Chapter 32
Chapter 32
har soro Umma ta raka ta sannan ta dawo cikin gidan. Yana zaune cikin mota ya hango zuwan su, Mimi yake kallo tun daga nesa taci Uwar kwalliya abun ya bashi mamaki sosai, yarinyar Da jiya I Yanzu take kwance magashiyan rai a hannun Allah, amma dubi kamar ba ita ba, abunda bai sani ba shine tunda Mimi taji labarin auransu zai yi wu dashi da ita ta watsake tamkar bata tab'a cuta ba, har suka k'araso gurinsa yana mamakin wannan abu . Murmushi mai k'ayatar wa take sakar masa, Wanda Sam hankalinsa baya kanta yana can gurin Granny wacce take kokarin shiga mota sai mita take masa, yace." Idan zaman gidan ne bai ishe ki ba sai ki koma ai ban ce miki dole ba." Tana daga cikin motar take fadin"Wallahi karshen zamana a wancan gidan yazo domin baza ka aje ni ba sai kace mayya ni daya gida kullum kana gidin matan ka, nima gidan naka Zan dawo ." dariya yasa yana kokarin futowa daga motar yace." Sa ido ne zai kawo ki gidana bana Neman ki." Bude motar yayi ya futa yana jinta tana surutai ya shareta Fuskarshi dauke da murmushi yake kallon Mimi yace." Momyna jiki yayi kyau gashi har anyi min kwalliya mai kyau da burgewa." Mimi ta rufe fuskarta cike da kunya, yace." Kinyi kyau sosai zan so in ta kallon fuskar ki, sai dai Dole zan bar gurin nan saboda idon Jama'a ina fata babu wata matsala ko."? Cike da shauki Mimi tace." Babu wata matsala dama ji nayi zuciyata baza ta iya nutsuwa ba dole sai ta ganka." Murmushi yayi hade da Sosa kansa yace." Momyna kenan nagode sosai da wannan kaunar ina alfahari dake." Mimi ta dinga jin dad'i a zuciyarta yau gata ga masoyinta Amjadu Sam bata so yayi mata sallama ba, taso suyi ta tsayuwa a gurin tana kallon kyakyawar fuskar shi. Sai dai motar tayi nisa har ta daina ganinta sannan ta bar gurin cike da nishadi. ***** Labarin auran *Amjadu Young millionaire* ya baza garin kano da ka bude redio zan can kenan Young millionaire zai yi aure a Sati biyu masu zuwa inda zai auri 'yan gida daya ya da k'anwa jama'ar gari na mamakin wannan Abu, masu bin kwakwkwafi kuwa sai da suka bunkito ko su waye 'yan matan da zai aura hade da bunkice 'yayan wane mai kud'in ne ko kuma mai mulki a jahar kano da sauran garuruwa. Abun mamaki surutun jama'ar gari sai ya karu wannan gayawa wannan 'yan matan da *Amjadu Young millionaire* yake nema da aure 'yayan talakawa ne tilis d'aya ubanta ma ba'asan inda yake ba tun tana jaririya ya gudu ya barta ana zargin ma 'yar shege ce bayan yayi cikin ta ya gudu daga gari, ita kuma d'ayan ubanta ma'aikacin company ne na madara dake Sharada ya mutu bashi da ko kwabo bashi da famsho balle garatuti ya mutu bashi da gidan kansa,sai a company da yayi wa aiki ne suka bar mishi gidan da suka bashi a ro saboda iyalinsa, Duk ana zargin'yan matan da zai aura 'yayan mace ne." Duk cikin jarida ta gaskiya dokin k'arfe Amjadu ya karanta wannan labarin. Zufa ce kawai take keto masa ko ta Ina, wani irin kira ya kwalawa Rambo sai gashi ya shigo farlor da sauri. Jaridar ya mik'a masa muryar shi a sama yace."Kuna ina haka ta faru. "!! ? Rambo ya karb'i Jaridar yana dubawa hannunshi sai rawa yake yi, shima abunda ya gani ya tsorata shi, yasan makiyan sa ne suka shirya wannan Abu domin su tozarta shi, Yace." Sir ka kwantar da hankslinka wannan duk sharrin jama'a ne kar ka manta kana tare da mahassada ko su zasu aikata maka wannan Abu." Mik'ewa yayi yana kai wa da kawo wa a farlor yace." Kaje ka tsaurara bunkice ka gano gaskiyar abun shin abunda na karanta jikin jaridar nan hakane Mimi Bata da uba shegiya ce kamar yanda suka fad'a shin hakane wannan gida dasu ke ciki na company ne kaje ka tsaurara bunkice ka gano wane company mahaifin Asma'u yayi a aiki a sharada." Rambo yace." Insha Allahu Sir ka kwantar da hankalinka duk sharrine domin da d'aga maka hankali kuma a tozarta ka a don duniya. " Wayar shi tayi kara Rambo ya mik'o masa da sauri, kunnenshi ya kara wayar a dake yace." Salamu alaikum. " Kawu Yunsu Ya amsa cike da tashin hankali yace." Yaro mai halin manya na bugo ne in kwantar maka da hankali kan abunda jama'ar gari da kafafan yad'a labarai suke shela a kai, ina so in tabbatar maka da cewar mu 'yar mu Asma'u tsarkakkiya ce da Ubanta kuma muna da nasaba me kyau duk fadin koki da cikarta babu Wanda bai san mahaifinmu Malam Sulaiman mai ishiriniya ba, idan kana so kattabar da haka ka sanya ayi maka bunkice."" Muryar shi a sama yace." Babu bunkice da zan sanya ayi min akan Asma'u na yadda da ita Dari bisa Dari, kokwantona yanzu akan Mimi yake shin da gaske ne mahaifin ta ya gudu ya barta ko kuwa."? Kawu Yunusa yace." Hakane tun bayan haihuwar ta ya gud ..... Katse shi kafin ya karasa yace." Tabbata kenan abunda nake zargi." Kawu Yunusa har yayi niyyar cewa gaskiya ne sai kuma ya fasa tunowa da yayi da maganar Asma'u inda take fadin bata har indai Mimi bata aure shi ba itama baza ta aure shi ba, yayi saurin cewa." Yarinyar 'yar sunna ce sai dai ubanta ya hofintar da ita ne shine mahaifiyar Asma'u ta dauke ta ta raine ta. Amjadu ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin"Yau saura kwana nawa d'aurin aure."? Kawu yace." Kwana shida ne." Shiru na minti biyu sannan yace." Yau muna laraba ko."? Kawu yace.'k'warai kuwa" Yace. "Idan Allah ya kaimu jibi d'aurin aure insha Allahu Ku zauna cikin shiri daga yanzu a fara shiri duk wani Abu da ake bukata kayi min magana kar ka samu damuwa. Kawu yaji wani irin sanyin dad'i ya shiga ransa yace."Insha Allahu komai za a yi kamar yanda kake so Allah ya kara arziki da wadata." Amjad yace." Ameen suma Ameen ina so in zauna da Waliyin ita Mimi domin akwai wasu muhiman tambayoyi da zanyi mishi." Kawu yace." Ai babu damuwa yana aiki ne a babbar makarantar ta PCE nan kofar famfo." Gyada kansa yayi yace." Insha Allah zan same shi a ofis din." Nan suka yi sallama da juna. Wanka ya shiga a gurguje ya kimtsa jikinsa ya futo sai zabga kamshi yake kamar ko da yaushe , fuskar sa a daure ya futa, abun mamaki da daure kai can ya hango 'yan jarida suna rigima da masu gadi gurin wai lallai sai sun shigo Estate din." Mota ya nufa zuciyarsa nayi masa suya wato yanzu za a sanya shi a bakin duniya kenan Saboda ana zargin zai auri Shegiya mata uba, shi yarinyar da suke maganar ta ba su San ba sonta yake ba, kaddara ce kawai auran su, da ita zasu sashi a duniya duk Wanda yayi masa tunon asiri nan bai kyauta masa ba. Ganin shi ya futo yasa suka dinga kokawar shiga cike da b'acin rai yace." Doh doh kayi kamar zaka bi takan 'yan iska da mota." Aikuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78