Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 74

Chapter 74

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tace"Wallahi maganar ki gaskiya ce Allah ya kyauta." Nace "Ni Abunda yake damuna Abu daya ne aurana da Jahid wallahi yanzu abun tsoro yake bani ina jin tsoron abunda zanje in Tarar."! Insha Allahu alkairi zaki yadda ke dai ki cigaba da yin addu'a.'a" nace "Nagode Munnu." Da Wannan hirarar muka isa gida. ******* Amjad zaune a harami ya d'aga hannunwan sa sama sai kwararo addu'a yake, yana zubar da hawaye ni kaina ya mugun bani tausayi, ya kai Rabin awa cikin wannan halin kana ya shafa addu'ar ya mike a nutse ya dauki daddumar sa da glass d'insa dake aje a gefe ya nufi mazaunin sa, ko da ya isa ba zauna ba toilet ya nufa cikin kuzari yati wanka ya fito fes dashi kasamcewar ana zafi bai shafa mai ba, sai ya shafe jikinsa da turare ya sanya wasu ubansu parkinsan ash coulor hade da wata hula mai kamar net fara tasa da ita, takalmi mai gidan yatsa yayi amfani dashi ya d'aura tsaddan a gogon shi, kana ya manna farin tabarau din shi a fuskarshi, sai ya kara wani uban kyau, kasancewar ya Tara kasumba bai yi aski ba, sai abin ya bada sha'awa Amjadu ya saje da larabawan saudia domun duk kwakwar mutum bazai tab'a cewa ba balarabe bane ga yanayin fatarsa lufluf domin har tafi ta wani balaraben goge wa fuskarsa babu walwala a dauki wayoyin shi hade da wata k'aramar haka irin ta matafiya, kulle dakin yayi da key ya sauka k'asa. Amjad ya nufin koma wa gida Cikin iyalinsa bayan yaje dakin Allah yayi addu'a ga iyayen sa dashi kansa da sauran alumar musulmi. Yana jirgi ya kira su Rambo ya Sanar musu gashinan kan hanya take suka wuce airport domin tarar sa, Granny ya kira a waya ya fada mata, tace"Amma kayi mana bazata! Mai kake so a girka ma." ? Murmushi yayi yace." Granny kuyi min Dambu da zogale." Dariya tasa tana fadin "Kasamu k'ato Allah ya kawo ka Lafiya." Kashe wayar tayi tana kiran Iyami. Tace" maza a shirya dambu mai kyau ga k'ato nan kam hanya." Iyami tace"Wallahi baby ce take kuka har yanzu taki hak'ura kawai tana wasa sai ta fashe da kuka." Dariya granny tasa tace"Tana tuno uwarta ne, jeki dauko min ita kije kiyi aikin ki." Da sauri Iyami ta dauko baby dake kuka har da majina. Granny ta mik'a hannu tana son ta karbe ta ta make kafad'a wai baza ta zo ba, dariya tayi tana fadin"Kaga ja'ira dole kuwa komai kukan ki kiyi shiru Ubanki na kan hanya. Tace iyami aje ta kije kiyi aikin ki." Iyami ta ajeta a kasan gurin ta nufi kicin da sauri. Lokacin baby ta tsandare da kuka, babu shiri granny ta dauke ta ta Goya Tana zagaye parlor da ita, Tunda ya doso kofar parlor yake jin kukan sweetheart dinshi yaji ranshi ya sosu da sauri ya shiga ciki hade da sallama k'asa_kasa granny ta amsa tana masa barka da zuwa, mamaki yake yi ganin baby a bayan granny a goye amma taba kuka, wayoyinsa ya zube kan teble din gaban shi ya fara kokarin daukar babyn da Granny take kokarin kwance ta, yace." Wai mai akayi mata ne take kuka tun kafin na shigo nake jiyo ihun ta." Granny tace"Sheganta ka ce kawai wallahi tun da taje gurun uwarta tayi kwana biyu Shikkenan ta dawo mana da rigima Don da kyar ma ta yarda da iyami, nu kuwa sai nayi da gaske nake daukar ta." Ya gane inda maganar Granny ta dosa, zama yayi cikin kujera yana goge mata fuska da hakincin sa, yace"Granny nifa bana ganin laifin kowa sai naki ke da kika dauke ta kika basu." Cike da jin haushi yayi maganar. Granny tace"To ka dawo ko zaka fara iyayin naka to me kake nufi iyayenta sunzo su dauke ta sai in hanasu ni kam ban iya wannan k'ek'e da k'ek'en ba irin naka." Baice komai ba ya sanye leb'anshi na k'asa bakin ta, kamar yanda yake mata tana jin jira, aikuwa ta kama tsotsa yarinyar bata manta ba. Kallon ta yake yana jin wani irin tausayin ta cikin zuciyarsa duk sanda zai kalleta sai ya tuna masa da Wife dinshi Mimi ko da yaje Saudia duk Rabin addu'ar shi tata ce. Baby Aysha ta fara lumshe ido kalaman bacco still leb'anshi take tsotsa kad'an kad'an har bacci ya rinjayeta ta saki. Ajiyar zuciya ya sauke ya rungume ta tsam a jikinsa tare da fad'in"Iyami ta gyara mata gurin kwanciya tayi bacci."! Granny ta bude baki zata kwalawa Iyami kira kamar yanda ta saba. Da sauri ya d'aga mata hannu yana yamutse fuska da ido ya nuna mata baby wai kar ta tashe ta. Tsaki granny yaja ta mike daga gurin. Da kanta taje ta gyara mata gurin kwanciya ta dawo zata karb'i ta kamar kurma haka ya zama Mik'ewa yayi ba tare da ya bata babyn ba ya nufi bedroom d'insa da Yarinyar granny tayi sakaro da baki, tana fad'in"On ni naga iyayi da feleke a ka dawo din zaka fara nuna mana iyakarmu ni da Iyami komai mukayi bamu iya ba hummm! Allah ya sawak'e maka." Ni da Munnu ne zaune a Uwar dakin aunty Hauwa ta sanya muku tsuguna cikin wani dogon bokitin na k'arfe inda ta sanya wata k'aramar tukunyar k'asa da garwashin wuta had'e da wani mugun turare da wasu saiwowi masu wani irin kamshi, kullemu tayi a dakin har da Dan mukkuli, tsaki babu irin wannan banyi ba, a ganina ni budurwa CE ba bazawara ba, mai zasa aunty Hauwa ta dinga azabtar damu da turaran matsi kawai garin Neman gira a rasa ido, tunda akace saura kwana goma sha hudu d'aurin auranmu aunty hauwa ta sanya mu a gaba, domin har munnu ma da take surukar ta tace ita bata dauke ta a matsayin suruka ba, k'anwar tace duk abunda zata min zata yi mata, kuma bayan haka Si Dan uwanta take gyarawa Munnu tun tana jin kunya ta daina ji domin yau kwananmu uku a gidan aunt Hauwa tana yi mana izaya iri-iri, magani kullum ta dama da nono mai Dan iskan bauri da wani irin k'amshi kai hawa ka taje sai mun shanye tasa, wallahi ina daga tsigar jikina na Mik'ewa saboda yanayin dandanon sa a bakina babu dad'i bauri yaji zak'i d'aci duka, ranar dai da taba ni zubarwa nayi Munnu kuwa saboda kunya sai ta shanye tasa ta aje kofin ni kuwa kullum rigima muke da ita kan hakan. Yanzu ma Mik'ewa nayi da sauri jin wani Abu na zuba daga k'asa na, zani na nasaki na mai da pant dina. Munnu tace"Ya kika tashi ne." Cikin b'acin rai nace"Munnu ke in zaki zauna zauna ki cigaba da azabtar da kanki kina budurwa ace wani Dole sai kin matse mtssss to wace irin katsewa kuma ake buk'ata. " munnu tace "Don Allah ki koma ki zauna Wallahi tunda kikaga ta dage akanmu hakan yana da amfani." Tsaki naja nace"Sai kiyi ke ni dai na gaji." Kofa na nufa ina bugawa hade da kiran sunan aunt hauwa nace"kizo ki bude min zan shiga band'aki. " bude min tayi taba fadin kiyi sauri ki fito kar maganin ya sane so nske ya bi jikin Ku sosai."

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});