Chapter 15
Chapter 15
dole ya shafe ni tunda Allah ya nuna min ko wacece ke, kuma kina maganar dan gantaka a tsakanimu idan yanzu babu ita tom nan da kwanaki kad'an zata samu, bana so duniya ta dinga kallon ki a matsayin k'anwar matata wacce ta dauko abun kunya......Ihu!!!! Na kurma da k'arfin gaske ina zuciya ta kamar zata tsage, dukan shi na kama yi kamar wata sabuwar mahaukaciya ina Kuka ina fadin "Allah ya Isa na."!!!! Motar ya tsayar da sauri ganin tana kokarin sauka daga kan titi. Bakina ya matse da k'arfi!!! Muka fara kallon kallo dashi, babu alamun sassauci a fuskarsa yace." Duk abunda na fada gaskiya ne, ga zahiri ne nan na gani, saboda na saba tab'a jikin ki in muka had'u shine kika sanyo k'aramar riga don in gani inyi sha'awa, tab'e bakinsa yayi ya cigaba da cewa"Ko tsirara zakiyi a yanzu bazan sha'awar komai naki ba, saboda kin gama rabawa gayu a titi yanzu sunan ki sorry."!! Ya k'arashe maganar sa hade da Sakar min bakina da ya matse yana shegen murmushin sa da ya saba. Fad'ar tsananin b'acin ran da nake ciki a lokacin b'ata wa ne,raina yayi min bak'ik'ikirin ta inda naji duk a fadin duniyar nan bani da babban makiyi sama da guy nan, tunda nake a rayuta ba a tab'ai min tozarcin irin na yau ba, lallai na yarda ko wane namiji akwai sharrin shi don shi wannan guy ma na rasa a ina zan aje shi, duk inda kake zaton sa ya wuce nan........ *6/November/2019* [11/7, 11:04 AM] BintuUmarAbbale: [11/6, 10:37 PM] .: *BABBAN YARO* *Mallakar_BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.* *43* Wani irin gudu yake da motar kan kwalta, tsoro duk ya kama ni burina kawai in ganni a gida, tun lokacin da yace nayi shiru na rufe bakina domin ina jin tsoron kar ya tsoro da wata futunar. Dai-dai tal'udu yayi parking din motar hade da futa kallonsa nayi ina cikin motar naga ya dauko glass cikin aljihunsa ya sanya a fuskar sa, tsallaka titi yayi ya nufi had'addan gurin abincin nan wato *Mai takobi* ina nan zaune mintuna goma na hango shi, Saurin kauda kaina nayi cikin zuciya nake fadin"Mutum har mutum amma babu kyawun hali Hannunsa rike da ledoji ya shigo motar kujerar baya ya aje ya kunna motar muka tafi Bacci ne ya fara daukata kamar daga sama naji muryar shi yana fadin "Kar ki sake kiyi min bacci a mota" Zumbur na bude idona Da suka fara yin ja.Kauda kansa yayi yana ya mutse fuska. Nima ban sake kallonshi ba, Har yanzu fuskata a hade take tamau! Nayi alk'awarin har in sauka daga motar bazan kara kula shi ba duk abunda yayi min na barshi da Allah. Wayar shi ce tayi kara a lamun ana kira, a hankali ya sanya hannunsa ya dauki wayar da take kusa dani. Ji nayi tsigar jikina ta mike jin hannunshi na tab'a gefan cinya ta. Addu'a ns fara yi a zuciyata ta neman rinjaye. Cikin wani irin voice naji yana fadin"Hibbah!! Wai sau nawa zan fad'a miki ki rabu dani ."! Ban ji abunda tace ba, sai naji ya ja tsaki yana fad'in"Ki jik'a ki sha kayan ki, kwanan nan zanyi aure in huta da bala'in Ku, ko wace 'yar iska ita dai a cita." Kallonsa nayi a fakaice ina mamakinsa cikin zuciyata nace"Zaka aikata abunda yafi haka. Ina jin budurwar tashi tana kaskantar da kanta hade da yi masa magiya, takaici ya she ni, cikin zuciyata nake fadin"Mata yanzu sun koma bin maza har da magiya akan ya so ta wallahi abunda bazan taba iya wa ba kenan. Tsaki ya ja ya kashe mata waya Draving dinshi ya cigaba da hannu daya daya hannun kuma da wayar a hannunsa yana dubawa. K'arfe goma shaura na dare, Aje wayar yayi gefe na, saurin matsawa nayi jin hannunshi ya tab'a ni Haka muka isa unguwar mu, masu sana'oin dake kan layinmu duk sun fara tashi unguwar tsitt!! Gashi duhu dumd'um muna Matsalar wutar NEPA. Parking yayi hade da juyo wa yana kallona. Dauke kaina nayi da sauri! Yace."Kina iya tafiya." Hannu nasa ina kokarin bude kofar Taki bud'ewa, hannunshi ya d'ora kan nawa cikin wani irin salo ya shafa sannan ya bude min kofar Jikina a sanyaye na futa daga motar ina wurga ido domin akwai ni da bala'in tsoro ga unguwar mu da karnukan tsiya gari yayi tsitt ga duhu. Leda guda ya mik'o min cikin ledojin nan yace."_Karb'i ki kaiwa my Wifi bayan haka kice ta kunna wayar ta ina son muyi hira." Share shi nayi ina kokarin tsallaka titi. Sunana naji ya ambata *Asma'u* kin ji yuwa nayi na wuce da sauri! Wani kare ne yayo kaina da gudu, yana haushi. Ihu!! Na sanya na dawo da baya ina haki! Dariya yayi ya bude motar ya futo Karan ya kara haushi da k'arfi! A hankali yace." Wannan bakin hijab din na jikin ki shiyasa yake miki haushi. Cikin tsoro na kalle shi, nasan bala'in karan nan bashi da sabo. Yace." Ni zan tafi ki San yanda kika yi kika wuce gida,ko kuma ki kira saurayin ki. Muryata na rawa nace"Motar ai zata shiga lugun don Allah in shiga ka kai ni Girgiza kansa yayi hade da bude murfin motar ya shiga. Shahada nayi na kara yunk'urin tsallaka titin a karo na biyu Cikin fusata karan yayo kaina. Da sauri na koma baya kamar wata zarrariya na dunga dukan motar ina fadin bude min don Allah. Sauke glass din motar yayi yace." Meye wai! Kiyi tafiyar ki ki k'yale ni." Hawaye suka zubo min nace." Nasan wancan karan bashi da mutumci kuma bashi da sabo Wallahi zai iya cizo na, kwanaki da ya ciji wani sai mutuwa yayi don dafi ya zuba masa " Cikin k'osawa yace."Tom yanzu ya kike so ayi."? "Ka taimake ni, wani in ya ganni anan ba zai min kyakyawar fahimta ba." Wani kallo ya watsa min tare da fadin"Au ke kina jira jama'ar gari suyi miki kyakyawar fahimta. " Shiru nayi Yace." Ki cire wannan a ran ki." Kunna motar yayi zai tafi, da sauri na bude na shiga ciki Kallona yake cike da mamaki yace." Meye haka? Kin damu in kawo gida na kawo ki, kin hanani tafiya." Karyar da kaina nayi cike da tausayin kaina nace"Ka taimake ni." Hannunshi na kama na rike gam!! B'ata fuska yayi tare da fadin "Wane irin taimako zan miki. Kai tsaye! Nace" Ka raka ni gida wallahi karan can bazai Bari in wuce ba." Tausayi ta bashi amma bai nuna ba yace."gaskiya bazan iya shiga lokon can ba, kawai kiyi tafiyar ki,ko kuma ki cire hijab din jikin ki ki yar. Nasan saboda hijan din ya Hana ki wuce wa, da zaki gane ma kawai ki daina sanyawa domin mugun muni yake saki." Wani irin. Kallon nayi masa nace"In cire hijab dina fa kace." Gyada kansa yayi tare da kanne min ido daya yace." Meye a ciki to bayan babu kowa a unguwar idan ma da mutane ai abun ba sabo bane a gurin su, tunda duk kin raba musu. Naji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78