bani ana gaidashi shi kuma yans faman kallon mutane tsaki naja na nufi bedroom din Mimi, wani irin kallo ya bita dashi, wato shi take wa tsaki lallai ne. Cigaba yayi da kurbar tea d'insa hankalinsa kwance. Halin da naga Mimi a ciki ya d'aga min hankali kuma ta bani tausayi mutuka hawaye na fara yi sosai ta rike hannuna tana kuka take fadin "Asma'u ciwo nake ji a gabana na kasa daga k'afafuna." Cike da takaici nace "Mimi kina nufin kice har ya kwanta dake ko d'aga k'afa babu ki gama warware gajiyar biki." Rikeni tayi tana yunk'urin tashi zaune tace." Gashi kuwa kingani Asma'u sau hudu yayi min zafi wallahi."! Naji wani irin bakin ciki cikin zuciyata wai wannan guy wane irin Dan iska ne, budurwa ba bazawara ba, kayi sau hudu sai kace wani bunsuru. Cike da takaici nace"Kinyi ruwan zafi ko."? Gyada kanta tayi tare da fadin"Sau biyu ma nayi. Nace"To yanzu kiran me kike min ne."? "Kawai kizo in ganki." Tafad'a muryar ta na rawa." Ajiyar zuciya na sauke nace." Tom gani shikkenan ko." Rike ni tayi ni kuma ina tunanin taimakon Da zan yi mata Shigowa dakin yayi cikin tafiyar shi ta jarumai ya k'araso kusa damu hannunshi rike da cup din tea dinshi, ya kalleni fuskarsa dauke da murmushi yace." Ina ganin ki had'a mata ruwan zafi ta gasa jikinta sosai tun jiya take kiran ki sunan ki, duk ts hanani sakewa da ita, a matsayin ki na makusanciyar ta, ki tamaka min ki gasa mata jikinta ba sai na dauko dector ba, idan kuma da matsala ta fada miki sai a dauko dector ya duba ta OK." Ji nayi ina nema in kifa daga zaune zantukan shi suka dinga yi min yawo aka wai in hadawa Mimi ruwan zafi jiya tana kiran sunana me yake nufi guy nan ne." Tambayar kaina nake yi babu me bani amsa. Zama tayi kusa da k'afafunta tare da janye bargon dake rufe a jikinta, da sauri na mike na bar gurin jin zuciyata tana wani irin bugawa toilet Din na nufa bana kallon gabana. Tsayuwa nayi cikin toilet din narasa me ma zanyi shikkenan ta tabbata Mimi matar Amjadu tunda gashi har ya kwanta da ita ya raya sunna shikkenan ita dashi sun haramta da junnan su, wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubowa daga idonna jingina nayi jiginayi jikin garo ina wani irin kuka me Sosa zuciya lokacin ji naka yi gwara in mutu in huta da wannan bakin cikin. Motsin bude kofar toilet din naji firgit na dawo hayyacina ina goge fuskata ya shigo toilet din, sauri nayi na juya baya na soma had'a ruwan zafi da na sanyi jikina sai b'ari yake. Bayanta ya k'ura ido da lumsassan idanun sa, kamar na mashaya sarai ya fahimci kuka take yi tunda ya gan hawayen a fuskar ta tana gogewa, murmushi yayi yana shafa siririn sajan shi, a hankali ya k'arasa har inda take, saura kad'an jikinsu ya had'u, gyaran murya yayi tare da fadin "Jimana."! Tun sanda ya iso kusa dani nake addu'ar Neman tsari dama nasan Neman fitina ne ya sanya aka dauko ni a daga gidanmu, fuskata a mugun hade da juyo k'irjina da nasa suka sad'u hakanan fuska ta da tashi ta had'u dogon hancin shi na tab'a goshina, Zame wa nake kokarin yi ya babbake gurin, fuskar shi na kalla da tawa fuskar wacce take a mutukar daure!! Wannan d'an iskan murmushin nasa ya saki tare da tsare ni da fitinanun idanuwan sa, da babu d'igon kunya ko kad'an a cikinsu yace." Kukan me kike yi uhumm."? Wani irin masiffafan fleengs naji yana taso min a lokacin sai na fara addu ar neman tsari daga sharrin shi, cike da jarumta kamar ko da yaushe nace." Ina kuka ne kawai saboda rashin imanin da ka gwada akan Mimi Wallahi baka da Imani."!! 'Yar dariya yayi as'usuel ya shafa sumar shi hade da sajan shi, yace." Wane irin rashin Imani humm? Ko ke na samu haka zanwa tunda hakkina ne kuma sadaki na ne, mallakina ne, yanzu ma na kiraki ne kawai ki gasa min amarya ta, zuwa dare idan ta warware in lallab'ata in kwashi gara yanda ya kamata." Cike da iskanci yayi maganar. Wani irin haushin sa da takaicin sa nake ji a lokacin sai na rasa me zance masa, kawai na buge k'irjinsa da mugun k'arfi na futa daga tsaka insa tare da fad'in"Dan iska kawai." Mamakin ta yake yi wai d'an iska take kiran shi a kan hakkin shi, ya gano kishi tsagwaron sa a idanunta dama so yake ya tunzurata, babu wata damuwa a tare da shi yace." Ni kam babu mahalukin mutumin da zai kirani da wannan Kalmar a kan HAKKINA, kawai Dan nayi marking love da Matata sai a ce min d'an iska, kin ci albarka cin My Wife Mimi na da sai kin gane kuran ki." Yana gama maganar shi ya futa daga toilet din ba tare da ya saurari abunda zata ce ba. Zamewa nayi na zauna dab'as! Kan tayal din dake kasan toilet din na hada kaina da gwiwa ta wani irin kuka ya kufce min Wanda nayi ta kokarin danne shi, kuka nake sosai da sosai ina addu'ar Neman samun sauki daga Allah, wani irin sabon sonshi da kaunar shi naji yana taso min a zuciyata take jikina ya kama rawa duk narasa me zanyi inji dad'i a rayuwa ta. Motsin bude kofar naji na mike zumbur domin na dauka shine ya dawo sai naga Mimi ta shigo tana bin bango, da sauri naje na kama ta, ita kuma ta dinga bin fuskata da kallo bakinta a bushe tace"Habibty kukan kike yi ko." Babu karya domin ga hawaye ne nan tana gani a kwarmin idona nace" Mimi kukan tausayin ki kawai kawai nake yi." Murmushi kawai tayi min tana fyada kanta, ruwan ha hada mata cike wani baho na zuba detol kad'an a hankali na zaunar da ita ciki. Kara ta k'walla ra tana rike hannuna nace" Mimi ki zauna ki Dade a ciki ZAKIJI dad'i jikin ki." Gyda min kai tayi tana rintse idonta, futa nayi daga toilet din na barta. Babu kowa a dakin, na hau cire bedshirt din shina duk ga d'igon jini nan, gashi duk ya cukurkude raina babu dad'i ko na kwabo na cire shi hade da aje shi gefa guda, wani na ciro kai kyau na shimfid'a kan bed din, na Ciro mata kaya masu kyau na aje gefan gado, zama nayi ina jiran futowar ta, Minti ashirin tayi ta futo yanzu tafiyar ta ta sauya ba kamar d'azu ba, na kalleta naga duk ta rame lokaci guda. Zama tayi kusa dani tana fadin,"Kinga yanzu naji dad'i wallahi."

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});