Chapter 23
Chapter 23
gidan da kallo, shiga nayi na barshi tsaye a gurin. Mamaki yake sosai yanzu dama acikin wannan gidan Asma'u take rayuwa? Duka girman gidan bai kai b'angaran mai gadin gidan shi girma ba, gyada kansa yake yana duba 'yan gujub-gujub din gidajen dake layin namu a cikin zuciyarsa yake fadin talaka na ganin rayuwa me zai hana baza'ayi zazzab'in maleria ba kwataci duk sun bi hanya sauro da kudaje da bola ko ina. Tsaye na ganshi jikin bango hannunsa nan nade a k'irjinsa nace"Shigo to" Gaba nayi yana bina a baya Umma na zaune gefen sabuwar tabarmar da ta shimfid'a masa tana sanye da farin hijab fuska a sake take amsa sallamarsa. Cikin ladabi naga ya tsaya bakin kofar ya cire hadd'adan takalimsa karfashi sanye da wata lafiyayyar safa ya karasa kan tabarmar . Umma fad'i take"Sannu da zuwa yaron arziki Mara ba lale. Zama yayi kanshi a kasa yace." Barka da yamma Umma na same Ku Lafiya."? Umma tace"Lafiya Lou Alhmdullahi ya kokarin ka da fama da jama'a. "? Yace." Alhmdullahi wallahi ya me jiki kuma."?.Tace" Jiki yayi sauk'i ai bs wani tsanani Yayi ba Asma'u ta ta soka." Murmushi yayi tare da fadin"Dama yau nayi niyar in shigo mu gaisa sai kuma take fadamin Momyna babu lafiya." Umma tace"Wallahi kuwa tari take amma da sauk'i dai tunda Aminu ya siyo mata magani Tasha ta samu tayi bacci." Yace." Tou Alhamdullahi Allah ya kara sauk'i. " Yanda suke hira da Umma sai abun ya bani mamaki kamar Wanda suka shekara da sanin juna Umma sai shi masa albarka take da fadin"Muna ganin taimakon talakawa da kake yi a garinan muna jin dad'i Ubangiji Allah ya tsare ka ya kare ka daga sharrin masu sharri. " yaji dadin adduoin da Umma take masa ga yanayin yanda yake amsawa Mimi dake kwance a daki tana bacci kamar a mafarkin taji muryar shi firgigt ta tashi ta zauna k'irjinta yayi mata nauyi sosai rarrafowa tayi ta futo tsakar gida tana dafa bango Nice na fara ganinta ganin kamar tana kokarin fad'uwa ya sanya naje da sauri na rike ta muka karasa kusa dasu Umma Tace." Yauwa ai gata nan ma ta tashi sannu Mimi." Zaunar da ita nayi kusa da shi, na matsa gefe Amjad mamaki ramar Mimi yake duk da yake dare ne kuma tsakar gidan babu wadataccan haske sai da ya fahimci tana jin jiki. A hankali yace." Momyna ya jikin ki? Ashe haka Abu yayi tsanani. " Cikin sanyayyr murya tace." Jiki da sauk'i ." gyada kansa yayi tare da kallon Umma yace." Kunje asibiti da ita kuwa."? Kafin Umma tace Wani Abu Yaya Aminu ya shigo gidan. Gabansa ne ya fad'i ganin Mutumin dake zaune ga gidan jininsa Mimi kenan a zaune a kusa dashi, lokaci guda ya b'ata fuskarsa hade da yin kicin-kicin da ita sama-sama suka gaisa dashi Yana mamakin me ya kawo shi, zama yayi gefen rijiya yana sauraran maganar da suke yi da Umma. Umma tace." Ba muje asibiti ba amma dai gobe in Allah ya kaimu za muje a duba ta sosai." Gyada kansa yayi shiru na minti biyu yace." Gobe idan Allah ya kaimu zan turo dravar sai a kaita asibtin malam Aminu a duba ba ta sosai." Umma tace"Allah yayi albarka ai da ka bari ma, sai muje asibitin Murtala ." Hannu ya zura aljihu ya futo da kudi masu yawa ya zube gaban Umma ya mike tare da fadin" Zan wuce Allah ya bata Lafiya ." Umma tace"Harda wahala kuma ai da ka barshi." Shiru yayi ya mik'awa Aminu hannu suyi sallama. Rai babu dad'i Aminu ya mik'a masa nasa hannun sukayi musabaha. Takalmin shi ya sanya Umma sai godiya take masa futa yayi cikin sauri Umma ta kalleni tare da fadin" Kije ki raka shi mana kinye tsaye." Bayansa nabi da sauri.. Yayi nisa sosai don Haka sai da na k'ara sauri. Na tadda shi. Yana kokarin bude mota na same shi Yace." Amma nayi mamakin ramar Mimi,Abunda kika fada gaskiya ne."? 'K'warai kuwa Mimi na sonka sosai kai kuma kana yaudarar ta." Shiru yayi yana tunani tabbas abunda Asma'u ta fada gaskiya ne baya jin dai-dai da kwayar zarrah na son Mimi a zuciyar sa, yana yi mata so ne kawai irin na musulunci sai kuma sunan mahaifiyar sa da take dashi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da fadin"Allah ya bata Lafiya, Nasan ni babu laifina anan gaskiyar magana ko Yanzu aka ce an bani ita zan aure ta darajar son da data ke min." [11/10, 8:25 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *Mallakar_BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.* *47* Shiru nayi masa domin na rasa abunda zance dashi ni kaina al'amarin Mimi yana bani tsoro Mota ya bude ya shiga tare da fadin"Ni zan tafi zan kira waya insha Allahu. " Matsawa nayi daga jikin motar ba tare da nace masa komai ba ya ja ya tafi na lura jikinsa duk yayi sanyi. Ina koma wa gida na tarar da Ya Aminu ya tasa Umma a gaba sai faman bala'i yake mata Ina shiga ya hau d'ura min ashar wai me yasa na gayyato Amjadu gida wallahi komai kulafucin sa ba zai bar mishi Mimi ba. Masifa yake kamar zai dake ni Umma tace"Kar ka sake ka doke ta Aminu Sam Asma'u bata da laifi Kaine dai idonka ya rufe, ka ke ganin da laifin ta anan.". Kan Mimi ya dawo cikin hargowa yace." Wallahi Mimi ko mutuwa zaki baza ki aure shi ba sai dai idan ki Mutu ni dashi mu rasa amma ina ji ina gani bazan bar masa ke ba." Yana gama maganar shi ya fuce daga gidan a fusace.! Mimi ta fashe da kuka tari ya sark'e ta, aikuwa ta dinga yi bubu ji babu gani, Umma ta jawo ta jikinta ta rungume ta sosai tana danne mata kirjinta hankalinta duk ya tashi Da sauri tace"Asma'u d'ebo ta murhu a shafa mata ko Allah zai sanya ya Tsaya tari. Da gudu na nufi kicin na d'ebo toka Umma ta bude rigar Mimi ta shafa mata. Kamar kara ingizata ake ta cigaba da tari!!! Nace." Ina maganin a dauko a kara bata." Da kyar Umma tace"Dauko a daki." Dakin na shiga da sauri na dauko maganin, abunda na gani yayi mutukar gigita ni da bani tsoro wani irin jini bak'ikkirin na gani daga bakin Mimi yana zubowa jikin Umma, Da sauri na jefar da kwalbar maganin nayi kanta INA salati. Umma kuwa kuka ta fashe dashi tana tare jinin da hannunta. Baki na rawa nace"Umma jini ne ko."? Tace." Asma'u maza duba waje ki gani Aminu nan ki kirashi mu tafi asibiti abun ya zama babba." Da gudu na futa ko talkami babu. Mimi ta galabaita iya galabaita tari take sosai jini na zuba daga bakinta idanunta sunyi jajazur dashi sai daga hannu take. Ni da Aminu muka shigo gidan hankalumu ya tashe. Yana ganin Abunda yake faruwa ya gigice tare da fadin"Innalillahi wainnailahi raji'un. " futa yayi da sauri ya dauko mota. D'aukar ta yayi kacokan ya futa da ita da saurin Nida Muka rufa masa baya zuwa yanzu na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78