Chapter 41
Chapter 41
suka Isa badawa yayi parking a inda ya saba, kallonta yayi da lumsassun idonsa saurin dauke kanta tayi, ya saki murmushi tare da fadin "Kije ki huta kinji ko gobe ina jiran ki, kiyi min tanadi me kyau." Kofar motar ya bude mata hade da sumbatar hannunta guda, Mimi ta futa a hankali tana d'aga masa hannu, motar yaja ya bar gurin, dake da wutar NEPA a unguwar yasa matasa basu watse ba. Mimi ta tsallaka ta shiga lokonsu cikin sauri Hira muke da su Munnu amma hankalina da tunani na nakan Mimi gamin har k'arfe goma sha biyu saura bata shigo gidan nan ba, Umma ma ta leko dakin kusan sau uku tana tambayar ta shigo, aunt Hauwa ce ta kwantar da hankalin ta, tunda dai tana gurin mijinta,Ni da Munnu hirar muke Mimi ta shigo da sallama, duk muka bita da kallo, 'yar dariya tayi tare da fadin'Meye daga shigowa ta zaku zuba min ido."? Tsaki naja ina d'an hararata nace." Mimi dubi lokaci fa ke ko tsoro bakya ji, bakya ce masa dare yayi." Maryam dake danne-danne a waya tace "Wane irin tsoro tana tare da mijinta." Munnu tace "Nima dai abunda na gani kenan." Tab'e bakina nayi kawai ina kallonta ta tsallako har inda nake zaune k'amshin turaran sa ya buge ni, domin duk jikin Mimi k'amshin masifaffan turaran sa take, d'an rungume ta da yayi, sai naji zuciya babu dad'i wani irin kallo nake mata cike da zargi ina tunanin ko wani Abu ya shiga tsakanin ta dashi, tunda nasan halinsa ba hakuri ne dashi ba, mik'ewa nayi na futa daga dakin domin ji nayi wani irin fleelings na taso min jin k'amshin turaran sa sai na dunga tuno da salon soyayyar shi, Uwar dakin Umma na shifa duk mutane kwance a rumfa na tsallake su, kwanciya nayi kan gadon ta, gefan aunt Hauwa wacce take bacci sosai nasan gajiya ce." Lumshe idona nayi ina addu'ar kar Allah ya dora min tashin sha'awa ta a wannan daran nasan zan shiga mugun hali ga jama'a a gidan. **** Shima bashi bangaran damuwa da tsanani gajiya su suka dame shi, don haka yana shiga part dinshi yayi wanka ya futo parlor ya kwanta kan doguwar kujera lokaci guda bacci ya dauke shi, mai cike da mafarkai bar katai. **** Washe gari da kuncin zuciya na tashi har 'yan buki suka so su gane ganin naki walwala kamar jiya yasa suka dame ni da tambaya dole na sake na cigaba da wurda da mutane kamar yanda na saba. K'arfe bakwai dai-dai motoci sun fi ashirin kofar gidanmu da bakin layinmu duk na d'aukar amarya ne da 'yan uwanta kowa sai da ya samu guri wasu ma basuyi niyyar zuwa ba, mussaman makotanmu amma saboda su kashe kwarkwatar idonsu yasa suka dinga futowa daga gidan jansu su da gayyar 'yayansu suna fadin"Hali Yayi yau Dole suje suga gidan *Young millionaire* Estate din sai da ya kusa cika da mutane sai hauka suke da ihu hade da k'auyanci aikuwa karnuka na rufe a gurinsu suka dinga haushi sosai, saboda ganin sabon Abu. Kowa fadin albarka cin bakinsa yake game da kyau da tsaruwar gidansa ni da Munnu da ita kanta Mimi gidan ba bakonmu bane, saboda haka bamu damu ba, amma dai naga sauye-sauye a parlor ba kamar zuwana na baya ba. Mimi kuka take sosai da sosai ta rirrike Aunt Hauwa wacce take kuka a fakaice,ji nayi idanuna na kokarin kawo ruwa da sauri na fuce daga dakin, Umma kuwa dama kin zuwa tayi domin ba k'aramin artabu aka sha da ita da Mimi ba, tana kuka Mimi na kuka aka futo da ita. Da kyar mutane suka futa daga gidan ko wacce tana jin ina ma itace a cikin gidan Mimi mussaman 'yan matan gurin. Munnu da Mimi kuka suke sosai, naja tsaki tare da fadin"Dallah Munnu ki tashi mu tafi ki rabu da ita." Mimi ta dago kanta tana kallona cikin hawaye take fadin "Haka zaka ce, ko ? Shine kika munafurce ni wato kin San bada ke aka d'aura auranan ba, kukayi min shiru ni yanzu yaya za'ayi na iya rayuwa ba tare dake ba." Kuka take sosai, nace"Haka Allah ya nufa kiyi hakuri mu zamu tafi." Tashi Tayi da gudu taje ta kulle kofar hade da tsayawa jikin kofar tana kuka, ni da Munnu muka bita da kallon mamaki! Nace" zaki bata kwalliyar taki tun kafin angon yazo." Cikin kuka tace"Asma'u baki yi min adalci ba, yanzu ke idan aka ce ki tafi ki barni a gidan nan sai ki tafi ki barni." Dariya ta bani sosai nace"Mimi mata nawa akai wa aure suka zauna su kadai kema kiyu hakuri dama mace 'yar haka CE." Tace"Ni dai na fada miki babu inda zaku je Wallahi." Tun muna d'aukar abun da wasa har mu ka dawo rarrashin Mimi amma kememe ta ki bude mana kofa, agogon dake manne a dakin na kalla k'arfe goma da kwata nace" Mimi dubi lokaci don girman Allah ki bude Mana kofa." Ki tayi, Munnu ta kwanta kan gado tare da fadin""Ki k'yaleta dole idan angon yazo komai abunta mu tafi, gwara mu d'ana gadon amarya." Bude bakina nayi zanyi magana naji muryar shi k'asa kasa yana kiran Mimi da "Momyna" yana kokarin bude kofar. Da sauri na janye ta daga jikin kofar na zaunar da ita kan bed din hade da rufe mata jikinta. Jan kofar yake yana kiran sunanta a hankali na gyara fuskata sosai naje na bude hade da juyawa. Idonshi yayi masa tozali da bayan Asma'u tana tafiya, take yaji yana nema ya fadin saboda abunda ya tsone masa ido, saurin kauda kansa yayi ya shiga dakin sosai hade da rufe kofar, babu yabo babu fallasa ya kalleni tare da fadin"Me ya hana Ku tafiya."? Idona tsaye kanshi yana sanye da jallabiya me ruwan tuka, fuskar shi fayau da ita, nace"Mimi ce ta hana mu tafiya amma tunda kazo zamu tafi yanzu.." Na fada ina kokarin futa, Munnu ta mike ta itama tana YAFE mayafin ta Da wani mugun gudu Mimi tayo kaina hade da rungume ni muka kusa fad'uwa ni da ita kuka take sosai tana fadin"Wallahi babu inda zaki je." Cike da mamaki nake kallonta kuka take haik'an sai naji tausayin ta ya kama ni da gaske murya ta ta karye tana rawa nace"Wai meye haka Mimi wannan abunda kike ba dai-dai bane gaskiya ni sake ni don Allah."! Kin sakina tayi ta cukyukuye min mayafi har d'ankwalin kaina na cire wa yalwatacciyar suman kaina ta bayyana, banyi ki tso ba, tunda aka wanke min kai sai na tattarashi guri guda na Daure da k'aton ribbom. Takaicin ta ya kamani, kokarin nake in janyo mayafina in rufe kaina dashi ganin yanda Yayi tsaye a kanmu hade da kura mana ido, kafin in Ankara mayafin ya fad'i kasa saboda yanda take rikeni rai a bace nace ja Tsaki tare da fadin"Ki sake dallah."!!! Ki Tayi har ilahi yau tana kuka. A hankali ya karasa kusa dasu, ya sanya hannunsa yana kokarin janye Mimi tana kara rungume ni kamar cingum, nima nawa b'angaran kokari nake in kwace kaina mussaman yanda nake jin hucin nuffashin sa kusa dani hade da k'amshin sa, yayi yayi ya janye Mimi taki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78