Chapter 67
Chapter 67
duk daran dadewa baby zata neme mu." Munnu tace"Ai sai munje har gidan mun ganta wallahi hakkin mu, dole zan hurawa Babanmu waya muje tare." Shuru nayi mata ita kuma ta hau tura hoton baby a wayar ta. ****** Amjadu kuwa ranar da yaje amsa kiran da me girma governor yayi masa basu kwashe da dad'i ba, domin wasu zantukan banza yake masa wai yaga jama'ar gari suna zargin sa kan harda sa hannunsa kan afkuwar abunda ya faru, ya kama rantse-rantse yana fad'in kwata-kwata bai San zancan ba, don haka yayi hakuri kar ya kulle CE shi kuma a matsayin sa na shugaba insha Allah zai sanya a tsaurara bunkice domin gano wadanda suka aikata haka." Kallon shashasha Amjad din yake masa domin ya ma kasa cewa dashi komai kawai ya mike zai bar gurin, governor yadawo dashi, cikin sigar rarrashi yace." Sai magana ta biyu cewar nayi maka alk'awari insha Allah wannan kujerar tawa Kaine zaka maye gurbin ta, tunda na lura jama'ar gari na sonka zamu had'a baki dakai muyi murdiya ga Wanda yaji zab'e zaka tsaya takara a jam'iyya ta, sai milki ya dawo hannuna." Amjad yaji kamar ta kwakwkwad'a masa Mari lallai shaye-shayen da yake yi ya soma tab'a masa kwakwalwa da har yake tunanin dashi zaiyi wannan aiki. Kallon banza Amjad yayi masa yace." Idan ina sha'awar mulki kai! Baka isa ka sanya ni nayi ba, lokacin da zaka ji ni a duk jam'iyyar da nake so zakayi mamaki so wannan Ba damuwar ka bace tawa ce, maganar zaka tsaurara binkice kan mutanan da suka shirya wannan sharri gami da yin izgili ga Allah da manzon sa, wannan bai dame ni ba, saboda ni nasan ko su waye kar ka bawa kanka wahala kuma zan dauki mataki a Kansu."!! Tebur din gaban shi ya buga da k'arfi! Ya mike tsaye hade da fad'in"Na barka lafiya." Futa yayi cikin yanayin tafiyar shi, ta gwarazan maza. Governor ya bishi da kallon mamaki! Wato duk inda yake tsammanin yaron ya wuce nan, lallai su Alhaji Hashimu mai citta sun shirya masa sakiyar da babu ruwa ya tabbata da babu wannan maganar a kasa, zai iya Jan ra'ayin yaron ya karb'i takarar governor kano a jam'iyyar su, domin ya tabbatar Da babu abunda zai hanashi ya lashe zab'e saboda kaunar da jama'ar gari suke masa, shi kuma tanan sai yayi amfani da damar shi, shiru yayi yana tunanin mutukar ya sauka daga kan mulki kashin sa ya bushe zai tabbata bashi da tsunsu bashi da tarko. **** Tsaf ya fito cikin shiri, granny da Iyami na zaune a parlor suna hira, ya k'araso tsakiyar parlorn hannu ya mik'a ya dauki baby dake jikin granny a kwance sai wuntsin-wuntsil take, sama ya d'aga ta kamar yanda ya saba yi mata yana kyalkyala dariya itama na b'angale baki, yafi minti goma yana wasa da yarinyar sannan ya zauna da ita a jikinsa yana fad'in"Baby zanyi missing dinki fa....Granny don Allah Ku shirya mu tafi tare kinji. " cikin shagwaba yayi maganar, granny tace"Kasan Allah babu inda zamu bika kai dai kaje kurrum Allah ya bada sa'a idan ka dawo ma ina so muje muga 'yan uwa Chadi. " yace." Sai dai idan kin yarda mu tafi tare bayan nagama Abunda ya kaini sai mu wuce Chadi din ko ya kika ce." Girgiza Kai tayi tana fad'in"Oh-oh!! Kaje dai ka dawo idan kuma kak'i kaini ai da k'afafuna sai in tafi ka dawo ka tadda bama nan." Yace." Ki Bari zamu je granny nasan halin don girman Allah kar ki d'aukar min Baby kuje wani guri." Tsakaninsa da Allah yake maganar. Granny tace"Ikon Allah!! Yanzu ni kakewa gargad'i kan 'yar ka K'ato! Lallai baka da ta ido!! Dariya yayi ya mike yana fad'in"Granny soyayyar sweetheart dina ta cika min zuciya ta shiyasa idona yake rufewa. " romot din dake kusa da ita ta dauka ta jefe shi dashi, tace"Marakunya kawai, ni kam bana maka fatan samun matsala da duk matar da zaka aura nasan kam Aysha zaka iya sakin ta." Babu wasa a fuskar shi yace." Granny duk wacce zata zauna min da sweet heart lafiya ina maraba da ita, zaman lafiyar mu da ita ta so baby Aysha." Granny da Iyami suka girgiza kai cikin mamaki Iyami ya mik'awa baby din ya kalli agogon dake daure a hannunsa, Cikin nutsuwa yace." Ni zan tafi sai munyi waya ko "? Granny tace" Allah ya kiyaye hanya muna maka fatan alkairi,Iyami ma fatan alkairi take masa ya fuce daga parlor da sauri,baby ta bishi da kallo tana d'aga hannunwan ta, yarinyar sun saba sosai da baban ta. Yana futa su Rambo suka rufa masa baya, kai tsaye airport suka kaishi sai da suka ga tashin jirgin su sannan suka bar gurin. Hade da yi masa fatan dawo wa lafiya. **** Gurin Jahid naji cewar yayi tafiya sai ban nuna komai ba, ko da wasa ban fada masa abunda ya faru tsakanina dashi ba, haka muke tafiya dashi cike da kauna da kulawa kullum kuwa idan ya shiga gaida granny sai ya dauko min picture din baby ya turo min, mu yini muna kallonta ni da Umma. Allah mai iko tsakanin Ya Aminu da Munnu soyayya ce mai k'arfi ta kullu shiyasa ma Munnu ta rage zuwa gidanmu a cewar ta wai kunyar Umma take ji,magar auran su ta kankama inda Baban su Munnu da Kawu Yunusa suka tsaida magana insha Allah wata uku za'a d'aura auransu tunda Ya Aminu ya yarda ta cigaba da makaranta a gidan shi, Kawu Yunusa da kansa yazo gidanmu ya karewa Umma zagi har dani sai da ya had'a ya dinga zaginmu da cin mutumci iri-iri wai tunda na ki auran Amjadu to in fito da miji a hada da Aminu ya fuskanci wannan yaron da yake Neman aurena Mujahid yaudara ta zaiyi tunda gashinan kullum sai yace zai turo magabatan sa a tsaida magana sai yak'i saboda haka inyi maza in futo da miji ko kuma Wallahi ya d'aura min aure da Musa tunda dama tuntuni shine ya fara cewa yana sona." Ranar kuka ns yini ina yi ina samun chaji a waya ta ns kira Jahid din tare da fashe masa da kuka duk na kwashe Abunda yake faruwa na fada masa. Shima babu shiri ya je ya Sanar da mahaifin sa halin da ake ciki. Take Alhaji Auwalu yace." Zai tura akai kud'in aure da sadaki. To ko da Jahid ya samu mahaifiyar sa da maganar tsalle tayi ta dire tace wallahi Sam! Bata yadda yaje ya auro 'yar talakawa ba, domin baza ta tab'a had'a jinita da talakawa masu dattin hula ba, tsaf! Ta sanya akaje akayi mata bunkican su waye su Asma'u kai har gidan su sai Da tasa aka binkito mata. Aikuwa ita da Aminiyar ta suka shirya cikin shiga ta alfarma suka tafi gidan, Baban abunda ya tayar mata da hankali yanda taga wani k'aramin gida kamar akurki wai nan gidan Mujahid dinta zaije ya nemi aure salon ya zubar mata da mutumci da kima a fusace! Suka shiga gidan Momy Mujahid din ns karkada key dinta motar ta cikin izgili Ina sunkuye bakin rijiya ina dauraye hijabai na, Umma kuma na cikin rumfa tana d'aurin sukari hira baby Aysha
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78