Chapter 13
Chapter 13
babu k'wari na shige dakinmu hade da fadawa kan katifa ruf da ciki rumtse idona nayi sam zuciya ta babu dad'i ni kadai nasan abunda yake damuna. Parking yayi bakin hanya hade da kunna Fitilar wayar sa, unguwar duhu dumd'um!! Sai hasken masu ababen siyarwa dake kan hanya, masu charge masu wanki da guga, masu provision da sauran su, yaji dadin haka domin baya son ya futo har jama'a suka gane shi, wayar Mimi ya kira hade da fada mata gashinan ya iso. Lokacin tana kan hanya. Inda ya Saba parking ta nufa cikin yanayin tafiyar ta tsallaka titi tayi ta isa kusa da motar hade da d'an kwankwasa wa, a hankali ya bude motar tare da haske fuskar ta da wayar hannunshi, sakin Fuska yayi yace." Momy na tafi ta kowa." Mimi tayi wani fari da ido. Yace." Shigo ciki mana." Cike da kunya ta shiga motar ya mai da murfin ya rufe. Kashe ta yake da kallonsa na goggun 'yan duniya, sunkuyar da kanta take tana fadin"Sonka zai iya kashe ni." Cikin zuciyar ta tayi maganar Yace." Bamu gaisa ba Momyna kunyar ki na bani mamaki tana d'aya daga cikin abunda yasa naji kin kwanta min a raina" Mimi tayi murmushi yace." Ok ni ne yafi kamata na gaishe ki tunda nine danki. Kinga kuwa dole in nemi albarka." 'Yar dariya tayi sai kace sokuwa, tace"Ina wuni"? Cikin sangarta yace." Umum!! Nine zan fara gaishe ki." Mimi taji kamar tana yawo kan gaji mare don shauki gaskiya guy nan ya iya love. Yace." Ya jin dadin ki Monyna hope komai lafiya Lou." "Alhmdullahi wallahi." Tafad'a fuskarta dauke da murmushi "Ina *Asma'u?* ya tambaye ta kai tsaye!!! Wata irin fad'uwar gaba taji jin ya baci sunan Asma'u. Bakinta na rawa tace" Tana gida." "Owk d'azu mun Dade da yayan Ku a waya ina fatan duk kunji sak'ona ni Amajadu zan aure ku dake da 'yar uwarki Asma'u." Gyada kanta tayi tace"Ya fada ma Umma." "Masha Allah." Ya fada da murmushi a fuskar sa, shiru na minti biyu sannan yayi gyaran murya tare da fadin" Shikkenan kije gida sai munyi waya, sai ki kira min *Asma'u* itama muyi zance kamar yanda mukayi dake." Jiki babu k'wari Mimi ta bude mota ta futa, ya bita da kallo had'e da fadin "Kar ki manta fa ki kashe wayar ki, kafin in kwanta ina son jin muryar ki." Mimi taji wani sanyi ya tsirga mata a zuciyarta murmushi ta saki tare da fadin"Insha Allah." Hannu ya d'aga mata ta tsallaka titi kana ta shiga layin su. Umma na zaune a inda take tace"Har ya tafi."? Mimi tace"A'a Asma'u yace." A kira masa." Umma tayi shiru cike da mamaki tace." Asma'u Kuma. " daga Kai Mimi tayi. Ina kwance a dakin ina jinsu sama-sama, domin bacci ya soma hawa kaina. Ina jin sanda Umma take fadin "Sai kije ki kira ta tana daki." Mimi ta shigo dakin hade da tsayawa a kaina tana kiran sunana. Banza nayi mata. Tace" nasan dai kina ji don yanzu ba lokacin baccin ki bane, kije Amjadu yana kiran ki." Mik'ewa zaune nayi nace"Uwar me zanyi masa." Tace"Idan kinje sai kiji." Yanda ta fad'i maganar na gane taji zafin zagin da nayi. Tsaki nayi na koma na kwanta. Tace.don Allah ki tashi kije babu kyau wulakanci." Ina daga kwance nace"Kin San Allah Mimi babu inda zanje domin ban ga tsiyar da zan masa ba. Futa tayi daga dakin. Can naji Umma na kwala min kira. Mik'ewa nayi da sauri na futo tsakar gidan INA amsawa Fuskarta a hade tace "kije kiran da ake miki ko ranki ya b'aci." Shiru nayi raina a bace Cikin tsawa tace." Ko bakya ji ne." Nace" Tom Umma" dakin mu na koma na zurmo hijabina na sallah na futo silafas na zura a kafata na futa. Tsayuwa nayi a waje ina tunanin ko in lab'e a wani gurin ne. ? Wata zuciyar tace" kije ki kare masa rashin mutumci tunda yazo unguwar Ku. Aikuwa tafiya nayi inda nasan zan ganshi Can na hango motar shi kasancewar ya kunna futular motar. Ina zuwa gurin na buga motar da k'arfi. Budewa yayi hade da haske fuskata da hasken wayar shi, kalon-kalon muka fara ni dashi. Gani nayi ya kauda kansa yana dariya Haushi da takaici suka kama ni, sai kace mahaukaciya ya tasa ni a gaba yana dariya. Cike da takaici naja tsaki hade da juyawa da niyyar tafiya, ji nayi an fuzgo min hijabi da k'arfi na fada cikin motar. Jikinshi ya kwanto kaina ya rufe motar hade da sanya mata security, kallonshi nake a tsorace! Naga fuskarsa a mutukar murtuke Yayi bala'in shan kunu irin Wanda bai tab'a yin irinsa ba, Ya hasko fuskata sosai da wayar shi, Yana kallona tare da ya mutse fuskar sa. Kauda kaina nake ganin yadda ya dallare min ido. Hannunsa guda ya sanya ya shak'o wuyana dake cikin hijabi, Murya k'asa-k'asa yace." Maimata irin zagin da kikayi min a waya jiya." Kifkifta idona kawai nake, ya k'ara shak'e min wuyana hade da d'aga kaina sama sosai, yace"Ko bakya ji ne."? Da kyar na samu na kakaro magana nace"Sakar mun wuya kar ka kashe ni." Kin saki yayi sai ma kara damk'e wuyan yayi, hannuna guda na sa ina kokarin b'anb'are hannunsa daga jikin wuyana, ko motsi ya kiyi, wuyana yayi bala'in sagewa, nace"Ka Sakar min wuyan....... Ka tsani Yayi ta hanyar fad'in" Ki maimata irin zagin da kikayi min jiya Zan sake ki." Babu wasa a cikin maganar sa. Hawaye na ziraro min nace"Wane irin zagi nayi maka, duk abunda na fada maka gaskiya na fada ciki babu sharri ko kashe ni zakayi sai dai ka kashe ni." "Very good."!! Ya fad'a yana k'ara bank'are min wuyana sama, cike da mugunta, yace." Na lura da abunda kike so in yi miki ni kuma bazan yi ba, na daina hora ki da abun domin na lura yana miki dad'i shiyasa kike bukatar haduwar mu, Yanzu zanyi miki horo ne irin na gidan prison. " Kasa magana nayi saboda yadda naji mak'o gwarona ya bushe, Hannu ya sanya ya cire hijab din jikina, na rintse idona saboda nasan babu rigar arziki a jikina wata vest ce mai kama jiki sosai kuma iya kacin ta cibiya ta, domin nayi shirin bacci Mimi ta tashe ni shine kawai na zura hijab din a kai. Miskilin murmushi ya saki tare da cije lips d'insa yace" Surprise!" Wato dama kin tawo da shirin ki kenan ko."? Shiru nayi masa wasu zafafan hawaye na zubo min a Kumatuna. Murmushi yayi had'e da shafa sajan shi yace."Wannan karon baza ki samu abunda kike so ba, domin na fara nisanta kaina dake, sai kije gurin wannan saurayin naki mai kama da alade,sai Yayi miki wasa dasu." Shashshekar kukana ce ta fara futowa fili ina mugun Jin ciwon rashin mutumcin da yake min. Muryarsa a kaurare! Yace." Wancan karon kin min lafi nace ki bani hakuri kink'i OK wannan karon ki bani hakuri ko kuma in dauki mata ki nag gaba a kanki." Cikin shashashekar kuka nace"Babu hakurin da zan baka tunda banga laifin da nayi maka, ba, kuma bak'i mai kama da alade da kake magana a kansa gwara min shi sau dubu a kanka, Allah ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78