Chapter 2
Chapter 2
'yan kasuwa wad'anda suka ci suka ts dakai marasa tausayin na k'asa dasu Wanda Kansu kawai suka sani. Masu bakin ciki ga duk wani Dan kasuwa da ya sauke farashin kayansa, a cewar su talaka ba abun tausayi bane. Su biyar ne a dakin meeting din gidan gomnati wato government house suna tattaunawa game da yanda zasu b'ulluwa Amjadu domin dukaninsu saurari jawabin sa, na yau, hankalin su yayi masifar tashi sosai jin wai har company biyu ya bude a kasashen waje bayan company shi nan Lallai ya zama dole su San yadda za'ayi su rusa shi. Alhaji Sunusi mai leshi ne Yace. " Ni ina gani kawai mu hada baki da ma'aikatan sa mu Sakar masu KUDI Sosai mu fada musu bukatar mu. Cewar muna so su sanya algus da mugunta a ko wace irin adduga da zasu sarrafa, a company ta inda duk kayan da za'a futar a company su zama marasa k'wari da karko kunga daga nan Jama'a zasu gane sai su fara guduwa." Mai citta ya gyara zama hade da sakin murmushin mugunta yace." Wannan shawarar taka tayi kyau kuma itace abar d'auka dole zamu San yadda mukayi mu jone da ma'aikatan nasa idan muka jik'asu da kudi kome ye zasu yi ko ya kuka gani."? Duk suka yi na'am da haka, nan taro ya watse ko wannen su cike da farin ciki. ***** Tana zaune a parlor kamar ko da yaushe me aikin ta Iyami na zaune a gefanta tana bata labarin garin su, yayi sallama ya shigo parlor, Iyami dattijiwa mai kirki ta dinga yi masa sannu da zuwa had'e da tsokanar sa, zama yayi cikin kujera yana gaishe ta, ta amsa da fuska a sake, da sauri ta nufi kicin domin ta kawo masa abunci. Granny ta kalle shi babu yabo babu fallasa tace"K'ato me k'irar damu dawa kana tafiya gotai-gotai da kai babu iyali kai ko kunya baka ji, ka kai munzali amma ka tsaya shirme." B'ata fuskarsa yayi yace. " zan can kenan daga zuwa sai maganar aure wai a kanki nake ne." Granny tace." Yo ni in a kaina kake ai da tuni ka kashe ni. Dube ka don Allah kamar zaka ji babu jiki a murd'e ai kai kam matarka zata fad'awa 'yan garinsu." Gyara zaman sa yayi yana dariya kasa-kasa yasan halin kakar tasa da sakin magana ko wace iri ce ita babu ruwan ta, kafin yace wani Abu yaji tace" ka fad'amin in baka da lafiya sai in baza ma nema maka magani ko kauyen su Iyami muka je nasan za'a samo maka maganin k'arfi, ina amfanin girman jiki da k'wanji babu fus!! Uhum? Irin Ku ne matayen Ku suke shan takaici a zahiri dai gaku maza a bad'ini kuwa sai takaici." Ta k'arashe maganar ta tsakanin ta da Allah. Gyara zamansa yayi da k'awataccan murmushi a fuskar sa yace." E dama na kasa fad'a miki bani da lafiya don Allah ki shiga k'auyika ki nemo min maganin k'arfi kinji."!! Granny ta kalleshi da hankalinta a tashe tace"Yanzu kai k'ato da kana fama da wannan lalurar ka zauna sai dai kaci ka sha ka nemi kudi? Au! Ko da naji shiyasa ko wace mace aka kawo maka sai kace bata yi maka ba, tom yanzu yaya kake ji a jikinka shin kana sha'awar mace sa'i da lokaci ko A'a."!? Granny ta tsarashi da tambaya hankalinta duk ya tashi. Kamar gaske yace." Kwata-kwata bana jin sha'awar mata, amma ina ganin a haka zanyi auran da kike so nayi." Tace" innalillahi u ni 'yasu! Amma yaron nan kaso kacuci kanta.....Iyami Iyami Iyami.!" Ta dinga kwala wa mai akinta kira. Yace." Nifa ba cewa nayi kiyi min taron dangi ba, uhumm ke kad'ai na fad'awa damuwa ta." Hararasa tayi tace"Naji kana maganar zaka yi aure a haka Uwar me zaka tsinanawa matar taka, abunci da madara kawai zaka bata bukatar ta kuma waye zai biya mata."! Cike da tuhuma tayi masa tambayar." Dariya yake sosai yace." Ai Irina zan auro kinga bani da matsala ." "To baka isa ba ehe! Nima ai ina son 'yan yara, a gaba, ni kawai zaka cuta.'!!! Tsakanin ta da Allah take maganar, Iyami ta shigo parlor da sauri take fadin" Hjy kira kike ko."? Granny tace"Iyami zama bai kama mu ba, k'ato babu lafiya." Iyami ta kalleshi cikin rawar baki tace"Mai gida babu lafiya Ashe? Allah ya kawo sauk'i.'" Yace." Ameen Iyami ai tace"Zata shiga ta futa ta samo min magani." Iyami tace"Hjy meye yake damun Shi ne." Granny tace"Iyami je ki cigaba da aikin ki zamuyi maganar idan anjima." Iyami ta mike da jiki a sanyaye. Kallo ya bita dashi yana kumshe dariya. Ita kuwa granny surutai kawai take masa tare da yi masa fad'a ya zauna cuta yaci k'arfin sa, saboda yana so ya zama lusarin namiji. Aikuwa tana tsaka da fad'an ta taga an hasko shi a TV tashar CTV kano mutane kewaye dashi yana jawabi. Tace." Duba ka gani k'ato dubi yanda Allah yayi maka kwarjini da daukaka ta jama'a kudi duk kana da su. OO ni! 'Yar nan Allah kar ka jarrabe mu da abunda baza mu iya ba." Granny ta fashe da kuka sosai! Cike da mamaki yake kallonta, ganin da gaske kukan take yasa ya rungume ta a jikinsa yana rarrashinta tayi shiru yasan ko ya fad'a mata da wasa yake ba yarda zata yi ba ganin yadda duk ta tada hankalinta yasa yace." Granny kiyi hakuri ki daina kuka don Allah zan yi aure in haihu, ina ganin ma yanda nake jin k'arfi a jikina in dinga bada k'wayayen 'yan biyu ko uku , ki kwantar da hankalin kinji kiyi shiru kiji wani."Shiru granny tayi tana share hawaye tsakanin ta da Allah. Wayarsa ya ciro daga aljuhu yace." Bari in kira miki ita Ku gaisa." Tace"wacece kuma"? A hankali yace "My wifi mana." "Meye wifi."? Ta tambaye shi dariya yasa yace." Matata mana."? Sakin fuska tayi tace" 'yar albarka ta yarda zata aure ka da lalurar ka ko.'? Gyad'a kansa yayi kamar gaske, yana laluban numbar Mimi, sai da ya kira sau uku ba a d'auka ba, shi da in yayi kira sau d'aya baya sake wa, yau gashi yayi uku, yana shirin yin na hud'u. Mimi na band'aki a lokacin ta kuma b'oye wayar bayan katifar mu, ina shigo wa naji ringing din waya, dube-dube nake sam ban ganta ba, in da nafi jin karar tayi yawa nan na nufa na janye pillow da ta kare wayar dashi, ina dauka kiran yana katsewa, wayar na rik'e a hannuna ina dubawa cike da mamaki! Tabbas wayarsa ce, ga k'amshin sa nan jikin wayar domin hanci na ya Riga ya gama sanin k'amshin sa. Wani kiran ne ya shigo kamar kar in dauka sai kuma wata zuciyar tace"dauki kije abunda zai je da Mimi, dannawa nayi na bud'e speaker sosai na aje ta kan kati far. Muryar sa naji yo yana fad'in"Ungo wayar gatanan Ku gaisa, kafin in an kara Naji muryar mace, macen ma ba yarinya ba, dattijuwa me kamali. Motsin Mimi naji a tsakar gida, da sauri na k'wala mata kira ina fadin"Mimi kizo an kira wayar ki."!!!!!!! Granny da shi kanshi uban gayyar suka yi sak! Yayi wa muryar ta farin sani saboda tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78