Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,220 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

barmin shi ko in bar miki shi, Amjadu Mijin ki ne ki kwantar da hankalin ki." Shuru tayi ba ta sake cewa komai ba. Minti goma tsakani wayarta tayi kara dauka tayi tana lumshe ido na na tabbatar da cewar shine ya kira ta, mik'ewa nayi na fuce daga dakin domin bana son inji hirar da zasuyi ballantana i n shiga damuwa. Sai bayan Sallah la'asar Umma ta dawo gidan, jikinta duk babu k'wari tace" Asmau Zuba min ruwa inyi Alwala a hanya la'asar tayi min." Da sauri na zuba mata na mik'a mata ina nazarin ta, har ta shige band'aki Dakinmu na shiga jikina a sanyaye a zuciyata nace Akwai matsala gaskiya tunda naga Umma ta shigo gidan nan jikinta babu k'wari. Kusan Rabin awa da shigowar ta ta kwala mana kira. Ni da Mimi muka amsa a nutse muka Isa Rumfar, tana zaune da carbi a hannunta tace"Duk Ku zauna muyi magana." Zama mukayi ko wacce da Abunda take saka wa. Carbin ta aje ta kallemu tare da fadin "Babban al'amari ne yake tunkaro mu dani da Ku, ina so kuyi min adalci kuyiwa kanku a adalci bana son zumuncin Ku ya lalace saboda duk inda akace kishi to sai anyi shi ko ciki daya kuka futo Yanzu daga gidan Yunusa nake Wannan yaron da yake Neman Ku da aure tun safe ya turo magabatan sa, da kud'in aure harda sadaki yace." Nan da wata guda yake so, ayi komai a gama. Kawu Yunusa ya amsa musu hade da karb'ar dukiyar auran, kafin in futo daga gidan Aminu yaje da maganar shi ta cewar yana son auran ki." Tafad'a tana nuna Mimi da hannu, a cewar sa tun kina yarinya yake sonki ya ki fada ne kawai saboda yana ganin baza ki fi k'arfin sa ba, sai Kuma gashi lokaci guda wanki hula na Neman ya kaishi dare. Kawu Yunusa yace magana ta wuce tunda har ya bari aka karb'i kud'in auran ki. Sai dai yayi hakuri kawai. Yanzu halin da ake ciki yana babban asibiti na Malam Aminu domin fad'uwa yayi a gurin har na tawo bai dawo dai-dai ba." Umma ta k'arashe maganar ta zuciyar ta babu dad'i. Nace"Umma me yasa Ya Aminu bai yi magana da wuri ba har sai da ya bari aka karb'i kud'in auran ta, to ai itama Mimin. Zata shiga wani hali Kuma jiya mun gama magana da Amjadu cewar ya janye aurena saboda rashin dacewar haka, Mimi zai aura kuma daga baya azo ana kace nace." Umma tayi shiru fuskarta cike da alhini. A hankali Mimi tace." Umma ki kwantar da hankalin ki, Indai akan sona Yaya Aminu ya suma har ta kaishi ga kwanciya a asibiti insha Allahu ni zan share miki hawaye Dama nike son Amjadu bashi ba Asma'u yake so tuntuni zuciyata takasa yardar min da haka, Umma zan auri Ya Aminu ki kwantar da hankalin ki." Umma ta share hawayen ta, tace"A'a Mimi bazan miki dole ba bayan an kawo kud'in auran ki saboda son kaina ince ban yarda ba ga Wanda nake so ki aura duniya sai ta zage ni mutanan gari su dinga fadin"Don bani na haife ki ba shiyasa nake miki bakin cikin shiga cikin daula bayan haka kuma zuciyar ki tana son Amjadu idan nayi haka ban miki adalci ba, dole Aminu shine zai janye kudurinsa." Kuka Mimi ta sanya hade da rungume Umma tana fadin "Wallahi Umma da gaske nake babu abunda zaki nema a duniyar nan ban yi miki ba, mutukar ina dashi, Na hak'ura da Amjadu zan auri Ya Aminu." Cikin kuka ta k'arashe maganar. Rungume ta Umma tayi tana kuka, nima naji k'walla ta cika min ido nace"Umma yaushe zamu je asubitin ."? Je ki d'aura abunci da sauri ana idar da sallahr magariba sai muje." Mik'ewa nayi na nufi kicin. *7/November/2019* [11/8, 11:36 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* Mallakar_BINTA UMAR LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA. 44 A gurguje na kammala dafa abunci shinkafa da faduka nayi wacce taji allayyahu da albasa, Bayan mun idar da sallahr magariba ne muna shirye-shiryen tafiya sai muka ji sallama Umma ta futo da sauri Yaya Aminu ne da Musa da Kawu Yunusa suka shigo, Umma tace"Kaddai an sallame shi." Kawu Musa yace." Gashinan kina gani dama nace Zai farfad'o Suma yayi." Ya Aminu ya zauna kan tabarma hade da dafe kansa. Nida Mimi muka futo muka tsaitsaya Dariya nake wa Ya Aminu ganin yadda ya fyad'e lokaci guda. Sallama Kawu Yunusa yayi suka tafi ni da Musa kuwa babu Wanda ya kula kowa. Umma tace"Maza je ki kawo masa abunci." Kicin na nufa da saurina. Mimi ta zauna gefansa tana yi masa ya jiki. Abunci na kawo na aje gabanshi Naje na dauko ruwa pure watar babu sanyi,yace." Kije ki siyo min me sanyi." Umma ta mik'o min ashirin tare da fadin"Ki siyo guda hudu. Hijab din Umma na zura na futa daga gidan da sauri Ya Aminu bai ci abincin sosai ba ya aje cokalin ya mike ya bar gurin. Duk muka bishi da kallo. Umma tace"Cuta ta samu manya ." murmushi nayi kawai Mimi kuwa tashi tayi simi-simi ta shige dakinmu Nida Umma bamuyi hirar arziki ba muka tashi Ina shiga dakinmu na tadda Mimi ta juya baya tana Kuka harda shashsheka. Cikin mamaki nace"Mimi kuka kike yi."? Banza tayi min Da sauri naje na birkitota sai naga idonta yayi mugun ja sai ajiyar zuciya take. Zama nayi kusa da ita hade da rike hannunta nace"Mimi nasan kin amsawa Umma ne domin ki kwantar mata da hankali. Nasan bakya son Ya Aminu Amjadu kike so Mimi me zai sa baza kiyi wa kanki gata ba zaki jefa kanki cikin mummunan hali. Kinsan bakya son Ya Aminu me yasa kika amsawa Umma." Hannuna ta rike tamau! Naji jikinta sai karkarwa yake Tace." Asma'u na rasa yanda zanyi da zuciyata nayi-nayi incere son Amjadu abun yaci tura ji nake kamar zan mutu Mimi zuciyata tana azabtar dani kan abunda bazan samu ba, don girman Allah ki taya ni da addu'a zuciya tabar cutar dani, soyayyar da nakewa Amjadu Allah ya cire min ta gaba daya ta koma kan Ya Aminu." Kuka nasa saboda tausayin ta tabbas so bala'i ne hannunta NA rike dake yin wani irin karkarwa nace"Mimi zan sanya ki a adduata in sha Allahu, kinga na farko ke kika cuci kanki d'azu da Umma tayi miki maganar Aminu sai ki nuna rashin amincewar ki, tom kinga daga baya baza kije mata da wata magana ba. Zan cigaba da taya ki addu'a Ubangiji Allah ya yaye miki ya zab'a miki mafi alkairi." Sosai take kuka ina rarrashinta Sai kuma naji ta fara wani irin tari!! Na mike da sauri na dauko mata ruwa D'ago ta nayi na fara bata, Tana shan ruwan tana tari da idonta yayi jazur Cire ledar ruwan nayi na bugun bayan ta. Tare da yi mata sannu. Dana ga tarin yak'i sauk'i futa nayi da sauri na dauko gishiri a kicin na zo na Dan gwala mata a baki. Tafi minti goma tanayi sannan ya lafa. Sai haki! Take. Ruwan na mike mata

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});