Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

abunda bana yi shi nayi wato kwalliyar fuska, kamar wata Queen haka na zama muna sanye da material dinmu Wanda aka yi mana dinki duguwar Riga mai tattara daga baya daga gaba kuma yayi sama anyi masa wani irin yanke gege da gefe dogon hannu ne yayin da rigar ta kasan pitat gown ne gaba d'aya rigar take tayi matse ni tam!! Nishi ma da k'yar nake, gani da manya breast da uban hifs Sai da na sanya yari da sark'a na sannan na kalli mudubi, ni kaina nasan nayi kyau sosai, Munnu da Mimi suka saki baki suna kallona, nace" Meye wai!? Munnu tace." Anya baza ki cire kayan kuwa ba kinga yanda suka matse ki, ke gaki tubar kallah." Nace" lallai Munnu wallahi ko Umma yau baza ta hanani futa da kayan nan ba.Mimi tace" sai ki sanya hijabi idan muka je can ka cire,amma dai kin San gurin ya hada samari da 'yan mata duk budurwar da take da saurayi zata gayyace shi yazo gurin." Nace" Mimi ina ruwana wai don Allah Ku k'yaleni mana." Ganin raina ya b'aci ya sa suka k'yale ni. Umma na zaune s rumfa tana kule-kulen ta muka futo takalemu a tsanake tace "kunyi kyau tamkar wasu amare,amma ke Asma'u meye kika sanya hijabi."? Nace" Umma dinkin ne ya matsani shine nace"idan na shiga cikin 'yan uwana mata sai in cire." Tace" haka yayi to Ku kula don Allah Ku tsare mutumcin Ku ana gama taro ku dawo gida kar Ku tsaya kad'e-kad'e da raye-raye." Muka ce insha Allahu." Muna shirin futa daga gidan wayar Munnu tayi k'ara ts dauka a nutse tare da kashe muryar ta, kasa kunne nayi cike da mamaki jin tana ambatar sunan Shamsu. Ni da Mimi muka kalli juna. Ji mu kayi tana fadin"Eh ka shigo da motar yanzu zamu futo." Sukayi sallama, dukaninmu muka kalleta cike da mamaki nace"Munnu yaushe Shamsu ya dawo kuka kuma jone wa." Murmushi tayi tace" shekaran jiya ya dawo da k'arfin sa, Wallahi aurena zai yi domin aranar da ya dawo ma Baban shi yazo gurin Babanmu baku ga kayan da ya kawo mun ba, wannan hayaniyar da muke ciki ce ta hana ni fada muku." Ni da Mimi muka Ce"Toum Allah ya sanya alkairi lallai alk'awarin Allah ya cika. " dariya Munnu tayi cike da farin ciki muka futa daga gidan. Samari na bakin titi suka bimu da kallo kamar wasu mayu. Wata had'adadiyar mota na hango a fake gefan titi Shamsu na zaune a mazaunin dravar tare da wani Wanda ban gano fuskar shi na, suna sanye da wata masifaffaiyar shadda wagambari hade da hula damanga sunyi kyau har sun gaji. Ganin zuwan mu gurin yasa Shamsu futowa da sauri ya bude wa tauratowar shi motar yana fadin" Girman kujerar ki ne." Hararasa nayi tare da tab'e bakina nace"Haji Shamsu Ashe zaka dawo ai na dauka muma yaudarar tazo kanmu." Dariya yayi yace." Inaaa!! Baby Asma, Ai Munnubiya ta daban ce cikin mata, tab'e bakina nayi nace"Allah yasa da gaske kake." Tunda na fara magana abokin Shamsu yake kallona ina kallonsa ta wutsiyar ido tsaki naja a fili na tsani kallo wallahi. Munnu ta shiga ta zauna Mimi ta zauna nima nashiga sannan Shamsu ya koma gurin zaman shi hade da kunna motar muka tafi. Shamsu sai janmu da hira yake yana fad'in"Ai duk naji labari lokacin da na tafi har daku ake cewa dama yaudarar Munnu nake yi humm yanzu Asma baby kina ganin zan aikata haka kuwa." Nace"sosai ma kuwa Shamsu namiji ne fa kai hunm halin Ku sai Ku."Abokinshi ya juyo yana kallona tare da sakin murmushi yace." Baby Asma wasu mazan ne suka bata wasu amma abokina da gaske yake." Tab'e bakina nayi nace" muna da labarin fa duk 'yan Matan da ya yaudara sun kai goma. " Shamsu ya rike baki yana dariya tare da fadin" duk sharri ne wallahi, karya suke min." Mimi tace"Babu sharri nan gaskiya ce mu dai don Allah kar ka kara guduwa domin wancan karon sai da mukayi jiyyar ta" suka kwashe da dariya shi da abokinsa. Munnu sai mintsina take wai in daina surutan da nake yi ina jinta na kiyin shiru. **** Lokacin da muka Isa guri ya soma cika sosai aka kawata gurin gurin malamai daban da iyayen yara wajan dalibai daban, muma wajan mu daban wajan manyan baki daban .. Masu hotona da vedio baza su kirgu ba, saboda ko wacce da nata,muma mun dauki namu can muka tadda shi, MA kad'a sun fi su biyar suna gefe suna jiyar taro ya watse a fara shagali. Ko wane class da gruop d'insu da kuma irin kalar ankon su, ko wacce tana wace wannan. Mai girma principal ya bude taro da addu'a tare da yi mana nasiha sannan yayi wa 'yan matan da aka kusa bikinsu a cikinmu addu'ar zaman lafiya Wanda basu da mazaje Allah ya kawo musu, hakanan Wanda suke shirin cigaba da karatu Allah ya bada sa'a. Haka Malamai suka dinga mik'ewa suna jawabi tare da addu'a, taro ya tashi guri ya hautsine kowa da ta wagar mutanan shi, da kawayen shi sai d'aukar hoto ake hade da vidio, Ina gefe tare da jama'a ta domin wasu ma ranar na fara ganinsu duk ya wancin su maza ne, tuni na cire hijabina ina yawo yanda na gadama 'yan ajimu sai jana suke dole sai munyi hoto duk inda na sanya kafa abokin Shamsu nan yake sauke tasa ya zame min jele, haka na dinga shiga cikin abokan da samarin 'yan ajinmu muna hoto wasu nayi da waya wasu nayi da Camera man. Abun mamaki ni kadai jama'a suke ja lallai sai sunyi hoto dani, haka Alina ma duk gabar da muke da ita sai da tazo ta jani cikin a bokanta maza da mata mukayi hoto wasu daga cikinsu na fiddo wayoyinsa nayi min. Mimi ce tazo ta jawo ni da k'arfi tana fadin" meye haka kike yi don Allah ki daina ratsa maza kina shiga tsakiyar su baki San suba Fuzge hannu nayi INA fadin "Kinga Mimi yau rana daya ce daga ita babu wata ki k'yaleni." Mimi ya rabu dani ta koma gurin Munnu da sauraynta Duk ankon da mukayi sai da muka sanya su Shadda ce karshen sawa. Waiiiii!!! Fitina! Lokacin Dana futo cikin shadar idanun jama'a kamar ya cinye ni, ni kaina sai bayan na futo a haka Nazo ina da na sani dinkin fitat ne iya cibiya Sam rigar bata da hannu gashi ta matse ni, siket din yayi d'an, kwankwaso na kamar zasu yi magana da kyar nake cire k'afa ta saboda yanda ya matse ni. Tuni suka yo kaina suna ihu!!! Wani Dj ya saki wak'arnan ta *Hamusu brekar wato shimfidar fuska* Filin na nufa sauran k'awayenmu suka rufa min baya, rawa sosai na dinga *wakokin gwanja kamar ni na rera su* mussaman wak'ar shi ta *d'akin bak'uwa dudu bak'ar ashana* ai ina bala'in son wak'ar nan na zage ina rawa tare da sauran 'yan ajinmu Mimi ma da Munnu sun shigo filin ana yi da su. Alina ce tazo ta ja hannuna wai inzo muyi sallama da abokanta, muka nufi bakin get, kamar walkiya naga gilmawar motar guy nan ta futa daga gurin. Abunda yasa

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});