Chapter 71
Chapter 71
bayar ba, ba dai a kan 'yar kake min wannan hayaniyar ba Tom sha kurumin ka baby Aysha na gurina yanzu ma ta farka daga bacci na bata ruwa tasha, ka cigaba da kirana mayya a kanta wallahi dad'i nake ji, maganar da wa nake waya bai dame ka ba, mutum na son yayi bacci an dame shi."!! Kashe wayar nayi gaba ki d'ayan ta, wani irin sanyi naji cikin zuciyata na mayar masa da Martani Nasan yau da kyar in zai iya bacci. Aikuwa sakato yayi da waya a hannu yana kallon abun kamar almara baby Aysha na hannun Asma'u wato duk kauce kaucen sa yarinyar nan sai da taje ta dauko mata sweetheart, yasan halin Asma'u farin sani bata munafurci yasan da gaske take, shifa yanzu babu wacce yake jin haushi sai granny domin yana ganin itace ta bada fuskar a dauko masa 'yar sa, da kyar bacci ya dauke shi yana tunanin maganganun da Asma'u ta dankara masa. Abunda yafi tsaya masa a ransa shine tunanin da wa take waya, yasan dai idan da 'yar uwarta mace take waya baza su kai kusan a wa guda ba, wata zuciyar tace masa ko Mujahid ne? Take ya yardar wa zuciyar sa shi din ne....... Cike da tunani. Ta da mafarkin sweetheart d'insa yayi bacci. Ko da safe ma da ya tashi babu kuzari a jikinsa har abokansa suka gane, nan yace musu baya jin dad'i ne kawai, yini yayi a kwance yana kewar gwalantun baby kuma yayi alk'awarin bazai k'ara kiranta a waya ba balle ta kara fada masa magana shifa Yanzu neman hanyar da zai yi nesa da ita yake saboda alak'arsu da Mujahid. Da safe da kyar baby Aysha ta yarda da Umma lokacin da zan tafi skull ma sai Goya ta Umma tayi ta shige da ita daki don kar taga futata ko gilmawa ta ta gani zata fara zillo idan kuwa ban dauketa ba sai ta sanya kuka. Koda muka had'u da Munnu a skull cewa tayi wai kunyar Umma take ji baza ta iya zuwa ta dauki baby ba, sai nace ta bari zan kawo ta insha Allahu. Bayan sallahr la'asar na fito tsaf dani baby na bayan Umma a goye ta sauko ta, ina kokarin sab'ata a kafad'a Umma tace"Ki Goya ta akwai sanyi- sanyi hadarin nan ya zama sanyi, towel din na karba na Goya ta sosai na saki hijab kana nayi wa Umma sallama, gidan su Munnu na nufa kai tsaye. ***** Ummansu Munnu tayi farin ciki sosai ta karb'i baby ta goya ta tam a bayan ta har sai da tayi bacci ta tashi sannan ta sakko da ita, tace " Ya kamata a gwada bata abunci fa." Dariya nayi nace"Ta isa cin abunci yanzu."? Tace"Bari ki gani." Wake ta Mirza ta sanya mata a baki Aikuwa baby ta lamushe ni da Munnu muka dinga dariya, Ummansu Munnu tace"Yaran yanzu da wayon su ake haifar su, gashi dai daga laluba mata wake ta lamushe, haka Ummansu Munnu tayi mata kusan sau biyar sannan ta k'yaleta ta bata ruwa, kuma Allah ya taimaka bata yi kuka ba, sai bayan magariba Babansu Munnu ya dawo gida, ya dauki baby Aysha yayi mata addu'a hade da sanya mata albarka yayi mata addu'a sosai da sosai kana ya sanya k'aramin yaron shi yaje kanti yayi mata siyayya sosai kalolin biscuits iri-iri Ummansu Munnu tayi ta dariya tana fad'in "Irin wannan siyayar akai wa kishiyata alhalin gani a zaune ba'a min ba, dadin abun dai cin abunci ma ni na koya mata." Baban su Munnu yace." Da kin sani Baki koya mata ba ai." Mudai dariya kurrum muke musu, hira muke da Munnu sosai wacce ta dauke min hankalina sai da Ummansu Munnu ta leko dakin tana fad'in "Asma'u ko anan zaki kwana ne ga hadari nan yana had'owa." Agogo na kallah da sauri naga tara shaura da sauri na mike INA fad'in "A'a wallahi Yanzu zan tafi." Baby na dauke wacce ta Dade da yin bacci na Goya ta da sauri na zura hijab na fito wani bakin hadari na gani a gabas Nace"Munnu Allah ya kiyaye ni da dukan ruwa." Tace "ameen dai amma ni shawara ta ki bari sai gobe kawai kya tafi." Ko kallonta banyi ba nayi hanyar futa ina sallama da Ummansu dake Uwar daki. Ina futowa titi aka fara wata irin iska mai k'arfi abubuwan hawa sai gudu suke akan titi duk yawanci motocin gida ne da kyar na samu a d'an sahu Wanda ya rage mutum d'aya a ciki na shiga aikuwa kamar almara ruwa ya kece kamar da bakin kwarya,ni da nake gefe ruwa ya fara duka na, kafin kice me na jike jagab, ta karewa nayi ina tsoran kar ruwa ya taba baby sai ta fara motsi tana k'ananun kuka, gaba na ya fad'i jijjigata nake yi INA so tayi shiru yarinya kamar wacce ake zugawa ga feshin ruwa sai dukan fuskata yake, kamar zanyi kuka nace "Don Allah kayi sauri babyna na Kuka."! Mai dai-dai ta yace." Hajiya ai ina ganin parking ma zanyi saboda ban San iya inda ruwan zai tsaya ba, domin karfinsa yayi yawa sai ya tsagaita sai mu tafi." Kafin ince komai ya tsayar da 'Dan sahunsa, nace"Na shiga uku ni Asma'u nayi da na sani tawowa da na hak'ura na zauna na kwana gidansu Munnu zai fi min, tausayin baby nake ji jin yadda take sakin ajiyar zuciya tana baya sai kyarmar sanyi jikinta yake yi, ni da ita duk mun jike matan dake a dai dai ta na kalla naga sai hirarasu suke yi babu abunda ya dame su, su kadai ne single babu wacce take da yaro Karami balle tayi fargaba. Sai da aka dauki 30minutes ana ruwa mai k'arfi sannan ya tsagaita sai wata irin iskar sanyi ta soma kadawa, a lokacin naji Baby ya fara atishawa sakkota nayi ina duba jikinta, naga jagab duk da dabarun da nayi mata sai da ta Nike hatta da gashin kanta, kuka take so tayi ta kasa sai sakin atishawa take, hawaye na fara sharewa kana na rungume ta tsam! A jikina Ina fadin"Duk nice na jawo miki babyna."! Jagab! Muka shiga gida muna d'igar ruwa Umma na gani cikin ruwa ta dinga min fada "Shin baza ki bari gobe idan Allah ya kaimu kya dawo ba, ko kuwa gidan su Munnu din bak'on ki ne.? Ko tausayin k'aramar yarinya bakya ji sai kinje kin kwaso mata mura da da tari ko." Fada sosai Umma take min, ni kam hankalina na gurin baby wacce take ta motsi majina har ta fara zurara a hancin ta, kayan jikinta na cire mata da sauri na sanya mata Pampers na sanya mata kayan sanyi masu kauri kudindine ta nayi. Umma tace"Bani itanan mu gani." Mik'a mata ita nayi, ina tsaye da jikakkun kaya ban damu da In cire su ba, duk da nima hakan take kamar baby kwata kwata bana son dukan ruwan sama Shikkenan zazzab'i da mura zai kama ni. Robb Umma ta dinga Mirza mata k'irjinta da bayan kunnen ta, da tafin kafarta sannan ta Goya ta. Futa nayi jikina duk babu kwari, har yanzu da ragowar ruwa kadan kadan yake sauka d'akinta na shiga na kwabe kayan jikina pant
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78