Chapter 31
Chapter 31
galan din mai robibin magi da su d'aurikan busassan kayan miya rumfar tayi tas da ita Umma ta shimfid'a tabarma ta zauna jiran zuwan su. Wani irin kamshi ne ya bugi hancin mu kafin muji muryar dattijiwar matar cike da nutsuwa da kamala tayi sallama. Umma ta amsa mata tare da fadin"Sannu da zuwa maraba lale shigo ciki Hajiya." Granny ta shiga ta zauna kan tabarma fuskarta cike da farin ciki da annushuwa, suka gaisa da Umma cikin mutumci, aunt Hauwa ta gaishe ta hade da dauko mata Lemo mai sanyi hade da ruwan roba Wanda aka siyo mata shi mussaman, Granny ta bude ruwan tasha tayi hamdala, sannan ta kalli Umma cikin barkwanci tace. " Nazo duba kishiyoyina ne, kafin a Kai min su mu fafata da juna." Dariya Umma tayi tace." Aikuwa dai, dole suyi miki ladabi domin shi kanshi uban gayyar da bazar ki yake taka rawa ba a raba hanta da jini kuma da tsohuwar Zuma ake magani." Dariya Granny ta sanya tace." Ai ya juya min baya kwana biyu baya ta tawa kullum bashi da zance sai na kishiyoyina kin ga kuwa dole inyi kishinsu." Umma tace"In ya gama d'akinsa ai dolen sa ya dawo gurin ki." Dariya suka yi a tare aunt Hauwa ta mike tare da fadin "Bari a kira miki su Ku gaisa wai kunyar ki suke ji." Granny tace." Wane irin kunya? Suna jin dai tsoron su hada ido dani tun kafin su shiga humm zasu aure min miji ai dole su b'oye je ki kira wo mun su." Aunt Hauwa ta futa tana Dariya tare da mamakin halin grnay kamar sun saba mata Mai fuska da fara'a gaskiya tana da kirki. Tun lokacin da naji sallamar matar gabana yake fad'uwa har yanzu narasa ko ta menene aunt ta shigo tare da fadin "Sai kuzo Ku gaisa da ita ko." Mimi tayi s'aurin mikewa tana gyara hijab dinta ko jira na bata yi ba tabi bayan aunt Hauwa cike da mamaki nake bin ta da kallo ina mugun mamakin azarb'ab'inta da rashin kawaici lallai Allah mai mutane sai ga mutum yana Abu shi a ganinsa ba komai bane. Muryar Umma naji tana k'wala min kira na amsa da sauri na dauki zurmemam hijabi na sanya na futa da sauri Mimi na zaune kusa da ita sai faman sunkuyar da kanta take tana murmushi nayi sallama granny ta daga kanta tana kallon Asma'u fuskar ka a sake tace" Zo nan kema ki zauna mu fahimci juna daku domin bana don Ku kwace min mijina." Babu yabo babu fallasa naje na zauna kusa Da ita kaina a kasa na gaishe ta, ta shafa kaina tana fadin"Sannu Asma'u d'iyar arziki Allah yayi muku albarka gaba ki d'ayan Ku, Allah ya baku hakuri. Zama da juna kuyi ta hakuri da Mijinku domin wani irin mutum ne shi muskili kuyi hakuri da dabiun shi, gaku 'yan gida daya nasan baza a samu wata Matsalar ba ta fannin kishi tunda 'yan uwan junane Ku, Ku rike junanku da amana kunji ko Allah yayi muku albarka." *12/November/2019* [11/13, 7:59 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *50* Umma tace." Ameen suma ameen Hajiya ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu wata b'araka da taza faru a tsakaninsu zasu zauna lafiya tunda Allah yasa sun hada miji gasu kuma 'yan juna, komai zai zo da sauki. " Granny tace." Masha Allahu to Allah ya tabbatar mana da alkairinsa, hira tsakanin Umma da granny ta mik'a sosai ba tare da sun gane ba, ni bar dakin cike da kunya, Sai ga Mimi ta biyo bayana kwanciya tayi kusa dani hade da lumshe idonta, murmushi nayi ina kallonta cikin tsokana nace." Mimi amaryar Amjadu Alherin Allah." Bude idonta tayi tana kallonta fuskarta dauke da murmushi nace." Ko ba haka bane."? Girgiza kanta tayi tare da fadin." Ni amarya ke kuma Uwar gida ko."? Nace." A ina na zama Uwar gida ke amarya kuma ke Uwar gida. " mik'ewa zaune tayi ta rike hannuna tare da fadin "Yanzu kakarshi take fada cewar k'arfe biyar zai dawo ya dauke ta, wane irin Abu zamu tanadar masa."? Nace." Mimi duk abunda kikayi NIYYA ki bashi domin ki faranta masa kuma kinyi dabara hakan zai k'ara jawo hankalinsa gare ki." Tace." Me zan bashi yanzu."? Dariya na sanya hade da fad'in "Idan baki da abunda zaki bashi in yazo to ki bashi labari mai dad'i da wannan sanyayyar muryar taki." Dariya tayi hade da bani hannu muka tafa, haka dai na dinga biye wa Mimi da duk abunda zata ce min akan Amjadu kuma bana bata shawarar banza. K'arfe shida shaura kira ya shigo wayar tata lokacin tana band'aki tana wanka, Kin dauka nayi don na duba naga shine, motsin ta naji bakin rijiya nace"Mimi yi sauri kizo ana kiran waya. " aikuwa sai gata ta shigo da sauri hannunta na digar ruwa ta karb'i wayar daga hannuna. Kallo na bita dashi. Wata irin murya da ban Santa da ita ba naji tace." Hello." Daga bashi bangaran naji muryar shi sama-sama yace."Momyna kuna ina ina ta kiran waya kusan sau biyar babu wacce ta dauka a cikin Ku." Muryar ta a sanyaye tace." Ni ina wanka ne." "Asma'u fah."! Yafad'a babu sauki a muryar shi,kallonta tayi sai kuma naji tace." Gatanan. " yace." Ok kina nufin kice min tana ganin kirana taki d'aukar wayar."? Mimi shiru tayi taki bashi amsa. Shurun da Mimi tayi shi ya tabbatar masa da abunda yake zargi. Tsaki! Yaja yace." Ok ki fad'awa granny gani Nazo ta futo mu tafi OK." Kafin Mimi tace Wani Abu ya kashe wayarsa. Jikinta a sanyaye take kallona nima ita nake kallo nace"Dole ki koyi hakuri fa, kuma kiyi hakuri da halin shi tunda aure zakuyi ." zama tayi kusa dani tare da fadin"Wai sai ki dinga cewa aure zamuyi eh aure zamuyi har dake a ciki ai,ko" mik'ewa nayi ina dariya nace." Har dani mana, ni ai farin cikin ki ne nawa kar ki damu dani." Futa nayi daga dakin ba tare da na saurari abunda zata ce ba." Cikin sauri Mimi ta shirya ta futo tana ta zabga kamshi ina zaune kofar kicin ina gyara kayan miya na bita da kallo sakin fuskata nayi tare da fadin "Kinyi kyau sosai Mimi." Mirmushi tayi ta shiga Rumfar inda naji grnnay tana sallama da Umma, suka futo a tare Umma sai godiya take mata, sun kuyar da kaina nayi kasa na cigaba da aikina har tazo kusa dani ta tsaya da sakskkiyar fuska tace." To ke zan tafi naga sai wani b'uya kike yi ko tsorona kike ji tun kafin ki shigo kinga 'yar Uwar ki ta saki jikinta mun saba da ita." Murmushi nayi nace." Ki gaida gida mun gode." 'Yar dariya tayi tare da fad'in"Na ga alama gudun angon naki kike yi 'yar uwarki tafi ki sonshi." Ni dai ban ce komai ba har suka fuce ita da Mimi da aunty Hauwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78