Chapter 68
Chapter 68
muke yi da ita kawai naji wani mugun kamshi ya bak'unci hancina sawun tafiya naji na kalli kofar shigowa da sauri, wasu hamshakan mata ne suka shigo cikin ya tsine fuska sukayi sallama, na d'ago Cikin nutsuwa nake amsa musu, Hajiya Fatima ta kalleni ya a mutse tace"Da'alama kece "Asma'u ko."? Babu walwala a tare dani nace" Nice." Kallon banza tayi min ta wani ya mutse fuskar ta had'e da tofar da miyau! "She is ugly girl!!." Ta fad'a tana kallon Momyn Jahid dake bin tsakar Gidanmu da kallo kamar Wanda take Neman wani Abu.... Wani irin tsinkewar zuciya naji lokacin da tafad'i min wannan Kalmar kallo nake binsu dashi cikin mamaki!! Momy Jahid ta kalleni a wulakance tace"Ke! Ina uwarki kwad'ayyaya gurun ta nazo ni." Umms ta futo tana fad'in "Asma'u ke da waye ne."? Cikin takaici da jin haushi nace "Umma wad'annan sakarkarun matan ne suka shigo mana gida babu sallama ko wacce tana fama ra karnin bleecing sune har suke kiran wani da mummuna."! Momy Jahid ta kawo min wani bahagon mari tare da fadin" Ke don ubanki kin San kuwa ni wacece a gari nan. "? Kaucewa nayi da sauri ina fadin " Sanin ko ke wacece bai dame ni ba nasan dai ke macace mara tarbiyya mace mai izgil...... Kafin in karasa Umma ta gwab'e min bakina tare da fad'in"Asma'u baki da hankali ko."? Nace. " Umma kin..... Tsawa tw buga min tare da fadin",wallahi in bakiyi shiru ba ranki zai b'aci a gurina."!!Momy Mujahid tace "Ki k'yaleta ta zageni da kyau! Nagode Allah da ya nuna min halin ki tun kafin Dana ya aure ki dama jama'ar gari na fadin haka a kanki,to bari kuji gargadi na daku da babban murya tun wuri Ku janye jikin Ku domin har indai nice mahaifiyar Mujahid wallahi bazai aure ki ba bazan hada jini da talakawa fakirai irin Ku ba, mutsiyata kawai." Mamaki ne ya lullub'e ni jin Ashe da da mahaifiyar Jahid nake magana naji tsoro da kunya sosai amma lokaci guda naji wata irin muguwar tsanar matar domin a rayuwata na tsani masu kudi marasa kaunar talaka ya rab'e su. Cikin daki na shige cike da takaici a fili nace "Wallahi kinci darajar Mujahid ne kawai." Ashe taji duk da k'asa kasa nayi maganar aikuwa naji tana fad'in"Da kin sani kin dake ni kamar yanda kikayi NIYYA marakunyar yarinya kawai. " Umma kuwa hakuri kawai take basu Hajiya Fatima ta daka mata wata irin tsawa "Dallah rufe mana baki."? Umma ta rike hab'a cike da mamaki! Hajiya Fatima ta cigaba Da cewa" DUk laifin naki ne ai hausawa suka ce ido na mudu ba yasan k'ima, in banda abunki ina mu INA Ku kwadayi ne ya rud'e ku kuma kinyi a banza domin dai d'anmu bazai auri yarinyar Ku ba." Umma taji zafin maganar da Hajiya Fatima ta fad'a to dake kowa na da nashi hankalin, sai ta share kawai tace "Shi aure nufi ne daga Allah idan Mujahid shine mijin Asma'u babu mahalukin da ya isa ya hana, idan kuma bashi bane Allah ne masa ni don haka Ku kwantar da hankalin Ku." Momy Jahid ta Ciro d'aurarrun kudi cikin jakar ta dauri uku ta watsa ma Umma a jiki cikin izgili tace"Ki tofar da bakin miyau na bakin ki domun kinyi sab'o Wallahi Mujahid bazai auri yarki ba mutukar ina Raye. "!!! A fusace taja hannun Hjy Fatima suka futa daga gidan. Umma ta shigo inda nake tana fad'in" Ikon Allah Ashe haka wasu masu kud'in suke? Ashe mahaifiyar Mujahid bata da kirki shikam yaron kirki dashi lallai albasa bata tayi halin ruwa ba." Nace Umma ki k'yaleta badai Jahid ne bata so na aura tom ni. Kuma sai na aure shi sai inga ya zata yi."! Umma tac"A'a ni bana yi miki sha'awar auran shi tunda uwarsa bata so ko anyi anyi auran ma to ba dad'i zakiji ba, kowa ya shaida cewar matar shi mutuniyar kirki ce kingani ke babu Matsalar kishiya tunda ta amunce ko ka bata amunce mijinta ya aure ki ba tom Allah da manzon sa, sun hallasta amma gaskiya matar nan ta bani tsoro." Nace"Umma ki kwantar da hankalin ki, kamar yanda kika fad'a cewa aure nufi ne na ubangiji to ni ina nan kan bakana Wallahi babu gudu babu ja da baya sai dai in Jahid din ne yace ya janye maganar aure na tom sai in hak'ura. " Umma tace "To Allah ya zab'a abunda yafi alkairi dai." Amin nace zuciyata duk babu dad'i. Kuka sosai Momyn tasa take da kyar ya shawo kanta tayi shiru yace." Ki fada min ko menene Mommy" Tace"Wai ni yau ka kajawo wa zagi a gurin wadanda basu isa ba, Mujahid yau matar da kake Neman auranta ta zage ni ta kirani karuwa wai mai bleecing sai ta kara fashewa da kuka sosai har da dafe kanta." Jahid ya sunkuyar da kansa cike da mamaki anya kuwa Asma'u zata iya zagin Momyn sa kamar yanda ta fad'a to wai ma shin a ina suka had'u da juna ne.? *27/11/2019* [11/28, 7:55 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *66* Mujahid ya cigaba da rarrashin Momyn sa har sai da tayi shiru tukkuna ya kalleta a nutsu yace."Momy wai ina kika ga Asma'u da har tayi miki rashin kunya nifa abun nan ya bani mamaki."! Cikin fusata Momy tace"Naga kamar kana shakka ne Jahid har kana titsiyeni ka tambaye ni, to gidansu nasa aka kaini domin in gargade ta ta fita harkar ka domin naga mayu ne kana zaune da matar ka ta kirki ka je ka kwasowa kanka kaska shine fa ta yi mana wankin babban bargo nida Hajiya Fatima." Mujahid yayi kasa da dansa cikin mamaki jin wai momy gidansu Asma'u taje to in hakane Ashe itace ta jawowa kanta raina yasan halin Momyn sa da zubda girma mybe taje tayi wulakancin da ta saba ne. Tace "Saboda haka in dai nice mahaifiyar ka ban yarda k auri yarinyar ba, shida shiru yayi mata har sanda ta kare fad'an ta yayi mata sallama ya tafi gida. To ko da yaje gida ma matarshi kasa gane kansa tayi dama 'yan kwanakin nan haka yake mata duk ya sauya kwayenta nace mata dama idan namiji zai kara aure canza hali yake, ita dai tunda ta hada masa abunci sai ta shige d'akinta domin ta lura kamar zamanta a kusa dashu baya so. Jahid kuwa ba wani ci abunci da yawa ba, ta kwanta duguwar kujera yana tunanin ala'amri lokacin yi wayar su nayi ya kirata. Lokacin ina zaune ina yin game a wayata naga kiransa dama na tsammaci haka, Muka gaisa kamar yanda muka saba kana ya d'ora da maganar shi kamar haka" Asma'u wai da gaske Momyna tazo gidanmu."? Nace"Babu wai Mujahid Momynka tazo gidanmu. " shiru yayi na minti biyu yace."Ki fada mun gaskiyar Abunda ya faru." Nace"Jahid Momyn ka tazo tayi mana cin mutumci sosai takai har sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78