Chapter 62
Chapter 62
ta motsa jikin ta, kamar yanda Jahid ya fada. Yau sati na guda da barin asibiti Wanda yayi dai-dai da satin Mimi biyu a asibitin kuma yau sallahr saura kwana bakwai sati daya kenan. Ranar juma'a ne na tashi da wani irin mutuwar jiki. Naji bana son zuwa skull din, cikin sauri na shirya jikina na bar gidan, kai tsaye asibitin nasarawa na nufa, duk sunyi mamakin ganina lokacin makaranta nace musu yau baza ni ba, muna tsaka da hira Mimi ta mike ta shiga toilet din dake cikin dakin. Minti biyu naji ta kwalamin kira, da sauri na bude band'akin na shiga ina fadin"Menen..... Kafin in karasa naga jini jazur nabin kasan gurin gata a tsugune ta rike kan famfo na toliet din tana cije bakinta cikin azaba ta rike Cikin nata tana ynukurin tashi tsaye amma ta kasa [11/25, 7:38 AM] BintuUmarAbbale: Hannun ta na rike ina kokarin mikar da ita tsaye abun ya gagara, babban abunda ya bani tsoro da ita shine yanda naga jini na zuba da sauri na fita na kira Umma ta shigo taga halin da ake ciki, itama hankalin ta ya tashi tace"Maza ki karawo Jahid din zubar jini na da matsala futa nayi da sauri kafafuna na rawa, Granny tana tambaya ta menene? Ko juyowa banyi ba, Ina kokarin shiga ofis din ne shi kuma yana kokarin futowa muka buga karo dashi, dauke kaina nayi daga kanshi ina kokarin shigewa, tunda ya ganta a d'amauce ya tabbatar akwai matsala da sauri ya fada dakin da Mimi take, dama zuwan shi kenan asibiti ya tsaya ofis din Jahid domin su gaisa, yana shiga yaga granny tsaye kofar toilet tana fadin"Kama ta Ku futo a hankali, kai amma dai jinin yayi yawa likita yazo ya duba ta." Granny yake kokarin bugewa yana kutsa kai ban dakin inda Umma take kokarin mikar da Mimi ta kasa ko da d'aga k'afarta guda d'aya, da sauri ya mik'awa granny wayoyin shi ya tartare hannun rigar shi, ba tare da damuwar komai ba ya d'auki Mimi hankalin sa duk a tashe ya futo da ita jikinsa duk jini hakanan itama doguwar rigar dake jikinta sharkaf take da jini. Hannunta ta mik'a ta kamo wuyansa tana lumshe ido dishi-dishi take gani. Ya kwantar da ita da sauri ya futa daga dakin, Jahid da Asma'u ya ci karo dasu, sai yayi saurin koma wa dakin, shi kuwa Jahid ganin jikin Amjad din da jini ya tabbatar masa da akwai matsala, aikuwa suna shiga dakin suka tadda Mimi tana wani irin buge-buge kan bed din tana wani cije bakin ta ga idanunta sunyi sama sun k'afe fari tas!! Da su. Innalillahi wa'ina ilahi raji'un " Shine Abunda Jahid ya fad'a ya futa daga dakin da saurin tsiya, mu kuwa rifuwa mukayi kanta Umma addu'a kawai take tofa mata, ni kam baki na ya kulle a lokacin kallon ta nake kurrum tana buge-buge na rasa wane taimako zanyi mata, a takaice ma da naji ina Neman fad'uwa sai na zube a gurin ina fad'in "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un." Amjad hannunta yake kokarin rikewa abun ya faskara domin yau duk k'arfin sa Mimi yafi shi, kokarin fadowa take daga bed din yayi saurin tare ta ta fad'i jikin shi, har ila yau ba daina cije-cije da take ba. Likitoci kusan biyar ne suka rufu a kan Mimi domin ceto rayuwar ta suma sun tsorata da al'amarin kuma yayi musu bazata lallai ubangji Shahidi ne kuma shine yasan gaibu kana taka Allah na tashi, duk iya bunkicen su a kan Mimi bai nuna musu wata alamar na cewa zata yi jijjiga ba, amma dake Allah Allah ne ya saukar da hukuncin sa kan baiwar shi, a war su biyu a kanta suna kokarin shawo kan Matsalar da tsayar da jinin da yake zuba Abu ya fassakara, Wanda a wannan lokacin Mimi ta amsa kiran Ubangji dukanin su sun tsorata mutuka duk da suke likitoci suna ganin irin wannan tashin hankali amma al'amarin Mimi ya girgiza su, Dr Faruk ya lura cikin na na motsi take suka shirya yi mata CS domin a Ciro abunda yake Cikin tunda da ran shi. Jahid daure wa yake akeyin aikin dashi, zuciyar sa nacan tunanin ya za'ayi ya Sanar da Amjadu wannan mummunan labarin. Cikin hukuncin Allah suka samu nasarar ciro baby girl 'yar wattani bakwai ba sati d'aya, yarinyar 'yar mitsitsya da ita, tana cikin koshin lafiya take suka sanya ta Cikin kwalabar su, da aka tana da domin irin su, suka kimtsa gawar Mimi , cike da alhini da tausayi suka futo Da Amjad suka yi karo tsaye a kofar dakin dasu ke, Jahid yaji gaban shi na fad'uwa, hannunsa yaja suka shiga ofis din sa. Amajad yace." Jikina na bani bazan ji alkairi ba daga gare ka, kawai ka fad'a min menene? Domin fuskar ka ta nuna alamun damuwa." Babu wani kwane-kwane da b'oye-b'oye domin dole ya Sanar dashi hakkin shi, yace." Allah yayi wa Mimi rasuw..... Kafin ya karasa ya d'aga masa hannu da saurin! Yace." Kar ka k'arasa min naji."!!!!!!! Jahid ya mike daga inda yake ya zauna kusa dashi da kalamai masu taushi yace." Ubangji shine ya hallice ta a sanda yaso babu tsammani kuma a karb'i abunsa a sanda yaso kar ka manta dani da kai duk zamu je inda Mimi taje komai daran dad'ewa mutuwa riga CE, aya ce ga dukanin wani musulmi Mimi tayi sha hada ta mutu ta farkin haihuwa addu'a zaka yi mata."!! Hannun Jahid ya rike tamau! Leb'anshi na rawa haka zalika jikin shi na wani irin tsuma yace." Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!!!!!!!! Jahid ya dinga dukan kafad'un shi alamun rarrashin yana tausar zuciyarsa da kalamai masu sanyi, d'ago idonsa yayi Wanda suka zama kamar Jan gauta bakin shi na rawa yace." Muje a shirya min gawar Momyna ayi mata suttura."!! Jahid ya mike tare da shi suka futa kai tsaye dakin dasu ke aje gawarwaki suka nufa, tuni an daure Mimi guri guda tana kwance sambal kan wani siririn gado an lullub'e ta da wani farin zani, fuskar ta ya bude, yaga tayi kyau sai murmushi take kamar yayi mata magana ta amsa, zubewa yayi jikin gado yana sakin wani irin kuka. Tare da fad'in"Momyna Allah ya jikan ki, halin ki nagari ya biki, Momyna na hafe miki insha Allahu kece Uwar gida na a aljannar Fiddausi."! Jahid na tsaye yana kallon shi cike da tausayi da alhini, mik'ewa yayi hade da sanya tafukan hannayen shi ya shafe fuskar shi, ya kalli Jahid din a dake yace." Muje." Jahid ya bishi a baya suka futa. Ko da ya shigo dakin da muke bai yadda ya had'a ido da kowa ba yace." Zamu je gida yanzu Jahid ya bamu sallama." Granny da Umma ba yara bane balle maganar sa ta shige su Granny tace"Kai k'ato bana son kumbiya-kumbiya kawai ka fad'a ma kome yi mu 'yan Adam ne zamu dauki kaddara rufewar bata da amfani, shin ya jikin Aishatu ne."? Yana kokarin futa yace." Allah ya amshi ta." Wani irin ihu! Na kurma had'e da bin bayan sa a guje, ina kokarin taddashi tafiyar mu ba d'aya bace ina kuka nake fad'in"Karya kake mugu azzalimi sai dai idan Kaine ka kashe mana ita, idan hakan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78