Chapter 60
Chapter 60
da abunda yake Cikin ta sai granny su kadai suka rage min a duniya my friend bana so in rasa Momyna."!!!!! Tsabar tausayi ta hana Jahid cewa komai ya ja hannunsa suka shiga wani d'aki. A gigice Ya Aminu ya shigo gidan Hannunsa rike da wayar Garba abokisa. Kamar dai d'azu da ya shigo mana da ita, duk ya rasa inda zai tsoma ransa, ya mik'o min wayar bakinsa na kyarma yakasa cewa komai Hannu na rawa na fara dubawa Farko abunda na gani ya sani kurma wani ihu na jefar da wayar hanna hannu na d'ora aka ina fad'in "Innalila wa'ina ilahi raji'un, shikkenan sun kashe mana Mimi mu."!!!!!! Umma ta dauki wayar da sauri tana dubawa, Mimi ce rungume a hannun Amjadu lokacin da suka shiga asibitin nasarawa abunka da mutumin da yayi suna a duniya aka samu wasu suka dauke su vedio a wayoyin su, a lokacin suka fara turawa Media hade da sharhi cewa jama'ar gari sun shiga har gidan *Young millionaire* sun Sassari matar shi mai dauke da ciki Dan wata shida gashinan tana halin rai da rayuwa.! Abunda ya k'ara tayar mana da hankali shine yanda mu ga jikin Mimi dashi kansa Amjadu din duk ya b'aci da jini duk da cewar dare ne amma akwai hasken fitulu a ko ina na asibitin. Umma ta mik'e tsaye cikin tawakkali ta kalli Ya Aminu da yayi tsaye a gurin duk ya rasa me zai yi tace" Muje mu gani Aminu Mimi tata kaddarar kenan, bawa baya wucewa kaddarar sa, muje idan ta mutu ne sai mu karbo gawar ta." Hawaye Ya Aminu ya share ya futa daga gidan da sauri domin samo abun hawa. Ni da Umma muka futa daga gidan kamar wasu zautattu! Shi kanshi hijab din dana sa a baibai na sanya shi, hawaye ne kawai yake zura ra a idona shikkenan Mimi sai ta Allah a yanda na ganta ina gani kamar kafin mu Isa a sibitin za'ace ta mutu. *24/11/2019* [11/25, 8:46 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *62* Lokacin da muka Isa asibitin goma da rabi ta wuce, Dan dai ma daran azimi ne akwai jama'a a bakin asibitin suna siye da siyarwa, har ciki mai a dai-dai ta sahun ya shiga damu, Ya Aminu ya biyashi kud'in sa, ni kam tuni na Dade da futowa daga a dai-dai sahun sai kyarma jikina yake yi. Ko da muka shiga ciki babu mutane sosai wasu kujera muka samu muka zauna. Ya Aminu ya nufi wani d'aki da sauri. Waya ta dake hannuna na kunna na fara Neman numbar Jahid, sai da na kira sau biyar a kashe, cikin mutuwar jiki na aje wayar a cinya ta, Ya Aminu ya futo daga dakin da ya shiga ya nufo mu, fuskar sa babu walwala Gaban Umma ya tsaya yace. "Yanzu wata nurse take min bayani cewar Mimi tana ciki har yanzu ba'a futo da ita ba, kuma abun mamaki na dauka zamu samu mijin nata anan gurin bab........ Kafin Ya Aminu ya rufe bakin sa, Jahid da Amjadu sun futo daga wani d'aki. Da sauri Jahid ya k'araso gurin mu. Shi kam Amjad yana tsaye a gurin da yake. Jahid ya kalli Umma tare da fadin" Ashe har kun samu labari." Umma tace"Ba dole ba wannan tashin hankali dai Allah ya sawwake, mana shi, yanzu ya jikin Mimi yake. "!!? Jahid yace." Jikinta Alhmdullahi Umma ku kwantar da hankalin Ku, jini ake bukata sosai za'a kara mata saboda ta zubar da jini sakomakon fad'uwar da tayi." Mik'ewa nayi zumbur nace"Muje ka sa mata nawa jinin kaji Don Allah ka cece rayuwar ta." Murya ta na rawa na k'arashe maganar. Jahid yace." Dole haka za'ayi muje a dauka a auna mu gani, idan yayi dai-dai sai a d'aura mata yanzu ma an d'ibi na Amjadu ne." Kallon shi nayi dake tsaye kamar wani maraya sai ya bani tausayi mutuka wata zuciyar tace ba abun tausayi bane mutumin nan. Wani daki muka shiga da Jahid ya dauki jinina ya duba yayi dai-dai Dana Mimi take ya umarce ni na kwanta kan wani gado domin ya dauki jinin. Amjad kuwa jingina yayi jikin bango hade da lumshe idonsa Sam ya kasa zuwa ma ya gaishe da Umma saboda halin masifar da yake ciki.....Muryar Granny yaji ta shigo gurin cikin kuka take fadin"Sai da tace kar ka futa kar ka futa ka futa gashi da ka futa ka dawo sumul k'alau! Da kai ita kuma saboda tsananin son da take maka, ta fadi kan cikin ta."! Komai a kunne magangan da granny take yi domin dakin da nake ciki a bude yake, Jahid na kalla Ina daga kwance nace "Nasan kasan dukanin abunda ya faru don Allah ka fad'a min komai."? Ba tare da tunanin komai ba Jahid yace." Wallahi Asma'u tsautsayi ne ya afka kan Mimi lokacin da abun ya afku, tana hana Amjad din futa saboda jama'ar garin da suka kawo masa hari har gida, garin kokarin rik'o rigar sa, kawai santsi ya kwashe ta ta fad'i kan cikin ta to shine fa take ta zubda jini, amma insha Allahu zata dawo normal. Murya ta a cunkushe nace"Kana nufin ya sane ya futa bayan tace masa kar ya futa yanzu me futar tashi ta jawo mana, ai dai gashinan da kunnen ka kaji Abunda kakar shi take fad'a ko." ? Jahid ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Tsautsayi fa baya wuce ranar sa, don Allah mu bar maganar bana so Ku Dora alhakin abun kan shi." Shiru nayi ganin ranshi ya b'aci Jahid yana da saukin kai da dad'in mu'amula amma baya son musu da taurin kai shiyasa nayi shiru kawai amma cikin zuciya ta nayi alk'awari sai na fad'awa guy nan magana a kan Mimi komai daran dad'ewa kawai don yaga tana da hakuri sai ya dunga gara ta kamar gare-gare kullum cikin damuwar sa, da bata mata rai. Jini Leda biyu a kauda a jikina nan Jahid din yace min na kwanta kan gadon na huta mintuna talatin, INA kallon shi ya futa daga d'akin. Granny ce ta fad'o dakin tana kuka tana k'ara tisa maganar da abunda ya faru. Fad'i take "wannan yarinya Ubangiji Allah ya tashi kafad'unta amma babu shakka tana shan wahalar rayuwa. " Shiru nayi mata kawai ina bin ta da kallo. Amjadu masjid ya nufa domin yin sallah istigufari kawai yake a fili da Cikin zuciyarsa. Ta shi nayi jikina babu kuzari na futo daga dakin, har yanzu su Umma na zaune cikin sauraron hukuncin Ubangiji, kusan awa guda da shigar Jahid dakin da Mimi take ya futo, kallon mu yayi ya kalli a gogon hannunsa sha biyu na dare saura minti ashirin, futa yayi ya nufi gurin Amjad dake cikin mota Amjad yace." Ta farko ko."? Daga kai Jahid yayi a hankali yace "Alhmdullahi ta farko kuma munyi nasarar tsayar da jinin insha Allahu an sanya mata, shi gobe dole za'ayi scanning din cikin domin ganin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78