Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fara kuka tukuru ganin yanda Nuffashin Mimi yake hawa da sauka. A dai-dai sahu har kofar gidanmu don haka muna futa muka shiga saboda idanun Jama'a Umma ta rungume Mimi a jikinta hankalinta duk ya tashi mai a dai-dai ya ja mu katafi shi ma hankalinsa ya tashi da ganin abunda yake faruwa ya tausayawa Mimi sosai. Murya a sanyaye Umma tace" Ka kira aunty Ku a waya ka fada mata halin da ake ciki, sannan ka kira Kawunta wato Babansu Munnu." Wayarsa ya futo da ita da sauri. Kai tsaye!! Asibitin zana d'an a dai-dai ta ya sauke mu, Aminu ya sallame shi mu kuma muka taitayi Mimi muka shiga da ita ciki. Har yanzu tarin take idanunta a rufe gaban rigarta duk ya b'aci da jini Wani ma'aikacin gurin ne ya k'araso gurunmu da sauri da wani keke dama mun San ka'idar asubitin Mimi muka Dora kan keken ya ja ta da sauri ya shiga ciki da ita. Tsayuwa muka yi bakin kofa duk jikinmu a sanyaye. Umma tace"WANNAN kukan da kike bashi ne zai bata lafiya ba, addu'a zakiyi mata kawai." Nace"Umma Mimi na bani tausayi haka kurrum zata jawo mana abunda baza mu iya ba." Tace"Itama ba ita ta dorawa kanta ba Allah ne saboda haka sai dai mu bar masa. Yaya Aminu kuwa kai wa yake yana kawowa a filin asibitin idan ka kalli fuskarsa sai ka rantse da bai taba dariya ba tunda uwarshi ta haife shi, shi a ganinsa zuwan guy gidan ne ya dawo da Mimi ciwon ta sabo ta inda har ya tsananta ta fara zubar fa jini dole ya mike tsaye a kan al'amarin domin yana ganin Ana so ayi masa tsakiyar da babu ruwa wani irin haushin guy yake ji da tsanar sa a cikin zuciyarsa K'arfe goma saura sai ga aunt Hauwa ta shigo asubitin hankalinta a tashe take tambayar abunda ya sami Mimi Umma ta dinga fada mata tun farkon al'amarin Jama'ar gidansu Motar Babansu Munnu ce ta shigo asubitin Aminu ya karasa da sauri ya bude masa motar Ya futo tare da Ummansu Munnu da ita Munnu duk babu nutsuwa a tartare dasu. Su k'araso kusa da mu suna gaisawa da Umma jiki duk babu nutsuwa Yace." Ina Aishatu take." ? Dake da haka yake kiranta Umma tace." Tana ciki tun d'azu dector yana dubata." Jin Gina yayi jikin bango yana sauke ajiyar zuciya Mahaifin yarinyar ya tuno da yanda yake kaunarta da irin amanar da ya bashi kafin ya tafi Wanda har yanzu ba a San a wace duniyar yake ba, tun bayan rasuwar mahaifiyar Mimi din yaji duniyar ta isheshi ya hada ina sa ina sa, yayi sallama da 'yan cewar ya tafi Neman kudi tunda ga ranar har yanzu basu sake ganinsa ba amma labari na zuwan musu cewar yana cikin koshin Lafiya, kuma bashi da zance dai na d'iyarsa Aishatu. [11/10, 6:49 AM] Binta U Abbale: Umma da Ummansu Munna zancan suke yi cikin jimami ni da Munnu kuwa babu abunda muke yi sai aukin kuka Kusan awar Mimi daya a ciki sannan wata narse ta futo tace"Waye mahaifin yarinyar nan da aka wo ta yanzu emergency. " Kawu yace." Ganinan." Juyawa tayi tana fadin"Muje dector yana son ganinka ". Dukaninmu sai mukaji kamar mu bi Kawu muji me dector zai ce masa. Kawu da dector ne a ofis a hankali Dr ya cire farin gilashin dake idonsa ya kalli Kawu suka gaisa a mutumce yace." Kaine mahaifin yarinyar nan ko."? Jiki a sanyaye Kawu yace." Nine Dr Allah yasa naji alkairi." Dr ya gyada kansa tare da fadin " I'm sorry to say yarinyar ka tana cikin garari rayuwa domun zuciyar ta ta Riga ta tab'u sakamakon tunani da damuwa da ta sanya a ranta bayan haka kuma da akwai a Abunda take mutukar so Wanda aka hanata shi shine mussababbin ciwon nata idan ba 'ayi gaggawar kwantar mata da hankalin ba, to ana iya rasa ta a ko wane lokaci." Kawu ya share zufa da take tsatstsafo masa a goshi yace." Dr yanzu wane irin taimako za'ayi mana."? Dr ya gyada kansa cikin nazari yace." Taimakon da zan fara yi shine, kuje gida Ku rarrasheta sosai Ku lallame ta tayi kokarin fada muku abunda take so Wanda ta sanya a ranta ya dame ta, idan kun San abun to sai kuyi gaggawar bata shi domin samun zaman lafiya da d'orewar lafiyar ta, bayan haka kuma zan d'aura ta a kan magani insha Allahu mutukar aka bi doka zata samu lafiya, yanzu dai mun dakatar da zubar jinin insha allahu babu matsala." Kawu yace." Insha Allahu komai zai zo cikin sauk'i zamu bi doka zamu kuma zauna da yarinyar domin mu tuntube ta muji meye Matsalar. Dr ya gyda kansa tare da fadin"all right." rubuce-rubece yayi jikin wata takarda ya mik'a masa tare da fadin idan ka futa zaka ga pharmacy sai ka shiga ka siyo wad'annan magungunan insha Allahu, amma ba yau zamu sallame ta ba sai zuwa gobe dole zamu ga dai-dai tuwar numffashinta." Kawu ya karb'i takardar da sauri ya futa. Yana futowa muka mike da sauri dukaninmu tambayar sa muke jikin Mimi "Da sauk'i yake cewa kawai ya nufi dakin magani Aminu ya bishi a baya. Ofis din Dr suka nufa har Aminu Dr Ya kalli Aminu tare da Kawu yace." Wannan fa."? Kawu yace." Shine Wanda zai aure ta." Dr yace." Zauna muyi magana da Kai. " Aminu ya zauna kan kujera jikinsa sanyi k'alau! Dr yace." Kaine kafi kusanci da sosai Kaine zaka fi sanin abunda yake damunta domin sai ta fada maka abunda yake damunta bata fadawa Iyayenta ba, saboda haka Kayi kokarin rarrashinta ta Sanar da kai meye matsalarta domin magance ta kada ka rasa kyakyawar matarka Cikin lokaci kankani."Ya Aminu yayi shiru yana sauraran Dr da abunda yake fada Ba sai yayi masa dogon sharhi ba, yasan kome ye yake damun Mimi bai wuce soyayyar Amjadu ba, Wanda yake ganin a kan ya sadaukar masa da ita gwara Mimi ta mutu in yaso kowa ma yayi asara. Shiru kawai yayi har Dr ya gama maganar shi suka mike da niyyar futa Aminu ya tsaya tare da fadin" Dr babu halin ganinta a yanzu."? Dr ya gyda kansa tare da fadin" ta samu bacci yanzu sai dai gobe insha Allahu da safe sai Ku shiga Ku ganta kafin a sallame Ku." Jiki babu k'wari ya futa daga ofis din. Fuskarsa na kalla naga yayi kucin-kicin gabana ya fad'i nayi saurin kallon Fuskar Kawu nan ma naga babu sauk'i tuni kukana ya tsananta nace"Ku fada mana ko menene k'afafun Babansu Munnu na rike ina kuka. Ummansu Munnu ta janye ni tana rarrashinna ni a lokacin sai nake ganin kamar zasu ce Mimi ta mutu ne Sabuda yanda muka kawo ta a sibitin ta futa daga hayyacin ta. Can gefe guda suka tsaya suna magana. Kawu yace." Aminu ni a iya fahimta ta nafi tunanin Mimi ta sanya soyayyar wannan Yaro da zai auri Asma'u a cikin ranta ne Wanda yake kokarin haifar mata da WANNAN gagarumar Matsalar shine Abunda nake tunani." Aminu ya gyara tsayuwarsa babu sassauci a muryarsa yace." Dama ni tun kafin muzo gaban likita ya fada mana meye na gane komai,

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});