Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 56

Chapter 56

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bayan sallahr isha'i." Umma tace"Ubangji Allah yayi maja jagora mun gode kwarai." Da "Ameen yake amsawa ya futa daga reception din cikin tafiyar shi ta zaratan maza. Yanzu ya samu kwamciyar hankali kuma jakinsa na bashi cewar akwai nasara kan aikin da a kaiwa Mimi fatan shi ta farfado lafiya domin yanzu a zuciyarsa yaji yana yi mata wani sahihin so na gaskiya ga wani mugun tausayin ta da yake ji mussaman idan ya tuno rayuwar ta, ubanta ya gudu ta taso bata San mahaifiyar ta ba, shiyasa kullum yake jinjinawa Ummansu Asma'u uwace ita me baiwa D'a mama a yanda ya fuskanta yanda ta rike Mimi tamkar ita ta haifeta tana kula da ita sosai kular da bata yiwa 'yar cikin ta Asma'u. Aikuwa kamar yanda Dr ya fada bayan sallahr magariba Mimi ta farko kuma sa sunana a bakin ta, take Jahidi ya zo ya kira ni. Ina shiga dakin muka hada ido da ita. Idanunta duk sun kode sunyi ja sosai. Kallona take yi har na karasa kusa da ita gefan bed din na zauna hade da kamo hannunta na rike tamau. Nace"Mimi ya jikin naki."? A hankali tace"Da sauki Habibty kice wa Jahid ya bani ruwa nasha yak'i ya bani. " Mujahid na kalla cikin tuhuma yace." Ba yanzu za'a bata ruwa ba." Hannuna ta rike lebanta duk ya bushe, Mimi tayi mutukar bani tausayi. Nan na zauna ina rarrashin ta, su Umma suka shigo dakin. Tunda ta ganta hankalin ta ya kwanta. Granny kuwa fad'i take"Sannu kinji ko kishiya ta ko wace haihuwa da irin ta sai dai fatan Allah yasa Ku gama lafiya." Dr Jahid futa yayi daga dakin ya barmu da Mimi. Hannuna na nata bacci ya kara dauke ta. Kin tashi nayi daga gurin bare in cire hannuna daga nata har wajan k'arfe goma na dare, Amjadu ya shigo lokacin granny har ta soma gyangyadi. Sallamar sa naji dakin gabana ya fad'i , ciki-ciki na amsa masa, domin Lokacin Umma na toilet aunt Hauwa kuma ta tafi, muryar baban su Munnu na ji sun shigo tare. Amsawa nayi da sauri na juya INA masa barka da zuwa. Kan Mimi ya tsaya cike da tausayi da al'ajabi yake fadin"Ashe Abunda ya faru dake kenan Mimi." Umma dake futowa daga band'aki tace"Sannu da Zuwa." Baban su Munnu ya juya suna gaisawa da Umma. Nan yake jajan ta mata abunda ya faru yana kara addu'a ga Mimi tare da fadin"Sam shi bashi da labarin abunda yake faruwa in banda shi Amjad din ya fada masa a waya. Umma tace"Alkairi shi ake fada bata tashin hankali ba, duk da dai nasan hakkin Ku ne a fada muku munyi laifi." Baban su Munnu yace." Ya wuce yanzu babu Lokacin yin k'orafi ta lafiyar ta Muke ubamgji Allah ya bata lafiya ." Duk wannan abun da ake gogon yana tsaye kusa da kan Mimi ya rutsawa fuskar ta kallo kamar wani maye gani a zaune bayan haka kuma ko kunyar su Umma baya ji. Sallama Baban su Munnu yayi mana ya kama hanya ya futa Amjad din ya bishi a baya Umma kuwa zama tayi kan wata kujera tana fadin"Ni na manta shaf ban sanya kin kira Munnu a waya kin fada mata halin da ake ciki ba, in yaso ita sai ta fadawa Baban nasu." Nace"Wallahi nima na manta shafa."! Granny ce ta bude ido da sauri tana kallanmu ni da Umma tace"Kaddai bacci nayi a gurin nan."? Umma tayi murmushi tare da fadin"Bacci kika yi amma bai yi tsayi ba." Mayafin ta ta gyara tana fadin"Haba shiyasa kamar a mafar ki naji muryar k'ato ya shigo ko." Nida Umma ka kalli juna wanene k'ato kuma."? Kafin muga tunani mu ya shigo dakin hannunsa rike da wasu manya manyan ledoji. Kusa da Umma ya aje ledojin cikin nutsuwa yace." Umma zamu tafi gida. Ga abun bukata nan insha Allahu babu matsala." Umma tace"Godiya muke Ubangiji Allah yayi albarka a rayuwa. " Granny mik'ewa tayi tana wa Umma sallama, shikam tuni ya futa ko kallon inda nake zaune bai yi ba, Kai sai ince tun d'azu da safe da muka hada ido dashi ban kara ganin ya kalleni ba ko da wasa Shige da fucen sa kawai yake. Naji dadin Wannan sauyin da aka samu ta b'angaran shi. Ya daina samun ido zan sake sosai dama idanunsa mugun dafi ne a tattare dani. **** Alhmdullahi Mimi kullum samun sauki take yi yau kwannmu goma a sibiti kuma Alhmdullahi jikinta yayi sauki sosai tunda tana cin abunci Mara nauyi kuma tana zuwa ko INA, kwakwaran motsine dai Dr ya hanata Amjadu kuwa kullum sai yazo shi da granny tare da kayan ciye-ciye hummm mu dake muke jinya maimakon muyi rama muka yi kiba ta sati biyu sosai na ware ganin baya shiga harkata ko yazo gaisuwace take hadani dashi, to shima tunda yaga jikin Mimi yayi sauki baya wani dadewa yake tafiya sabgoginsa, Kullum ina cikin Ac fatata tayi luwai gashi kullum muna tare da Mujahid muna shan soyayarmu ko Amjadu yazo ya tadda mu baya nuna damuwar komai karkari su gaisa ya wuce ciki.ko a fuska baya nuna Alamun wani Abu wai don ya fanni tare da jahid ni ni kaina yanzu tunani sauayrwa shi nace tafarar daya duk wannan rawar kan da yake akaina ya daina yi, ta lafiyar matar shi yake. To nima hakan yayi mun dad'i yanzu zuciyata ta Riga ta tsayar min da Mujahid a matsayin miji maganar mu har gaban su Kawu Yunusa domun da suka zo duba Mimi sun gaisa da Mujahid din a matsayin sa na me Neman aure na. ***** Kwanan Mimi goma sha takwas ta warware sosai ni kuma dama tuni na koma gida saboda makaranta, take Mujahid ya sanya ranar sallamar Mimi tare da tsauraran matakai babu yawan motsa jiki da cin abun mai nauyi babu kar zurga zurga tayi yawa, shima Amjad din banda tsawwala gurin yin sex wannan sune sharadan da Dr ya shimfid'a wa Mimi. Granny itace ta dauki nauyi komai na gidan tunda anyi anyi dani kan na dawo gidan da zama har Mimi ta haihu naki ya Umma ma babu yanda bata yi dani ba, Amjad da kanshi ya turo Jahid gurina wai ya rarrashe ni naje na kula da Mimi fafar naki nace nima makaranta, lokacin mujahid har fushi yayi dani ya daina kirana a waya, kwana uku, nima shareshi nayi na cigaba da sabgata, da yaga Uwar bari ne yazo har inda nake ni kuma a lokacin na butsare masa sai ya dinga bani hakuri muka cigaba da sosyayar mu Cikin aminci da yardar juna. **** Tun da watan azimi ya kama yake zurga-zurga har sai da ya tabbatar komai ya kammala ta fannin company shi sosai ake aiki tare da fidda kaya samfura iri-iri abun sai son barka sosai jama'a suke tsallakowa daga garuruwa suna zuwa d'aukar kaya. Yaduka na mussaman ya sanya company ya shirya masa mai manyan zane ko wane kusan bandur dubu aka futa dashi gidanan yari(prison) bayan nan ya sanya aka futa da bandura na tampopi aka dinga shiga kauyi ka ana rabo, hatta da takalma sai da aka futa dasu aka rabawa mabukata. Farkon wata kenan tsakiyar wata ma haka ne ya kasance, karshen wata

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});