Chapter 63
Chapter 63
ta kasance sai na dauki fansa."!!!!!!! Ko juyowa bai ba, ya shiga wani daki, kokarin binsa nake wasu nurses suka rirrike ni suna bani hakuri, wani k'arfi ne ya zo min a lokacin na fuzge daga jikin su sai kace wata mai iskokai na afka dakin a guje! Abunda na gani ya sani jin wani irin jiri tuni na fad'i a gurin ina kallonsu dishi-dishi inda suke kokarin Dora mimi kan wani gado Duk an dad'adaure mata k'afafunta da hannaye ta babu Wanda yabi ta kaina harshi kanshi Jahid din suka tura Mimi dake kwance kan Wani k'arfe suka futa. Silalewa nayi na fad'i a gurin ba tare dana San a wace duniyar nake ciki ba. Tuni Umma da Granny sun futa sun tsaitsaya aka futo da gawar Mimi tare da sanya ta a motar asibiti Umma sai share hawaye take yi, suka shiga, dravar yaja motar, lokacin kowa ya manta dani sai Jahid din da ya dawo ta kaina shine duk yayi min taimakon su na likitoci na dawo hayyacina kuka sosai nake yi had'e da dukan shi kamar mahaukaci nake cewa an hada baki dashi an kashe min Mimi, ganin kamar bata cikin hankalin ta ya sanya yayi mata allura take bacci me nauyi yayi gaba da ni. Wasu nurses ya sanya suka shigar masa da ita mota, ya bar asibitin cikin halin damuwa da tashin hankali, Kamar gawa a ka shiga dani cikin gidan Amjadu inda ya cika da Jama'a maza da mata lokacin tuni an shirya gawar Mimi an futo da ita, saboda haka Jahid kawai ya tsaya nan aka sallace shi da ita, shine a gefe Amjad din a gafe suka dauki makarar dukanin su zuciyoyin su babu dad'i amma dai komai ubangji ya saukar kan bawan shi ne dai-dai. *25/11/2019* [11/26, 9:20 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *63* Mutuwar Mimi ta girgiza zuk'atan Al'umma bamu kad'ai ba hatta da masu gadin gidan sai da suka ji a mutuwar a jikin su, Jama'a kuwa daga ko ina b'arkowa suke yi ta'aziyya wasu kuma gulma ce take kawo su, domin 'yan jarida sun ruga sun gama wa tsawa duniya cewa mutuwar mayar Young millionaire tana da nasaba ne da harin da jama'ar gari suka kai masa, wa 'yanda basu San yayi aure ba suka dinga mamaki shine suke zuwa zaman makoki, mai girma governor Sarkin kano duk dasu akai sadakar uku, su mai citta ma duk dasu babu tsoron Allah ko na kwabo a tare dasu, a fili sun nunawa Amjadu kara a zuciyarsu kuwa murna suke yi sosai, shi kuwa governor abun ne ya soma bashi tsoro ganin yanda yazo zaman sa na k'arshe jama'ar gari na raka shi da dutsina suna fadin "Ba mayi."!!! Kuma tunda ga mutuwar Mimi jama'a suka fara gane cewa harda sa hannun governor akan sharrin da akai wa Amjdin, ranar a tsorace ya bar kofar gidan Amjad ganin yanda matasa suke jifansa kamar ba governor ba, sai da jami'an tsaro suka fara sakin harbi sannan kowa yq shifa taitayin sa, Umma kuwa jin irin zantukan da jama'ar gari suke yi kan mutuwar Mimi yasa tace" Suyi hakuri kar su bata wa Mimi gawa kawai Allah ya amshi abunsa lokacin da yaso. ***** Yau kwanan Mimi bakwai a karkashin k'asa, na fige na tsigale sai Umma tayi da gaske nake cin abinci kullum ina zaune zukud'inm! Ko kuma in tafi dakin ta in kwanta kam bed dinta hade da rungume wani k'aramin hoton mu, dake cikin frem a kan drowr gefan gado ta aje shi, kuka nake yi sosai, Umma granny dashi kanshi Uban gayya naga duk sun saki jikinsu har hira suke yi suci abunci hankali kwance kuma suyi dariya, ni kadai ce nake cikin halin damuwa da bakin cikin rashin Mimi, tsakanina dashi kallone domun tunda Mimi ta mutum magana ta fatar baki bata hada mu dashi yau kwanakinmu bakwai kenan a cikin gidan shi, ya sake sosai yayi wanka ya shirya harda fesa turare sai abun yayi ta bani mamaki ina zargin sa, dama ya fi son Mimi ta mutu ya cigaba da tsula tsiyarsa take wata irin tsanar sa ta cika min zuciya ta. Jahid kullum yana kirana a waya sai dai Sam bana sakewa dashi domin gani nake yi kamar bakin su da daya da Amjad din, matar shi Hafsa me kirki da ita duk a gama zaman makokin INA lura da ita da yanda take satar kallona a fakaice. Babu kuzari a jikina na futo daga dakin Mimi hannuna rike da k'aramin hoton mu, kusa da Umma na zaune a hankali nace"Umma zaman me muke yi a gidan nan? Wallahi nagaji gani nake kamar Mimi zata dawo gwara mu tafi." Umma tace"Eh dama yau kam zamu tafi tunda an share makoki, muna jira maigidan ya futo ne zamu je duba baby insha Allah daga asibitin sai mu wuce gida." Granny tace"Habadai Ku kuwa ai sai kace Wanda ake kora kwabari kuyi sati biyu mana in baza Ku bari ayi ar'bain ba, har yanzu fa ana zuwa gaisuwa." Umma tace"Tafiyar tamu ta dole CE Hajiya ni kaina a takure nake a gidanan wallahi, kiyi hakuri duk Wanda zai mun gaisuwa ya same ni a gida." Granny tace"To Allah dai ya gafartawa wannan yarinya. Tsaf ya futo Cikin dogayen kaya,na lura tunda akayi mutuwar nan bai sanya k'ananun kaya ba, k'amshin sa ne ya cika parlor ya tsaya bakin kofar shi yana gyara links dinshi, saurin kauda kaina nayi daga kanshi ina jan tsaki kasa-kasa wallahi wani mugun haushin sa nake ji. Umma tace"Ka futo kenan."? A hankali yace." Eh Umma Ku tashi muje yanzu, amma naji kuna wata magana ko." ? Umma tace"Eh kam yau zamu tafi gida." Yace." Umma kuyi hakuri ayi sadakar ar'abain mana." Umma tace"Bazai yiwu ba, INA da uziri Asma'u kuma makaranta zamana a gidanan bashi zai dawo da Mimi ba." Yace." Hakane Umma shikkenan Allah yasa ka da alkairi. " mik'e wa Nayi da sauri na bar gurin, hijab dina na dauko dama tunda nazo kayan Mimi nake amfani dasu, Umma ko granny ce ta dauko mata wasu sabbin atampopi super take sanya wa yanzu daya daga cikinsu a jikin ta, Granny ta mike tana fadin "Baza Ku barni a baya ba, muje inga 'yar yarinya cikin kwalba." Aikuwa ko da sukaje Asibitin fafur likitoci suka hana su shiga ganin baby Aisha yarinyar da Ubanta yayi mata huduba da sunan mahaifiyar ta, shi kam ai dactors din sun San shi farin sani dolen su suke kyaleshi ya shiga yaga babynshi kullum baya iya bacci sai yaje ya ganta haka kazalika kullum kara kaunar yarinyar yake Cikin zuciyar sa, yarinyar kamar su daya da uwarta sai dai ta kwaso hasken fatar shi, fara ce sosai, Amjad kam yafi Mimi haske nesa ba kusa ba, Alhmdullahi tana samun kulawa sosai daga gurin dactors ta fara k'wari da girma jikinta ya fara murjewa tana rayuwa cikin kwalba cikin hukunci ubangji. Babu yanda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78