Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 69

Chapter 69

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da na mayar mata da martani a rashin sani sai daga baya da ta fad'i cewar itace Momynka sannan naji kunya don Allah kayi hakuri nasan duk zata fada maka abunda ya faru tsakaminmu amma ni abunda nayi mata a rashin sanine." Jahid yaji ya kara kaunar Asma'u yana ganin ba zai iya janye kudirinsa akanta ba zai lallaba Momysa ta hak'ura ta barshi ya aure ta A halin yanzu ita kurrum yake gani yaji sanyi Asma'u tw zame masa wani b'angare na jikinshi, take ya manta da b'acin ran Momyna suka cigaba da hira shi da Asma'u Cikin shaukin so Sam! Ya manta ma cewar a cikin gidan shi yake kuma a patlor Maman Salim zata iya jinshi, Aikuwa tana daki tana tik'ar kukan takaici a zuciyarta tana ji ta tsani Asma'u tunda ta shiga tsakanin ta da mijinta da suka Gina rayuwar su cikin aminci da yardar juna. **** Mujahid ya nunawa Momynsa kamar ya janye maganar auran sa da Asma'u a b'oye kuwa sun hada baki da mahaifin sa, har anje gidan su Asma'u ankai kud'in aure da sadaki lokaci kurrum ake jira kuma kullum suna tare domin shakuwar su ta yanzu tafi ta da waya kullum babu dare babu rana haka suke yi. **** Watan Amjadu Biyu a chana komai ya kammala nan ya wuce Ingila domin can ma akwai bukatar yaje din domin duba company shi da ganin irin cigaban da aka samu. A shkekarar kullum suna tare da granny a waya maganar guda ce Babu Aysha tayi kaza kaza wani lokacin sai dai granny ta kashe wayar ta kyaleshi ko kuma ta kara wayar bakin baby Aysha tayi ta gwalantu shi kuma yana kyalkyala dariya sai Granny ts karb'i wayar sannan zai ce da ita wai tana fad'a masa ne tayi missing d'insa sosai. Granny tsabar haushi sai ta kashe wayar tana fadin'Kai da ita kuka San wannan." **** Muna a dai-dai sahu nida Munnu tace"Ke Wallahi yau sai munje gidan Young millionaire mun dauko baby Aysha ta kwana biyu a hannun mu tunda kince ai mahaifin nata bayanan ko."?Nace " Bayan nan yayi tafiya lallai Munnu ke 'yar rigima ce ni kam babu ruwana Wallahi. " Munnu tace"Ki sa wasa ki gani, mai a dai-dai muje Jambulo." Aikuwa Mai a dai-dai ta ya Karya kwana , nace "Munnu sai dai in ki shiga ke ni kam bazan shiga ba." Tace"Wallahi sai mun shiga tare "Dariya NASA Nace " Zakiyi kaffara kuwa. Muna isa Munnu ta biyashi kudinsa muka tsaya bakin gate din, take masu gadi suka bude mu din ba bakin bane a gidan, Jan hannuna take wai dole sai na shiga ganin kar abun ya zama da zargi yasa na bi bayanta gabana na fad'uwa ni yanzu Sam bana kaunar abunda zai hada ni da guy nan tunda yace s k'yale masa 'yar sa to sai a k'yaleta domin a zauna lafiya. Granny da Iyami na zaune a parlor suna kallon shirin dadin kowa tashar Arewa24 muka yi sallama. Granny ta amsa tana fad'in "Lale maraba da manya baki lallai yau Baby Aysha na da baki domin dai nasan domin ita kuka zo gidanan." Murmushi nayi na zauna Cikin kujera a nutse muka gaisa sosai tace"Shikkenan saboda babu Aisha sai Ku yanke zumunci damu har Umman taku ma ai wallahi bata kyauta ba." Hakuri na dinga bata INA fad'in"Bana samun lokacin zuwa ne saboda makaranta. Granny tace" Yau watan baby Hudu a duniya ace kuna a matsayin iyayenta babu Wanda yazo duba ta ai gaskiya naji haushin wannan Abu." Mu dai hakuri muke bata, sannan muka gaisa da Iyami dake kallon tana dariyar durmarmu d Granny tace"Iyami Kawu musu abunci." Duk da ina jin yunwa sai da nace "Granny a koshe muke Wallahi." Hararata tayi tace"Wato kinanan da halin ki na cutar kai ko? Dubi bakin Ku a bushe kice min a koshe kuke ai nasan daga makaranta kuka dawo." Shiru nayi kawai domin nasan dukanin abunda zan fada Granny ba yarda zata yi ba. Munnu tace"Ina baby Aysha ne? Domin munzo aba mu aronta." Granny tace"Yanzu kuwa tayi bacci wallahi ai kun fi k'arfin abaku Aron ta idan ma kyauta kuka je a baku za'a baku ita kyauta." Munnu tace"Granny da gaske nake wallahi zamuje da ita ta kwana biyu sai mu dawo da ita." Granny tace "Nima ai da gaske nake." Iyami ce ta shigo da k'aton tire cike da nau'ikan abunci da abunsha ta aje kan dogun tebur din da yake gabanmu. Granny tace "Iyami maza hada kayan baby Iyayenta zasu je da ita su ta kwana biyu." Iyami tace"To Hajiya amma fa zamu sha kewa da yawa." Granny tace"Zamu huta da rigima dai kinga zamuyi bacci harda munshari musamman ke." Dariya muka yi harda Iyami ta nufi wani daki da sauri tana fad'in "Baby Aysha rigima kenan. Sosai muka saki jiki muka ci muka koshi mana hira da granny Cikin barkwanci ni kam Allah-Allah nake a fito da baby Aysha na ganta. Aikuwa sai ga Iyami ta fito da ita a kafadar ta daya hannun NATA kuma k'aramin akwatu ne. Ni da Munnu rige-rige karb'ar ta mukayi Allah ya bani sa'a ina karb'ar ta na manna mata kiss a kumatu ina dariya ganin yanda take motsa bakinta tana tsotsar hannunta, da alama yunwa take ji. Granny tace" oh! Oh oh!! Wai meye amfanin abunda kuke yi ne, kuyi ta tsotsar kumatun yarinya shima haka wancan sakaran yake yi, mata har bakinta tsotsa yake." Ni da Munnu muka dariya nace"Ni kam sumbatar kumatun ta kawai nayi granny gaskiya Iyami ta iya raino naji dadin ganin baby Aysha haa duna granny kamar ba bakwai ni ba." Tana dariya tace"Yanzu zata nuna muka halin nata na k'uya Iyami kadai ta sani saboda ita take bata abunci ni kaina wani lokacin sai taga dama take yarda dani." Aikuwa sai ta fara tab'e baki tana so tasa kuka, rungume ta nayi ina rarrashin ta, granny kuwa sai dariya take mana, Iyami ta shigo da fidar ta da sauri ta sanya mata a baki ta kama tana tsotsa sosai, Dan kanta ta cire bakinta sannan ta fara daga hannu wai zataje gurin Iyami aikuwa Munnu tace"Baki isa ba kuwa kin bar hannunta da sauri ta karb'a ta a hannuna ta dauki towel dinta ta goya ta a bayan ta, mik'ewa nayi da sauri Iyami ta mik'o min duk abunda zamu bukata nata, nace "Granny zamu tafi gida." Tace"To Ku gaida min Ummanku da kyau kuce ta kyauta." Nace insha Allah kuwa. "Har waje Iyami ta rako mu tana d'agawa baby hannu ita kuwa sai dariya take bangala mata tana daga bayan Munnu." Ganin rana ta kwalle nace dama zanga su Rambo da sun kaimu gida. Wata zuciyar tace min lallai Asma'u kina da samun shiga. Ni kaina dariya nayiwa kaina. A dai-dai sahu muka shiga nace"Munnu muje gida yau Umma taga baby inyaso sai ki tafi da ita ko."? Munnu tace "Shikkenan muje.""' Wasa nake ma baby daga bayan Munnu ita kuma sai bangale min baki take, nace"Laa Munnu kinga har ta soma hakori wallahi. " Munnu tace"Da gaske ne." Nace sakkota ki gani.' Aikuwa ta fara kokarin saukota tana dubawa, Kuka ta fara yi da alama tafi son goyon nace"Munnu mai da ita

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});