Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 39

Chapter 39

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta zame masa ranar bakin cikinsa Asma'u ta cuce shi, bai ta tunanin zai fada rudani na so irin wannan ba.dole yayi kokarin sa Mimi cikin zuciyar sa, ko don ya haddasa Asma'u ciwan zuciya kamar yadda take kokarin haddasa masa, wannan itace shawarar da ya yanke. **** Mimi ta dawo fuskar ta cike da walwala da farin ciki, tace"Asma'u yace." Mu shirya bayan sallah magariba zai turo a dauke mu akwai walima da a bokanshi suka hada masa, da har nace ko in baki wayar Ku gaisa yace A'a in k'yale ki." 'Yan dakin suka kwashe da dariya tare da fad'in"Haka kurrum yana jin zakin muryar ki, zaki had'a shi da masifaffiya mai saurin baki, mai zai fuskanta ya burgini da ya gwale ki." Dariya suka kwashe da ita har Mimi din, wani irin b'acin rai ne ya kamani lokaci guda, ganin yanda suke min dariya sai naga kamar da gayya suke yi min har ita Mimi din, raina ya b'aci mutuka, Mimi tace. A bani wayar yace baya bukata lallai ma guy nan, cikin jin haushin su nace banzaye 'yan iska kawai baku da aiki sai iskanci da dariya Ko wacce ta rasa mashinshini don Allah a daure ayi aure ko kwa rage zumudi da tsiyayar da kuke yi." Ihu!! Suka sanya kamar wasu shashasha, Maryam tace"Dallah malama yi mana shiru ke akwai wacce ta fiki zuba, daga an fara zancan aure zaki hau lumshe ido idonki har ja yake yi "yar iska, hahahahaha " ta k'arashe maganar tana dariya Tare da bawa ta kusa da ita hannu suka tafa tsaki naja me k'arfi nace "Kanku a keji, kun dai ji Abunda Mimi tace ko, gaskiya Ku kintsa sosai bana son shirme a gurin ku zama manyan baby's kar Ku bani kunya shegu." Munnu tace"Dole ne ai nasan gurin zai had'a had'addan Samari gaskiya Dariya muka kwashe da ita nace"Munnu ta Shamsu kenan" Hararata tayi, ni ko na cigaba da shiryawa ta ina mata dariya, aunt Hauwa ce ta lek'o dakin tare da kiran Mimi hannunta taja suka futa, nace"Mimi yau kin bannu a gurin aunt Hauwa. **** K'arfe takwas dai-dai gurin Walima ya k'ayatu, nan cikin Estate din aka shirya komai guri Tasha decoration, haske ko ta ina ga wasu shegun kujeru an ajiye guda biyu na ango da amarya ne, su uku ne kacal cikin Estate din, Ma'aruf Mujahid Hafiz sai Amjadu din, dukanin su ma'aikata ne, Hafiz yana aiki a babban banki najeria, shi kuma Ma'auruf yana aiki a babban Asibiti na nasarawa Mujahid yana aiki a Company d'angote cement shine manager dukaninsu suna da aure da yara biyu Hafiz ne me D'a d'aya tunda shi bai jima da yin auran ba, sai Amjad da yayi aure yanzu, suna zama na fahimtar juna a tsakaninsu, kasamcewar su Ma'aikata yasa basa haduwa sosai sai weak end suke had'uwa su gaisa da junansu sai kuma lokacin azimi suke shan ruwa tare, yau idan an sha ruwa gidan wannan gobe a sha gidan wancan, Amjad sai dai yaje domin shi bashi da matar ma, sunyi ciwon baki har sun gaji, Matar Hafiz me suna Samina ita ce ta dinga nanika masa k'anwar ta yana basarwa da ta lura ba auran zaiyi ba kawai sai ta hak'ura, amma dukaninsu sun yi mamaki da suka ji labarin auran sa katsaham! Shine suka shirya masa walima domin taya murna, amma da ba don haka ba , shi babu wani shiri da yayi domin murnar ranar. Dukaninsu sun gayyaci abokanan su shiyasa guru ya tsaru domin duk manyan 'yan boko ne samari masu kwalisa gayu kenan, ango kuwa babu wani abokan shi da ya gayyata, to yawanci ma shi bai fiye sakewa da mutane ba, kuma abokan shi da suka shak'u da juna turawa ne, 'yan gari daban-daban shiyasa sam bai da abokai a najeria sai Wanda ba'a rasa ba. Shigar wani irin yadi suke yi baki Wanda bantab'a ganin irin shi ba, dinki iri daya huluna iri daya takalman su iri daya kai hatta da agogon hannunsu iri daya ne, sunyi kyau sosai da sosai, Amjad ya futo ango dashi sai gaisawa yake da jama'a fuskar shi babu yabo babu fallasa. **** To muma namu b'angaran haka take mun shirya sosai ko wacce ta k'ure kwalliyar ta, ni da Mimi kayan mu iri d'aya, cikin Wanda ya aiko Rambo dasu ne jiya muka dauki wani masifaffan les ruwan Zuma, anyi mishi wani irin dinki mai tutoci gaba da baya dinki Riga da siket ne rigar kuma bata da girma babu abunda yafi burge ni da dinki sai yanda aka kaya ta hannun rigar d'aya dogone d'aya kuma gajere gajeran anyi masa wani falmaran a saman sa cif rigar tayi min amma duk da haka saman k'irjina sai da suka futo k'aida ne dama indai zan sanya Riga pitatd to sai saman nonuwana sun futo har tsagar su, saboda Allah yayi min baiwar su, sai nayi amfani da gyale mai Dan fad'i inda na samu ya rufe min mazaunai na, amma yana da sharara dole sai an ga komai nawa, hakan ma dai dashi gwara babu, ni kuma bazan yi kwalliya ta in sanya babban mayafi ba. Mimi kam net ta sanya kamar yanda amare suke yi muka futo waje muna ta d'aukar hoto, wayar na hannuna naga kira, shine na daga kaina ina Neman Mimi tana can suna hoto, a dake na daga wayar nayi sallama. Zuciyarsa yaji dam!! Jin muryar ta, dake namiji ne sai ya maze cikin wata 'yar iskar murya yace." Mommahh ga motoci nan sun tawo d'aukar Ku, na k'agu naga fuskar ki, wallahi naji k'amshin ki, humm! Ina fatan zan same ki, a yanda nake tsammani, sai kunzo."! Kashe wayar yayi ba tare da ya bari tace komai ba, ya maida ita aljihunsa, ya cigaba da sabgar shi da jama'a. Saroro nayi da waya a hannuna gwiwa tayi sanyi sai naji duk wani karsashi da kuzari na, yayi kasa, tunanin guy nake, dama can yana son Mimi Ashe yake pretending ko kuma yanzu ya fara sonta, ni dai tunda nake dashi ban tab'a jinshi da irin wannan muryar ba, gashi yana fad'a mata kalamai na so, zuciyata ta shiga zullumi da wasi-wasi, gashi tayi min wani nauyi ina jin bakin ciki a cikinta da kyar na dai-dai ta kaina na shiga cikin jama'a muka cigaba da hoto amma lokaci lokaci sai inji fad'uwar gaba idan na tuno guy din. Motoci uku ya turo masu zafi dama ba mu fi mu bakwai ba, muka shiga sai Jan bolo gurin parking motocin suka k'arasa da mu sannan ko wacce ta futo, haske ko ina da ina kamar rana ga wasu manya manyan motoci a fake a gurin, k'amshin turare kuwa na wannan yana wane wancan, can hango shi ya tawo abokanshi biyu a bayan shi, gabana ya dinga bugawa tun kafin su k'araso nake kokarin nemo jarumta ta tana guduwa yayi min masifar kyau! Farin mutum cikin bak'aken kaya, sai ya zama kamar wani tauraro cikin abokan nasa abun mamaki tunda ga nesa nake hango wani kwantaccan murmushi k'ayattace a fuskar sa, Suna karasowa gurin ya rike hannun Mimi tuni abokan shi da masu d'aukar hoto suka fara aikin su, suka fara tafiya mukuma muka rufa musu baya,

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});