Chapter 12
Chapter 12
ado hade da stons kana ganinsu kasan zasu ja kudi, takalmi me gidan ya tsa ne a k'afafun shi kamfanin Gucci Dan Asali yayi kyau har ya gaji inda kasan wani ango, *Ni ko nace ba dole ba za'a tafi neman aure* fuskarsa babu yabo babu fallasa ya futa, bodyguard d'insa suka mike da sauri, hannu kawai ya daga musu ya karb'i key hannun Doh-doh da kanshi ya futo da motar daga inda take mai gadi ya bude masa gate ya futa daga gidan suna daga masa hannu Kai tsaye gidan granny ya nufa, bai shiga gidan ba sai da ya gabatar da sallahr magariba a massalacin dake manne da gidan sannan ya shiga. Kamilar Dattijuwa na zaune kan dadduma da carbi a hannunta tana lazimi da alama ta idar da sallahr ne, zama yayi a kujera Yana jiran ta kammala, minti goma a tsakani ta shafa addu'ar ta, ta kalle shi bayan ta aje carbi tace"Babban mutum." Kallonta yayi cike da mamaki! Tace"Yau dole in kira ka da wannan suna Wannan kwalliyar ta burge ni sosai don har na fara kishin ka tun kafin kaje inda zaka je." Dariya ya sanya tare da fad'in"Ai kuwa sai da kiyi domin babu abunda zai hanani tafiya Neman aure, auran ma na mata biyu kece ta ukun. Kafin in cika so ta hudun. Hararsa tayi tare da fadin"Mace biyu ai bata kama ce ka ba kaji da guda daya, ta Isa." Yace." Ba kin ce zaki shiga kauyika ki samo min maganin k'arfi ba."? Zama ta gyara tana kallonsa tace"K'warai kuwa yau a can muka yini nida Iyami ga wani sassak'e can na karb'o maka Wanda za'a dafa shi da jar kanwa ya zama shine ruwan shanka, insha Allahu mai maganin yace zaka koma kamar zaki gurin k'arfi." Dariya ya kyalkyale da ita Sam! Ya manta da b'acin ran da yake ciki yace." Toum kinga sai in fara Neman aurena da hujja." Mik'ewa tayi tsakanin ta da Allah take fad'in"Ai mutukar zaka diman ci shan maganin matar ka baza tayi takaici ba." Cikin dariya yace." To kawo min na fara sha yanzu ya bi jikina nasan dai already kin had'a min." Tace"Yanzu kuwa a i mikewar da nayi zan dauko maka ne, NASA Iyami ta k'ukkula maka shi a farar Leda kullum ka dinga shan d'aya." Yace" maza ki kawo min uwargina." Bedroom dinta ta nufa, tana tafiya tana kara tisa maganar. Shi kuwa bayan shigewar ta dariya ya kama yana mamaki wai shi Granny zata bawa maganin k'arfi hummm! Yana zaune ta futo dashi cikin Leda viva sabuwa dal, dauru kusan ashirin ya karb'a yana dubawa, dauri daya ya dauko yana sansanawa, cikin haushi da takaici tace"Meye haka kuma zaka haramtashi fa." Cikin dariya yace." In na haramanta ma ai ni nawa ne kuma ni zan sha." Tace" To fasa dauri daya kasha a gabana." Aikuwa ya fasa hade da zukewa yace." Idan cikina yayi ciwo kece kin yadda." Tace"Na yarda wannan maganin bazai saka ciwon ciki ba sai dai ma ya gyara ka." Yace." Naji to zauna muyi magana dake." Granny ta zauna kusa dashi. Yace." Neman aure zanje fa." Granny tace." Alhamdullahi yau Allah ya kawo ni wannan lokacin. " Gyad'a kansa yayi yace." Mata biyu zan aura ya kika gani. " Shiru tayi tana nazari daga bisani tace"Ai Matsalar Ka ce abun ji." Murmushi yayi yace." Kar kiji komai duk zan iya dasu. B'ata fuska tayi tace"to naji amma dai ta biyun Hafsa ce ko."? Yace."Wacece Hafsa kuma."? Tsaki taja tace"Kamanta kenan kana so ka hadani da Innar ka kenan? Dama suna cewa sai abunda nace dakai kake yi baka zumunci dasu dukiyarka baka Mora musu sai dai su ji a gari." Shiru yayi kawai domin shi kanshi ya San baya kyautawa Sam baya ziyartar dangin mahaifiyar sa, sun gani da korafin sun hak'ura dole yanzu ya gyara ko don kada duniya ta zage shi, Granny ya kalla yace." Yanzu yaya kike so ayi. "? Zama ta gyara tare da fadin" Kaje ka nemi auran Hafsa yarinyar na da kirki kuma tana sonka." Ya mutsa fuskar sa yayi wannan bukatar ta granny baza ta yi wu ba, yace." Kiyi hakuri Granny bana so ayi Abu daga baya azo ana da an sani kin fi kowa sanin halina bana rufa-rufa yarinyar bata yi min ba, zan dai yi kokari gurin ganin naje mun gaisa dasu kuma zanyi musu alkairi sosai." Ajiyar zuciya ta sauke tare da fadin "Shikkenan to Ubangiji Allah yayi maka zab'i na alkairi " "Ameen yace yana kallon agogon dake daure a hannunsa. Mik'ewa yayi yace." Insha Allahu komai ya dai-dai ta zamu je ki ga kawayen naki ko kuma in ce kishiyoyin naki." Tace",Allah ya kaimu yanzu ma ace dasu ina gaishe su." Har ya futa ta bishi a bays hannuta rike da ledar magani tace." Ka manta kuma." Shiru yayi yana nazari,hannu ya mik'a ya karb'a sukayi sallama ta koma gida Mota ya bude ya zura ledar maganin kusa dashi ya zauna sosai hade da kunna motar mai gadi ne ya mik'e da sauri ya bude masa Gate ya futa daga gidan. Kai tsaye,....... Gidansu Asma'u ya nufa. *5/November/2019* [11/6, 5:13 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *Mallakar_BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.* *42* Yana tafe cikin mota yana sauraron wak'ar Joy mutumin shi, gyada kansa yake da alamun Yana jin dadin wak'ar, sai da ya kusa shiga unguwar tasu ne ya kira Mimi a waya, lokacin muna zaune a tsakar gida bayan mun gama cin abunci muna ta fama da wasu shegun cinna ku da suka addabe mu, dama duk lokacin damuna haka suke futowa a gidan ta cikin ramuka suyi ta cizon mu. Wani ne ya cije ni a hannuna ina ta faman sosawa hade da haska gurin da toch din wayar Mimi neman sa nake in kashe, kira naga ya shigo wayar *Heartbeat* abunda na gani kenan, siririn tsaki naja hade da mik'a mata wayar ta karba hade da tashi daga gurin, Umma ta bita da kallo tana girgiza kanta. Minti uku sai ga ta ta futo da wayar a hannu tana sink'e kai Umma tace "Waye ya kira ki harda barin gurin."? A hankali tace" Amajad ne, yazo Umma." Sakin fuska tayi tace" To masha Allahu, alamu sun nuna ke yake so, tunda gashi ya kira ki a waya yazo zance maza je ki shirya Ubangiji Allah ya sanya alkairi." Umma ta k'arashe maganar cike da murna da farin ciki. Mimi ko kunya ta shiga dakinmu da sauri, sai abun ya bani mamaki ganin d'azu take kuka tana cewa ta hak'ura dashi ta barmin amma dubi yanda take rawar kafa saboda zuwan sa. Ni dai shiru nayi kawai, har ta futo Cikin shiri sai zabga kamshi take. Tace"Umma sai na dawo." Umma tace." Ki gaishe shi da kyau kuma ki iya ladabi da biyyaya." Tace"To tana k'okarin futa sai farin ciki take. Hira muke da Umma sama-sama nake jin ta domin a lokacin bana cikin hayyacina wani irin lami bakina yayi sai kace mace mai yaron ciki haka nake jin wata irin kasala da sagewar gwiwa jiki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78