Chapter 14
Chapter 14
ya hallice shi a haka. " Gyada kansa yayi tare da fad'in"Wannan ke yake damu, kiyi abunda na umarce ki kafin in Riga goma." Cikin daga murya ya fad'i maganar. Jin nayi shiru ne yasa ya damk'i gashin kaina hade da ja da mugun k'arfi !! Ihu! Na kurma ina fad'in"Zan y......Fuzgar gashin Yayi da k'arfi yace." Oya! Ce ne *Amjadu* kayi hakuri sau goma sha biyu nake so ki fada." Rintse idona nayi ina cije bakina na fara fad'ar *Amjadu kayi hakuri bazan k'ara ba.!"* sai fa na fad'i haka sau goma sha biyu kamar yanda ya umarce ni. Babu sauk'i a muryarsa yace." Duk naga shirme da kika rafka naga irin rashin mutumcin da kika tsula a gurin party ku , to ki sani ma Sam! Bakiyi wani kyau ba, kullum kina kiran kanki da Me aji mace mai daraja to duk baki amsa wannan sunan ba, *Momyna* ita za'a kira da wannan sunan." Shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa "Momyna ita yafi dacewar na aura a tsakanin Ku, to kuma sai d'azu wanki Aminu yake rokona kan in hada in aure Ku gaba d'aya, cewar kin tayar da hankalin ki, ke ni kadai kike so, hake ko ba haka bane."? Kallonsa nayi cike da mamaki anya Ya Aminu zai fada masa haka.? Wata zuciyar tace" Tsaf Ya Aminu zai iya fada masa haka saboda daman ba shiri kuke dashi ba." A d'age na kalleshi ina ya mutse fuskata nace"Sai dai Mimi don da ita kuka fi dacewa amma ni ko maza sun k'are bana jin zan aure ka gwara in k'are rayuwata a haka." Miskilin murmushi yayi bai ce komai ba ya sake ni, hijabina na dauka ina kokarin sanyawa naga ya tada motar nace"Ina zaka kaini."? Ko kallo ban ishe shi ba, ya figi motar da gudu.! Da sauri na sanya hannu guda na rike sitiyarin motar murya ta na rawa nace"Ka mayar dani gida don girman Allah." Ko kallona bai yi ba, ya cigaba da fafura gudu, kuka sosai na sanya tsoro ya shige ni ganin fuskarsa murtuk!! Nace"Wai me nayi maka ne kake kokarin wulakantani ? Ita Mimi meya sa baka yi mata abunda kake min. " Shiru babu Amsa, yanzu tsoron gida nake da tsoron dukan da Yaya Aminu zai yi min. Hannunsa na rike tamau! Ina rokanshi motar ta fara gargada! A fusace! Ya fuzge hannuna had'e da yarfa min mari." Cike da mamaki na dafe kuncina ina kallonsa... Da Jan ido ya kalle ni tare da fad'in"Ki shiga hankalin ki." Shiru nayi tsoro yana shigata. Gudu yake sosai kan kwalta, naga mun wuce Jambulo wajan gidan shi ya mik'e titin BUK bakina na rawa nace"Kayi hakuri." Hankalinsa na kan driving ki kallona bai yi ba. Rimin Gata muka shiga sosai, yayi parking dai-dai wani k'aton gidan mai Haske ko ina jama'a na ta shiga da motocin su Suna shan mai. Da sauri naga wani mai aikacin ya nufo mu jikinsa sanye da Uniporm orange da tambarin sunan mai gidan mai yana k'araso wa na ga jikinsa rigarsa an sanya *A&A Amjadu Mai nasara feturolium* nace Ashe har gidan mai ne dashi, cikin turanci naji suna maganar Sam ban fuskanci komai ba na dai ga mutumin ya juya ya tafi da sauri! Minti biyar sai ga mutumin shida wani, sai da suka k'araso sannan naso na gane wanene. Gaba na ne ya fad'i ganin Abokin Shamsu wato Abba gana, yayi tsuru-tsuru, Bude kofar motar Yayi hade da umar tarsa ya shiga Abba gana ya shiga motar ba tare da gaddama ba. Shi kuma ma'aikacin ya koma gurin akinshi Juyo wa yayi yana kallonsa, muryarsa babu wasa yace." Malam meye sunan ka? Kuma meye ya kawo ka wannan jahar."? Abba yace." Sunana Abba Gana ni mutumin mai duguri ne, yau sati na biyu a jahar kano, Nazo Neman kudi." Gyada kansa yayi murya a cunkushe yace." Kasan wannan yarinyar."? Naji gabana ya buga damm!!! Shiru Abbah yayi, tsawa ya buga masa tare da fadin" Answer me." Baki na rawa Abba yace." Banga fuskarta ba Yallab'ai." Cikin wata irin kyara da hantara yace." Ki juya masa fuskar ki ya kalle ki."!!!! Da sauri na juya muka hada ido da Abbah Wanda tun ranar party mu bamu sake had'uwa dashi ba. Da sauri Abba yace." Na Santa sosai Yallab'ai. " "Good."! Yafad'a yana jin jina kansa. Bakina na rawa nace" A ina ka sanni da har kake cewa kayi min farin San.....ban k'arasa ba, ya gwab'e min bakina da gwiwar hannusa. Dafe bakina nayi ina kallonsa hawaye na zubo min. Kallona yake shima fuskar sa babu sauk'i. Minfi minti biyu a haka sannan ya juya da kaurarriyar murya yace." Abba kana son ta ko."? Abba yace." K'warai kuwa Yallab'ai. " Gyada kansa yayi yace."Zaka aure ta ni zan tsaya maka a kan komai zan baka gida akin yi da duk abun bukata." Abba ya dinga godiya tsakanin sa da Allah, yace." Kana iya tafiya"Abba ya fara kokarin bude motar sai kuma ya daka ta tare da juyo wa Cikin sauri yace." Yallab'ai nagode k'warai da wannan karamcin naka, hak'ika idan ana samun mutane irin Ku to da talakwa sunji dadin su, amma ka yafe min hak'ika yanzu na kara tabbatar da cewar Asma'u matar manya CE, nagode da karamcin ka, Asma'u da kai ta dace Yallab'ai. " Wani kallo Amjadu ya watsa masa yace." Bayan kun gama wasan soyayyar da ita zaka ce dani ta dace. Tab'e bakinsa yayi yana girgiza kansa yace." Ni nafi k'arfin socond hand, kawai idan baka so in bawa wani." Abbah yayi shiru yana tunani daga bisani yace." To Yallab'ai duk yanda kayi dai-dai ne." 'Yar dariya yayi yace." Yanzu kayi magana guy kaje kawai ka fara shiri." Simi-simi Abbah ya bar gurin yana mamakin meye manufar sa kan haka, yarinyar da yayi-yayi ta bashi numbar waya tak'i yau ita za a bashi, shi ba Yaro bane yana kallon tsantsar so hade da kishi a idon sa, addu'a yake Allah yasa kar ya auna shi garinsu dama jarabar fad'an da ake ne yasa ya biyo Shamsu tunda dukanin su iyayen su sun mutu. Kunna motar yayi muka fara tafiya. Da gefan ido ya kalleni tare da fad'in"Ko kiyi min shiru ko kuma in sauke ki anan." Cikin kuka nace"Allah kad'ai na mik'a masa kuka na akan ka, ka zame min bala'i ka shiga rayuwa ta, me na tsare maka a duniyar nan, da kake kokarin tozar ta ni." Cikin zafin zuciya yace." Kika tozarta kanki dai! Ni gata nake so nayi miki saboda na lura da yanda bagalar ki take, kar ki dauko abun kunya domin baki da juriya, nace zan rufa miki asiri in aure ki kin ce bakya so, tom naje gurin sauranyin naki da Kuka gama rungume-rumgume dashi zan taimake Ku, shine kike min kuka harda hada ni da Allah, me kike so ayi miki."? Murya ta a shak'e nace"Idan na dauko abun kunya meye damuwar ka? Na farko dai dani da kai bamu had'a dangartakar komai ba, babu wata alak'a a tsakanimu,saboda haka baka da damuwa da wannan....ka tse ni yayi ta hanyar fadin"Sai kace ba musulumi ba, wato kina so Allah ya kama ni kenan ? Idan kika je kika dauko zunubi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78