Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 73

Chapter 73

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,222 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mace kamar Mimi sai an tona... Yini yayi yana tunanin Abu d'aya. K'arfe goma na dare dai-dai ya jira granny dake shirin kwanciya, ta dauka suka gaisa Yace. " Granny bani baby Aysha ko tayi bacci ki tashe ta kinji."" Cike da mamaki tace." Wai kai baka da lokacin kiran waya ne sai dare."? Yace." Time din nake da sukuni ki bani sweetheart please."Ya wani marairaice murya. Tsaki yaja tace." Wace baby kuma wacce take gidan kakaninta." Tashi yayi da sauri yace." Me kika CE Granny. "!? Cewa nayi baby na gidan kakanin ta, yo ko tans gurina kana tunanin zan tashe ta daga bacci saboda shirmen ka." Kashe wayar sa yayi ba tare da ya tsaya ya gama sauraron Abunda granny take fada ba. Wayar Asma'u yake kira, busy yau ma tana waya da wani, zuciyar sa kamar tayi bundiga ya jefar da wayar kan bed d'in ya dafe kanshi da duk hannunwan shi biyu. *29/11/2019* *BABBAN YARO* *MALLAKAR_BINTA UMAR* *68* Yafi Rabin a wa a Zaune a gurin sannan ya mike Cikin mutuwar jiki ya shiga toilet alwala ya dauro ya fito yana hada hanya, dadduma ya shimfid'a ya fara sallahr nafila cike da Neman zabin Allah domin shu kanshi al'amarin sa tsoro yake bashi. Komai ya da gule masa lokaci guda, bayan yayi idar ya jima yana rokon Allah ya kawo masa dauki a rayuwar sa, yaji wani sanyi cikin zuciyar sa, kwanciya yayi kan daddumar bacci ya dauke shi mai nauyin gaske. Ni kam bayan mun gama waya da Jahid tunani na fad'a mai tsayi zahiri dai gashi mahaifiyar shi ta nuna bata kaunata karara ko yanzu sai da ya kara fad'a min irin artabun da suke bugawa da ita kan Dole ya janye maganar saboda ta samu labarin kai kud'in da akayi a family lokacin da taje gidan buki suka dinga yi mata Allah ya sanya alkairi, sai abun yayi ta bata mamaki sai daga baya ta fahimta, shine tasa akai kiran sa, ta kare masa tanadi har tana ikirarin zata tsine masa in har bai janye maganar ba, duk yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta na lura Jahid idonshi ya rufe a kaina baya tsoron Abunda zai je ya dawo, dole in Sanar da Umma halin da ake ciki, yanzu jikina ya fara sanyi da al'amarin hak'ika ina son Jahid tsakani da Allah kuma bazan so ya fad'a cikin halaka ba, tunani na gwara ya hak'ura kawai domin ya samu albarka iyaye da wannan tunane-tunanen nayi bacci kwata-kwata na manta da Wani Amjad da damuwar shi. Da safe duk na warware wa Umma abunda yake faruwa tace"Asma'u dama ni tuntuni sai DW nace ki hak'ura da yaron nan tunda uwarsa bata so kika k'i, kuma kin san halin Kawun Ku ba kirki ne dashi Yanzu in wata magana ta sake faruwa zasu har gida su ci mun mutunci ne ki jawo tashin hankali ya kare a kaina da ban ji ba ban gani ba." Shiru nayi wasu zafafan hawaye na zubo min duk ja rasa wane tunani ma zanyi.. Karar waya ta naji a dakinmu da sauri naje na dauko ina duba baby dake bacci cikin kwanciyar hankali, INA dubawa naga jahid din ne ya kira sallama nayi ya amsa murya babu dad'i ya Dora da fadin"Asma'u duk abunda kike ki aje don Allah ki mai da wa da mutumin nan yarinyar shi, wallahi yai shi ya tashe ni daga bacci dama ga shi da kyar na samu ya dauke ina fama da damuwa." Nima cikin damuwa nace"Jahid ka kwantar da hankalin ka dama yau nayi niyyar mai da ita saboda Umma tace a k'yaleta ne yasa saboda sanyi jiya amma insha Allahu yau zan mai da ita Nima na huta da jaraba." Kashe wayar nayi a fusace! Ban saurari maganar shi ba. Hakan ce ta kasance bayan sallahr la'asar Munnu tazo gidanmu nan muka tafi domin mai Da baby kamar yanda nayiwa Jahid din alk'awari munnu tq kalleni cikin damuwa tace"Asma'u fyskar ki ta nuna alamun damuwa tabbas da Abunda yake damun ki."! Girgiza kaina nayi nace"Tabbas Munnu abokin kuka shi ake gayawa mutuwa nan na kwashe duk abunda yake faruwa na fada mata har irin rashin kunyar da nayi Monye Jahid din sai da na fad'a mata. Munnu ta dinga mamaki daga bisani tace"Wallahi wasu masu kud'in haka d'abi'ar su take Sam basa son talaka kiri-kiri ta zo har gida ta ci muku mutumci saboda zubar da girma yanzu kuma idan mukayi aura kuka Tara zuria tace me? Da aure da mutuwa duk na Allah ne mutane ne basa ganewa wallahi." Nace"Ke wace shawara kike gani." Tace"Kawai ki cigaba da nan zabin Allah idan da Rabin auran Ku za'ayi dashi amma ko da wasa kar ki nuna masa kin karaya domun kinga shima yana daurewa gashi saboda ke ya bujerewa mahaifiyar sa." Da wannan zancan muka isa. Babu walwala a tare damu muka shiga, Iyami da Granny na zaune a parlor kamar ko da yaushe ta amsa mana sallama a sake Iyami kuwada saurin ta ta k'araso gurin mu tana fadin "Oyoyo baby kokarin daukar ta take yi nayi saurin kwantota ta dauke ta tana cilla ta sama, yarinyar ta gane ta sai ta fara yi mata dariya. Zama mukayi a nutse muka gaisa da granny dake tambayar mu Umma nace" Tanan k'alau tace ma a gaishe ki da kyau kafin tazo." Granny tace"Ina amsawa nima...Iyami kawo musu abunci." Tafad'a tana kallon Iyami dake wasa da baby Granny ta karb'i baby ta nufi kicin, cikin zuciya ta nace yau kam baza muci abincin gidannan ba wallahi Mik'ewa nayi Munnu ta mike granny ta bimu da kallo tana fad'in"Za'a kawo muku abunci kun mik'e." Nace"A koshe muke Wallahi." Cikin nazari tace" kamar akwai abunda yake samun Ku kun shigo babu walwala kinji sakewa Lamar yanda kuka saba, yake kawai nayi nace"granny kenan babu komai wallahi mu dai mun tafi sai mun sake zagayo wa." Hanyar futa muka nufa Abun kamaer almara babyta fashe da kuka tana d'ago hannun ta! Granny tace"To maza Ku dawo Ku tafi da ita gashinan tana kukan rabuwa da Ku " gaba nayi cikin zuciyata nace yarinyar nan ko kukan me zata yi bai same ni ba wallah" Munnu CE ta koma da baya ni kuwa tuni na fuce da sauri, ina jiyo kukan ta har waje, ko da Munnu taje kin yarda tayi da ita sai kuka take yi Granny tace"Asma'u take nema ba ke ba. iyami ta kwalawa kira tana fadin "Bazan iya da wannan rigimar ba zo ki dauke ta yarinya k'arama da gane mutane." Iyami ta shigo da sauri ta dauke ta tana rarrashin ta, Munnu tace "Asma'u baby ta gane ki sosai wallahi har nayi sha" awar Dadyn ta ya Baki tunda kuna kusa in Allah yayi nufin auran ki da Mujahid." Murmushin takaici nayi nace"Munnu kenan, nasan ko mutuwa zanyi bazai bani ba, kar ki so kiji yanda nake jin zafi a zuciyata jin kukan da take yi." Munnu tace"Allah ya kyauta masa amma gaskiya na lura guy nan ya sanja hali da ba haka yake ba." "Hummm! Munnu kenan dole yayi abunda yake so tunda gonar sa a ka shiga kuma yana ganin ya wuce komai na rayuwa shiyasa." Munnu

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});