Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta karba ta sha kadan. Nace "ki kwanta kiyi bacci zakiji sassauci. Kwanciya tayi tana lumshe idonta Sai dana ga bacci ya dauke ta sannan nima na kwanta ina sak'e-sak'e Cikin zuciyata. Bacci ya soma fuzgata naji kiran waya *haetbeat* tsaki naja na dauki wayar na kashe gaba d'ayan ta domin shi nake mutukar jin haushi a ganina duk shine ya jawo mana wannan masifar. Tun farko da bai nunawa Mimi yana sonta ba, ina ganin duk haka baza ta faru ba. Da tune-tune bacci b'arawo ya kwashe ni. ****** B'angaran Amjadu kuwa, tun bayan da Wakilansa suka zo suka Sanar masa da cewar An bashi guda cikin 'yan Matan da yake so ya aura sai gaban shi ya fad'i ya tunini ko Mimi ce, shine dalilin da yasa ya tambaye su kud'in wacce a ka karb'a a cikinsu nan Kawunsa yace." *Asma'u* yaji dadin haka don haka kafin su tafi sai da yayi musu kyauta ta mussaman. Shirye-shiryen bude company ya kammala yau saura kwana biyu gari ya dauka kafufin yad'a labarai in ka bude zancan kenan *Ranar Juma'a Biyu ga watan bakwai za'a bude shaharrarn company nan wato AmjaduAbulAbbas materials* za'ayi bononza a ranar abun dubu daya Dari biya abun dubu goma dubi biyar. Mutanan gari sun kunzige kudinsu suna jiran ranar domin su je su kwaso garab'asa. *** Washe gari muka tashi da jiki a sanyaye Mimi ta rame lokaci guda, shi ko Ya Aminu dama tunda Kawu Yunusa ya Sanar dashi cewar an fasa karb'ar kud'in Mimi ya watsake ko da ya tashi da safe tamkar Wanda bai yi ciwo ba, yanzu Mimi CE abun tausayi so ya tasa ta a gaba. Da kyar na rarrashe ta ta Karya kummalo Umma ta tsaya bakin kofar mu tana fadin "Menene wai naji kuna takkadama."? Zuciyata tace kawai ki fadawa Umma ko menene ko Allah zai sanya ta fahimta." Kaina a kasa nace"Umma ina ganin wa....Shiru nayi na kasa magana. Umma tace." Meye kika yi shiru."? Bakina na rawa nace"Umma don Allah Ya Aminu ya janye kudirin sa a kan Mimi akwai cutar wa a ciki, ya kamata Mimi a bata zabin zuciyarta Ya Aminu Namiji ne shi zai iya jure komai kinga Mimi ko yarinya ce mai karanci shekaru gata kuma mace." Shiru Umma tayi tana nazarin magana ta. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace"Kin yi gaskiya Asma'u ni ma zuciyata batayi na'am da haka ba, saboda ina gudun zagin jama'ar gari tunda duk sun San komai Da Aminu da ke da Mimi duk daya kuke a gurina babu Wanda zan ce nafi so, amma kina ji da bakin ki tace ta amunce da Aminu kuma ko jiya Kawun Ku ya maimata min maganar babu gudu babu ja da baya tunda sunyi magana da mahaifin ta a waya yace ya bashi wuka da nama, Babansu Munnu ma har dashi cikin maganar kin ga bani da ta cewa." Nace "Umma kina da ta cewa mana don Allah ki sanya Ya Aminu ya janye magana.....kafin in karasa naji saukar Mari a kuncina Ya Aminu ne tsaye a kaina yana wani irin huci! Yace." Kina so naci ubanki Asma'u, wato kina zu ga Umma kina zuga Mimi kan su bujirewa Bukatata ko me? Ni kinsan halin da Zan shiga idan na rasa ta, ko kinsan irin son da nake mata, mutukar ina Raye a duniyar nan bani da mata sai Mimi, dake da ita kuje kuyi abunda zakuyi akin gama ya Riga ya gama." Yana gama maganar shi ya fuce daga gidan a fusace! Umma barin gurin tayi ni da Mimi mukayi shuru muna sak'e-sak'e A hankali naji tace"Asma'u don Allah kar ki kara wata magana kan al'amarin nan, kinji tunda dai kince zaki taya ni addu'a tom na gode miki.". Murya na rawa take maganar Nima naji zuciyata ta karye nace"Mimi sai dai idan gani nayi am d'aura muku aure da Aminu shine zan daina magana domin nasan ki nayi a banza ne, bakin alkami ya bushe, amma magana kan al'amarin yanzu na fara." Shiru tayi tans kallona. Mik'ewa nayi na futa daga dakin zuciya nayi min zafi! *RANA BATA KARYA* Manyan attajirai da manya manyan 'yan boko 'yan siyasa masu mak'ami daban-daban Sarkin Kano sarkin Zazzau Sarki Katsina Jama'ar gari tsakunsu da kwarkatar su, sun hallara a wannan guri. Hayaniya ce ta tsananta tare Da jiniya wannan ya tabbatar min da cewa me girma governor ne ya iso bani kadai ba, duk wani Wanda yasan da akwai dabi tsakanin *Amjadu* da me girma *Governor* sai da yayi mamaki, tuni jama'ar gari suka fara ihu!! Suna fadin abunda ransu yake so ga me girma governor. Ko kunya babu me girma governor ya futo daga mota tare da jamarsa ya dinga ratsa jama'a Yana daga musu hannu hade da washe musu baki wai shi lallai ga governor tsagerun matasa masu goyon bayan Amjadu suka sanya ihu!! Da dariya suna fadin abun da yayi musu kan governor din, wasu na fadin"Ba mayi!!!! Sai da 'yan sanda suka tsawa tar sannan hayaniyar ta lafafa, can gurin da aka tanadar wa manyan baki governor ya nufa, police na biye dashi a baya domin sun tsorata da irin ihun da jama'ar gari sukeyi, Sai da suka ga ya zauna sannan suka koma gefe suka tsaya da bundigun su a hannu. Can na hango Mai citta shida abokanan shi, sai zare ido suke. Limamin babban massalacin jama'a na garin kano ne ya tashi ya bude taro da addu'a yayi karatun alkur'ani me girma sannan daya baya daya manya baki suka fara jawabi kowa yana yaba kwazo da jajircewa irin ta Amajdu 'Yan jarida a gurin baza su kirgu ba, domin wasu jamar gari na gida kowa na gaban TV Wanda bashi dashi kuma kunne shi mak'ale da waya ko redio yana saurara. Lokacin da Amjadu ya futo zai yi Jawabi Ihu!! Jama'ar gari suka sanya tare da fadin"Sai kayi fari me farar aniya ka iya ka huta *AmjaduAbulAbas* muna biye da kai insha Allahu *2004* taka ce sai ka zama shugabanmu." Ihu! Kawai suke, sun hana aji bayanin da yake, da kyar jami'an tsaro suka shawo Kansu suka yi shiru. *Amjadu* yayi jawabi me gamsarwa jawabin da ya ratsa zukatan al'umma Su Kansu manyan gurin sun jinjina masa kuma sunyi masa fatan alkairi.mai Martaba Sarki yaji dad'i sosai da samun hazikin Yaro a garin shi yana mutukar alfahiri da shi. K'arfe goma sha biyu da rabi taro ya watse saboda ranar juma'a ce za'a tafi massalaci, nan Amjadu ya bada sanarwar cewa jamar gari suje massalaci su dawo bayan an idar da sallahr za'a bude company daga nan har zuwa goma na dare. Haka akayi kuwa bayan an sakko jama'a sukayi ta tururwa company suna kwasar garabasa.Sai k'arfe daya na dare sannan aka samu saukin Jama'a. ***** Duk abunda yake faruwa a gari muna da labarin shi munji a redio Kuma mun gani a TV dake ranar sun bar mana wuta, abun mamaki Mimi yini tayi tana farin ciki. Amjadu ya sha addu'a gurin Umma, aunty Hauwa ma ba abar ta a baya ba, kusan a dai-dai ta sahu guda tayo da kayan da bata koma gidan ta ba sai bayan sallahr Isha'i. Ni ko tunda nayi masa kallon farko a TV ban sake

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});